Gwamna Radda Ya Kara Yin Zarra, An ba Shi Lambar Yabo a Masallacin Annoor
- Cibiyar Al’adu da Ilimin Addinin Musulunci ta Ƙasa da Ƙasa da ke Masallacin Anoor ta karrama Gwamna Dikko Radda da lambar yabo
- Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami ya mika wa Gwamna Radda wannan lambar yabo ta AI & Tech Award of Excellence
- Gwamnan ya yaba wa masu shirya taron, tare da jaddada aniyar gwamnatinsa ta ci gaba da tallafa wa matasa shugabannin gobe
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda, ya samu lambar yabo ta AI & Tech Award of Excellence daga Cibiyar Al’adu da Ilimin Addinin Musulunci ta Ƙasa da Ƙasa da ke Annoor Masjid, Abuja.
An karrama gwamnan Katsina ne a yayin taron Future Leaders Conference 2025 da aka gudanar a Abuja daga 19 zuwa 21 ga watan Satumba, 2025.

Source: Facebook
A sanarwar da kakakin gwamnan Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed ya wallafa a Facebook, ya ce an yabawa Dikko Radda bisa kokarinsa wajen tallafa wa matasa, kirkire-kirkire da kuma haɓaka shugabanci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Pantami ya mikawa Dikko lambar yabo
Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani ne ya mika wa gwamnan wannan lambar yabo.
Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Katsina, Abdulkadir Mamman Nasir, ne ya karɓa a madadin gwamnan.
A jawabin da aka karanta a madadinsa, Gwamna Radda ya gode wa masu shirya taron saboda jajircewarsu wajen tallafa wa matasa.
Gwamna Radda ya ba matasa shawara
Ya shawarci mahalarta taron da su rungumi kirkire-kirkire, su tsaya kan dabi’un kirki, kuma su nemi kwarewa a fannin fasahar zamani da shugabanci mai nagarta da tausayi.
"Mutanen da suka jajirce suka yi aiki tukuru, su ne gobensu za ta yi kyau, amma masu sakaci ba za su je ko ina ba," in ji Dikko Radda.
Gwamna ya kuma bukaci matasa da su tashi tsaye, su rungumi fasahar kirkire-kirkire na zamani da gaske domin gina wa kansu gobe mai kyau.
Radda ya yaba wa iyaye da malamai saboda sadaukarwar da suke yi wajen koyar da tarbiyya, inda ya bayyana au a mataayin ginshiƙan ci gaban ƙasa.
Ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da shirye-shiryen da suka mayar da hankali kan ilimi, samar ayyukan yi da kuma bunkasa harkokin kasuwancin matasa.

Source: Facebook
Matasa sun halarci taron da karrama Dikko
A nasa jawabin, Abdulkadir Mamman Nasir ya bayyana farin ciki da yawan matasa da suka halarci taron, musamman ganin yadda suka kunshi maza da mata.
Taron na tsawon kwanaki uku ya tara manyan baki ciki har da masu tsara manufofi, kwararru, malamai da masu ba da shawara ga matasa daga sassa daban-daban na ƙasar.
Wani matashi kuma malamin makaranta da ya amfana da shirin gwamnatin Katsina ma raba wayoyin IPad ya shaidawa Legit Hausa cewa Gwamna Dikko na kamantawa a gwamnatinsa.
Malamin mai suna, Ibrahim Abubakar ya shaida mana cewa duk da ba za a rasa kura-kurai na dan adam ba, amma dai gwamnati mai ci tana kokari wajen inganta rayuwar mata.
Ya ce:
"Ba zamu ce Malam Dikko ba ya kuskure ba, shi dan adam ne, amma gwamnatinsa ta na kokarin kawo sauyi, musamman bangaren fasahar zamani.
"Mu kanmu malamai an raba ma a wayoyi domin mu shigo zamani, mu rika koyarwa dta hanyar amfani da abubuwan zamani, wannan ba karamin ci gaba ba ne.
Gwamna Dikko ya nada karin hadimai 15
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya amince da nadin manyan mataimaka na musamman har guda 15.
Radda ya kuma nada shugaban hukumar kula otal da otal na Katsina domin ƙarfafa kudirin gwamnati wajen samar da sauye-sauyen da za su amfani jama'a a fadin jihar.
Manufar nade-naden shi ne aiwatar da shirin Gwamna Radda na "Gina makomarka da kanka," tare da tabbatar da isar da ayyukan gwamnati ga Katsinawa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


