Ranar Laraba: Mamakon Ruwan Sama da Iska Mai Karfi Zai Jawo Ambaliya a Jihohi 3

Ranar Laraba: Mamakon Ruwan Sama da Iska Mai Karfi Zai Jawo Ambaliya a Jihohi 3

  • Hukumar NiMet ta fitar da sabon hasashen yanayi na ranar Laraba, 24 ga Satumba, 2025, inda ta yi gargadi ga 'yan Najeriya
  • NiMet ta ce akwai yiwuwar samun ambaliyar ruwa a jihohin Najeriya uku sakamakon ruwan sama mai yawa da zai sauka
  • An yi hasashen ruwan sama da iska mai karfi zai sauka a jihohin Bauchi, Gombe, Jigawa, Kano, Katsina, Yobe da dai sauransu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar kula da yanayi ta kasa (NiMet) ta yi hasashen ruwan sama da iska mai karfi a sassan Najeriya a ranar Laraba, 24 ga watan Satumba, 2025.

A cewar rahoton, mamakon ruwan sama da zai sauka zai jawo ambaliya a jihohi uku, yayin da za a iya fuskantar hadurra a titunan kasar nan.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gwabza kazamin fada da 'yan bindiga, an samu asarar rayuka

Hukumar NiMet ta ce ruwan sama da iska mai karfi zai sauka a jihohi da dama a ranar Laraba
Wasu mutane na kokarin tsallaka titi wanda ambaliya ta shanye sakamakon ruwan sama mai yawa. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Hasashen ruwan sama a Arewa

A sanarwar da NiMet ta fitar a shafinsa na X a daren ranar Talata, 23 ga Satumba, 2023, hukumar ta ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Da safiyar Laraba, akwai yiwuwar samun ruwan sama da iska mai karfi a sassan jihohin Bauchi, Gombe, Jigawa, Kano, Katsina, Kaduna, Taraba, da Adamawa, yayin da sauran yankuna za su kasance a yanayi na hadari.
"Da yammaci zuwa dare kuma, ana sa ran za a fuskanci ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a sassan jihohin Kebbi, Sokoto, Zamfara, Katsina, Adamawa, Bauchi, Kaduna, Taraba, Gombe, Kano, Jigawa, da kuma Borno da Yobe."

Game da hasashen yanayi na Arewa ta Tsakiya, NiMet ta ce akwai kuma yiwuwar saukar ruwan sama da iska a Abuja da jihohin Kogi, Nasarawa, Kwara, da Neja.

Da yammaci zuwa dare kuma, ana sa ran za a fuskanci ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a sassan Abuja da jihohin Benue, Plateau, Kogi, Nasarawa, Kwara, da Neja.

Kara karanta wannan

NiMet: Ruwan sama zai sauka a Kano, Taraba, Nasarawa da wasu jihohi a yau Talata

Ambaliyar ruwa a jihohi 3 na Kudu

Da safiyar Laraba a yankin Kudu, NiMet ta yi hasashen samun ruwan sama a sassan jihohin Legas, Ondo, Oyo, Ekiti, Osun, Delta, Bayelsa, Rivers, Akwa Ibom, da Cross River.

Da yammaci zuwa dare kuwa, an yi hasashen samun iska da ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a sassan jihohin Ogun, Oyo, Ondo, Ekiti, Osun, Bayelsa, Edo, Delta, Imo, Abia, Enugu, Anambra, Ebonyi, Rivers, Akwa Ibom, da Cross River.

Amma, hukumar ta kuma yi gargadin cewa, akwai yiwuwar a samu ambaliyar ruwa a sassan jihohin Legas, Ogun, da Oyo.

Hukumar NiMet ta ce za a samu ambaliyar ruwa a jihohi 3 sakamakon ruwan sama mai yawa ranar Laraba.
Wasu motoci da mutane na tafiya a kan titin da ambaliyar ruwa ta shanye a Legas. Hoto: Peeterv
Source: Getty Images

Shawarwari da gargadi ga jama’a

Hukumar NiMet ta yi kira ga jama'a da su yi taka tsantsan yayin da suke gudanar da ayyukansu na waje idan aka fara ruwan sama.

An shawarci masu abubuwan hawa da su yi taka tsantsan a lokacin ruwan sama saboda yadda yawan ruwa ke rage gani, wanda zai iya jawo hadurra.

Hukumar ta kuma ƙara da cewa, mazauna yankunan da suka saba fuskantar ambaliyar ruwa su ɗauki matakan kariya, don ruwa mai yawa zai sauka yau.

Kara karanta wannan

NiMet: Za a sheka ruwan sama da tsawa a Taraba, Neja da wasu jihohi a yau Lahadi

Ambaliyar ruwa ta mamaye titunan Legas

A wani labarin, mun ruwaito cewa, mazauna Alimosho a jihar Legas sun yi cirko-cirko a kan tituna bayan mamakon ruwan sama ya janyo ambaliya.

Ruwan saman da ya fara sauka tsakanin karfe 2:00 na dare ya ci gaba da sauka har zuwa karfe 10:00 na safiya a wasu sassan jihar Legas.

Hukumomin gwamnati sun gargadi wadanda ke zaune a yankin 'Command' din Alimosho da su kauracewa 'gadar Command' saboda ambaliya ta mamaye ta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com