An Samu Matsala, Jirgin Sama Ya Yi Gaggawar Dawowa Kasa bayan Tashinsa daga Abuja

An Samu Matsala, Jirgin Sama Ya Yi Gaggawar Dawowa Kasa bayan Tashinsa daga Abuja

  • Wata fasinja mace ta shiga mawuyacin rashin lafiya a cikin jirgin Ibom Air bayan ya tashi daga Abuja zuwa Legas
  • Matukin jirgin ya yi gaggawar juyawa tare da komawa filin jirgin da ya tashi a Abuja domin mika matar ga likitoci
  • Wannan al'amari ya jawo tsaiko ga jirgin saman, wanda daga baya ya sake tashi zuwa jihar Legas kamar yadda aka tsara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Jirgin sama na kamfanin Ibom Air Flight 561 mallakin gwamnatin jihar Akwa Ibom ya yi gaggawar komawa filin jirgin saman Abuja jim kadan bayan tashinsa.

Jirgin wanda ya tashi da nufin zuwa Legas ya dawo filin jirgin sama na Abuja ne sakamakon wata mata, daya daga cikin fasinjoji da ta shiga mawuyacin hali na rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Sabuwar cuta mai cin naman jiki ta bulla a Adamawa, gwamnati ta fara bincike

Jirgin kamfanin Ibom Air.
Hoton jirgin saman kamfanin Ibom Air Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tribune Nigeria ta ruwaito cewa ma’aikatan jirgin sun gaggauta bai wa matar taimakon farko ganin yadda rashin lafiyarta ta tsananta jim kadan bayan tashin jirgin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me yasa jirgin ya yi gaggawar komawa Abuja?

An tattaro cewa ma'akatam sun yi sanya matar ribar iskar numfashi da danna mata kirji domin ceto rayuwarta.

Kafin tashin jirgin, an sanar da babban mai kula da fasinjoji (SCCM) cewa akwai fasinja mai fama da rashin lafiyar da ta shafi motsi (PRM) da ke tare da mijinta da iyalanta.

A cewar bayanan da aka tattara:

"Bayan jirgin ya tashi, ma’aikata suka fara hidimar cikin jirgi, sai rashin lafiyar matar ta motsa. Jami'in SCCM da tawagarsa suka dauki mataki nan take.
"Su ka kuma yi kiran neman wani likita ko ma’aikacin lafiya a cikin jirgin, amma ba a samu ko daya ba.”

Bisa ka’idojin bayar da taimakon farko, ma’aikatan sun bi tsarin da doka ta tanada domin ceto rayuwar matar.

Kara karanta wannan

Abin da Gwamna Fubara ya fada kan Tinubu da Wike a jawabinsa na farko a Ribas

Halin da fasinjar jirgin sama ta shiga

Ma'aikatan sun gano cewa bugun zuciyar matar ya canza kuma tana neman rasa numfashi, sai suka kwashe ta zuwa wajen girki na jirgin inda aka sanya mata robar iskar oxygen.

A wannan lokaci ne matukin jirgin ya yanke shawarar dawowa filin jirgin sama a Abuja don matar ta samu kulawar likita cikin gaggawa.

A yayin dawowa filin jirgin, ma’aikatan suka rika danna mata kirji, sannan suka rika sanar da matuki halin da ake ciki har zuwa sauka.

Likitoci sun samu nasarar ceto matar a Abuja

Da suka isa Abuja, an mika matar ga tawagar likitocin gaggawa na filin jirgin saman Abuja domin ceto rayuwarta.

Rahotanni sun tabbatar da cewa likitocin sun yi nasarar dawo da numfashi da bugun zuciyar matar kuma yanayinta ya daidaita.

Bayan haka, jirgin saman ya sake komawa ya tashi zuwa Legas kamar yadda aka tsara.

Jirgin kamfanin sufuri mallakin gwamnatin Akwa Ibom.
Hoton Jirgin Kamfanin Ibom Air Hoto: @ibomairline
Source: Twitter

Kamfanin jirgin ya yaba da ƙwarewar ma’aikatansa da kuma saurin daukar matakin gaggawa wanda ya kai ga ceto matar, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Sakkwato: Shugabannin makarantun sakandare 6 sun tsunduma kansu a matsala

Matukan jirgin sama sun sha giya a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar NSIB ta gano cewa wasu matukan jirgin kamfanin Air Peace sun kwankwadi giya da kwayoyi kafin jirginsu ya sauka a Ribas.

Rahotanni sun nuna cewa jirgin da matukan ke ciki ya sauka daga kan titinsa a lokacin sauka a jihar Ribas, lamarin da ya kada hanjin fasinjoji.

A rahoton bincike da NSIB ta gudanar, sakamakon gwajin da aka yi wa matukan ya tabbatar da cewa akwai sinadaran giya da wasu kwayoyi a cikin jininsu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262