Yadda Gwamnatin Kano Ta Dauki Nauyin Karatun Ɗalibai 240 a Jami'o'in a Najeriya
- Gwamnatin Kano ta bayar da tallafin karatun digiri na biyu ga wasu daga cikin dalibai 'yan asalin jihar a jami'o'i daban-daban
- Dalibai 240 ne su ka shiga jerin mutanen da za su rabauta da tallafin karatun da za su yi a jami’o’i masu zaman kansu a sassan kasar nan
- Duk da akwai mata a cikin daliban, gwamnati ta ce an yi masu tanadi na musamman inda za su yi karatunsu a jami'o'i masu zaman kansu a jihar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnatin Kano ta sanar da bayar da tallafin karatun digiri na biyu ga dalibai 'yan asalin jihar guda 240.
Gwamnatin ta dauki nauyin karatun ne a jami'o'i masu zaman kansu da su ke a jihohi daban-daban na kasar nan da zummar ba su damar zurfafa karatu.

Source: Facebook
Ibrahim Adam, hadimin Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka a sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya lissafa cikakken jerin jami’o’in da aka ware don tallafin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami'o'in da daliban Kano za su halarta
A sakon da ya Ibrahim Adam ya wallafa, jami'o'in da gwamnati ta amince ta aika daliban jihar sun hada da Maryam Abatcha a Kano da jami'ar Baze da ke Abuja Abuja.
Sai kuma jami'ar Skyline ita ma a Kano da jami'ar Igbinedion Okada, sai kuma jami'ar Crescent da ke Abeokuta da Bells da ke Ota.
Sauran sun hada da jami'ar Al-Hikima a Ilorin da jami'ar American ta Nigeria da ke Yola a jihar Adamawa jami'ar da kuma Alqalam a jihar Katsina.

Source: Facebook
Sanarwar ta bayyana cewa dukkanin dalibai mata da za su ci gajiyar tallafin, za a bar su ne a jami'o'in da ke jihar domin yin karatunsu.

Kara karanta wannan
Abba Gida-Gida zai rage bashin Ganduje, za a biya karin N5bn ga 'yan fansho a Kano
Martanin jama'a ga tallafin gwamnatin Kano
Bayan sanarwar, jama’a da dama sun tofa albarkacin bakinsu, inda da yawa daga cikin mabiya shafin hadimin gwamnan su ka bayyana jin dadinsu.
Murtala Muhammad Fan’ido ya ce:
"Wannan haka yake, ni ma ina daga cikin wadanda suka rabauta da wannan talllafin karatu. Babu wanda na taba tuntuba da sunan kamun kafa ko kuma hanya. Cancanta ne kawai. Muna godiya mai girma gwamna."
Mahanga ya ce:
"Me yasa ba za a biya kudin a Jami’o’in Kano da muke da su ba, wato KUST da kuma Northwest? A gani na maimaikon a daibi mukudan kudi a gina jami'o'i masu zaman kansu gwara mu gina na mu na Kano."
Umar Adam ya ce:
"Gaskiya an batawa mutane da yawa lokaci, an sa musu rai sosai. Amma wanda suka samu, Allah ya sa albarka, wanda ba su samu ba, Allah kawo damar da tafi wannan daga gwamnatin Kano ko kuma tarayya, amin."
Gwamnatin jihar Kano ta yabi dalibanta
A baya, mun wallafa cewa Jihar Kano ta samu matsayi na gaba a jerin jihohin Najeriya bisa nasarar ɗalibanta a jarabawar kammala sakandare ta NECO na shekarar 2025.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana farin cikinsa da wannan nasara, yana mai cewa hakan wata shaida ce cewa matakan da gwamnatinsa ke ɗauka a fannin ilimi suna tasiri.
A cikin ɗalibai 1,358,339 da suka zauna jarabawar, 818,492 (60.26 %) sun samu sakamako mai kyau na aƙalla darussa biyar ciki har da Turanci da Lissafi, kuma 68,159 daga cikinsu 'yan Kano ne.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

