'Yan Sanda Sun Kama Malamin Addinin Musulunci a Jihar Bauchi

'Yan Sanda Sun Kama Malamin Addinin Musulunci a Jihar Bauchi

  • 'Yan sanda sun kama malami na makarantar Tsangaya bisa zargin azabtar da almajiri dan shekara 11 a jihar Bauchi
  • Kwamishinan yan sanda na jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu ya ba da umarnin mika wanda ake zargi ga sashen binciken manyan laifuffuka
  • A binciken farko da ya sanda suka yi, malamin ya ce ya daure yaron da igiya ne domin kada ya gudu kafin iyayensa su kariso

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Bauchi - Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wani malamin addinin musulunci mai suna, Malam Lawal Nasiru, mai shekaru 28.

Yan sanda sun kama shi ne bisa zargin duka da daure wani ƙaramin yaro ɗalibin makarantar Tsangaya, watau Almajiri mai shekaru 11 a ƙaramar hukumar Darazo.

Babban sufetan yan sanda na kasa, IGPG Kayode.
Hoton Sufeta-Janar na Rundunar Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka dan sanda, an yi awon gaba da jami'an tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malami ya azabtar da almajiri a Bauchi

Ya ce, lamarin ya faru ne a ranar 21 ga Satumba, inda ake zargin Malam Nasiru, mazaunin Unguwar Jarmai, da ɗaure almajirin mai suna Sani Abdullahi da igiya, tare da bugunsa da kebul da sanda.

Ahmed Wakil ya bayyana cewa yaron, wanda ɗalibi ne a wata Makarantar Tsangaya, ya samu mummunan rauni a hannaye da ƙafafunsa.

Wani mutumi mai suna, Idris Mohammed daga kauyen Gidan Waya, Darazo, wanda ma’aikaci ne a Sashen Walwalar Jama’a, ya kai ƙorafi ofishin rundunar ‘yan sanda a Darazo.

Idris ya shaida wa yan sanda irin azabatarwar da malamin Tsangayar ya yi wa karamin yaron, wanda ta kai ga raunata shi.

Yan sanda sun cake wanda ake zargi

Bayan samun rahoton abin da ya faru, DPO na caji ofis din Darazo, Auwalu Ilu tare da tawagarsa suka durfafi wurin, inda suka kama wanda ake zargi.

Tuni dai aka garzaya da almajirin zuwa asibitin gwamnati na Darazo domin samun kulawar likita.

Kara karanta wannan

Ewugu: Tsohon mataimakin gwamnan da 'yan bindiga suka sace kafin ya rasu

Yayin gudanar da bincike, wanda ake zargi ya amsa cewa ya ɗaure ƙaramin yaron, amma a cewarsa ya yi hakan ne don hana shi guduwa daga makarantar kafin iyayensa su iso.

Sai dai almajirin da aka azabtar ya shaida wa yan sanda cewa an tsare shi cikin azaba na tsawon lokaci ba tare da wani dalili ba, in ji rahoton Tribune Nigeria.

Jami'an yan sanda.
Hoton wasu dakarun Rundunar Yan Sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Getty Images

Matakin da yan sanda suka dauka

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya bayar da umarnin a mika lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuffuka (SCID) a Bauchi domin ci gaba da bincike.

Rundunar ta tabbatar da cewa za a gurfanar da wanda ake zargi a kotu bayan kammala bincike.

Dan sanda ya harbe soja har lahira a Bauchi

A wani labarin, kun ji cewa wani dan sanda da ke aiki a sashen rundunar na MOPOL ya bindige sojan Najeriya har lahira a jihar Bauchi.

Wannan al'amari ya tayar da hankulan mazauna garin Futuk da ke cikin karamar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi musamman wadanda abin ya faru a kan idonsu.

An ruwaito cewa rigima ta tashi ne a daidai lokacin da sojoji da aka ajiye a shingen bincike na garin Futuk suka yi kokarin dakatar da motar kamfanin China da dan sandan ke wa aiki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262