"A Tsage Biri har Wutsiya": Lauya Ya Nemi Bayani a kan Kudin da Remi Tinubu Ta Tara

"A Tsage Biri har Wutsiya": Lauya Ya Nemi Bayani a kan Kudin da Remi Tinubu Ta Tara

  • Lauyan kare hakkin dan adam, Ayodele Ademiluyi, ya maka matar Shugaban Kasa, a kotu kan kudin da aka tara don gina Sabon Dakin Karatu na Kasa
  • Lauyan ya bayyana cewa hakan ya zama dole bayan an bayyana cewa an bai wa Remi Tinubu sama da Naira biliyan 20 a matsayin tallafi
  • Ademiluyi na neman kotu ta tilasta wajen tabbatar da cewa an shaida wa 'yan Najeriya yadda ake shirin kashe wannan kudi da aka tara

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Ayodele Ademiluyi, wani lauya mai fafutukar kare hakkin dan adam, ya shigar da kara a gaban kotun tarayya da ke Abuja, yana kalubalantar Oluremi Tinubu.

Lauyan ya shigar da koke ne a kan matar Shugaban Kasa, dangane da kudin da aka tara domin kammala aikin gina Dakin Karatu na Kasa.

Kara karanta wannan

Hankalin Tinubu ya koma kan kundin tsarin mulki, yana so a yi masa kwaskwarima

Ana tuhumar Mai Dakin Shugaban Kasa a kotu
Hoton Uwargidan Shugaban Kasa, Remi Tinubu Hoto: Oluremi Tinubu
Source: Twitter

The Cable ta ruwaito cewa a cikin karar mai lamba FHC/L/CS/1900/25, lauya Ademiluyi ya hada da shugaban kasa Bola Tinubu da Ministan Shari’a na kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma akwai Ministan Ilimi, Tunji Alausa; Veronica Chinwe, shugabar Dakin Karatu na Kasa; Hukumar Dakin Karatu na Kasa; Hukumar Bunkasa Binciken Ilimi ta Najeriya; bankin Zenith Bank; da kuma Hukumar EFCC.

Yadda aka tara wa matar Tinubu kudi

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa a ranar 1 ga Satumba, Matar Shugaban Kasa ta sanar da cewa za ta sadaukar da bikin zagayowar ranar haihuwarta ta 65 ga inganta ilimi.

Ta ce a bikin da ya gudana a ranar 21 ga watan Satumba, 2025, tana son a tallafa wajen tara kudi domin kammala aikin Dakin Karatu na Kasa.

Mai dakin Shugaban Kasar ta bukaci abokai da masoyanta su tura kudi maimakon aika da kyaututtuka kamar fure, katin taya murna ko sako a jarida.

Kara karanta wannan

Shettima ya kalli shugabannin duniya, ya fadi matsayar Najeriya kan kafa kasar Falasdinawa

Lauya ya maka Tinubu a kotu
Hoton Shugaban Kasa, Bola Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A yayin liyafar da ta yi da munema labarai a fadar shugaban kasa, Remi Tinubu ta bayyana cewa an riga an tara Naira biliyan 20.4 don aikin.

Lauya ya kai Remi Tinubu kotu

Lauya Ademiluyi ya bayyana cewa ya bukaci kotu da ta bayar da umarni wanda zai tilasta wa EFCC binciken asusun da ake amfani da shi wajen tara kudin.

Hakazalika, yana rokon kotu da ta umarci Shugaban Kasa Bola Tinubu da ya ware 26% na kasafin kudin shekarar 2026 ga ma’aikatar ilimi ta tarayya.

Haka kuma yana son a tabbatar da cewa an ware kaso mai tsoka daga ciki zuwa ga Cibiyar Bunkasa Littattafai ta Kasa wato National Book Development Centre.

Sanata Remi Tinubu ta raba tallafi

A wani labarin, kun ji cewa uwar gidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana cewa duk kudin da ake amfani da su wajen bayar da tallafi a karkashin shirinta ne.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An yi kutse a shafin gwamnatin Najeriya, an wallafa wata takarda

Ta ce babu ko sisi daga cikin wannan kudi da ya ke fito wa daga asusun gwamnatin tarayya kai tsaye, sai dai ta kan nemo tallafi daga wurare daban-daban sannan ta raba ga mabukata.

Bayaninta na zuwa bayan wasu daga cikin ‘yan Najeriya na tambayar tushen kudin da ake rabawa, ganin cewa ofishin Matar Shugaban kasa ba shi da kasafin kudi a cikin tsarin mulki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng