Matsala Ta Kunno Kai a Najeriya, Miliyoyin Yara na Fuskantar Hadarin Mutuwa a Arewa
- Bill Gates ya kara ware makudan kudi domin yaki da cututtukan da ke jefa rayuwar kananan yara cikin hadari musamman a Najeriya
- Attajirin dan kasuwar ya ce yaro daya cikin shiga na fuskantar hadarin mutuwa kafin cika shekara biyar a Arewacin kasar nan
- Ya bukaci gwamnatoci da kungiyoyin agaji su gaggauta daukar matakan da suka dace domin ceto rayuwar kananan yara
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Attajirin nan kuma mai taimakon jama'a daga Amurka, Bill Gates, ya bayyana damuwa kan yawan mace-macen yara a Arewacin Najeriya
Hamshakin mai kudin ya yi gargadin cewa daya daga cikin yara shida na fuskantar hadarin mutuwa kafin cika shekaru biyar da haihuwa a Arewa.

Source: UGC
Bill Gates ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi kafin fara taron shekara-shekara na gidauniyarsa watau Gates Foundation a New York, in ji The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaran Arewa ke fuskantar hadarin mutuwa
Ya ce wannan al’amari babban gargadi ne ga gwamnati da hukumomin da ke da alhaki domin su dauki mataki cikin gaggawa don ceto rayuwar yara a Arewacin Najeriya.
Bill Gates ya ce:
“Yaron da aka haifa a Arewacin Najeriya na da kashi 15 cikin 100 na yiwuwar mutuwa kafin ya kai shekara biyar. Zabi biyu ya rage, ko dai a dauki matakin dakile hakan ko a yi kamar ba shi da muhimmanci."
Bill Gates ya kara ware makudan kudin tallafi
Domin ƙara ƙarfafa yaƙi da cututtuka, Gates ya ce gidauniyarsa ta ware Dala miliyan 912 domin yaƙi da cutar kanjamau, tarin fuka da zazzabin cizon sauro daga 2026 zuwa 2028.
Wannan tallafin zai ci gaba da tabbatar da nasarorin da ke rage mace-macen yara a duniya tun daga shekara ta 2000 daga kusan miliyan 10 a shekara zuwa ƙasa da miliyan 5.
Sai dai Gates ya yi gargadin cewa nasarorin da aka samu na iya rushewa, ganin cewa tallafin kiwon lafiya daga ƙasashen duniya ya ragu da fiye da kashi 20 cikin 100 a bara.
Attajirin dan kasuwar ya jaddada cewa gudummawar agaji da taimakon da wasu daidaikun mutane ko kungiyoyin ke bayarwa, ba ya nufin sauke wa gwamnati nauyin da ke kanta.
“Ba za mu iya cike gibin da gwamnati ta bari ba, kuma ba na son a ɗauka hakan zai yiwu,” in ji shi.
Attajirin ya ba gwamnatocin Najeirya mafita
Bill Gates ya bukaci gwamnatoci da su inganta asibitoci, su faɗaɗa harkokin rigakafi, tare da amfani da sababbin kirkire-kirkire na kiwon lafiya.
Ya ce idan shugabanni suka sake dagewa a kan dabarun da aka gano, za a iya ceton rayukan miliyoyin yara nan da 2045, rahoton Channels tv.
Najeriya na daga cikin ƙasashen da ke da mafi girman matsalar mace-macen yara, musamman a Arewa, inda lalacewa tsarin lafiya, talauci da rashin tsaro ke hana mutane samun kulawar gaggawa.

Source: Getty Images
Wane mataki Gwamnatin Najeriya ta dauka?
Wani babban jami’i a ma’aikatar lafiya ta tarayya, da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce gwamnati ta fara ɗaukar matakai don magance matsalar mace-macen yara
“Mun faɗaɗa rigakafin yara, muna kokarin farfaɗo da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko, tare da aiki da abokan haɗin gwiwa kamar Gates Foundation don cike gibin da ke akwai."
Ana zargin zazzabi mai tsanani ya shigo Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Kano ta gargadi jama'arta kan zazzabi mai tsanani mai sa zubar da jini da ake zargin ya bulla a Najeriya.
Wannan gargadi na zuwa ne bayan Hukumar Yaki da Cututtuka ta Kasa (NSCDC) ta ce an killace mutum biyu da ake zargin sun kamu da zazzabin a Abuja.
Binciken farko ya tabbatar da cewa ba cutar Ebola ba ce ta kama mutanen da ake zargi, amma ana ci gaba da masu gwaje-gwaje dok tabbatar da cutar da ke damunsu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


