Duk da Ta Koma Ofis, Natasha Ta Ki Yin Shiru, Ta Sake Bankado Wani Laifin Akpabio

Duk da Ta Koma Ofis, Natasha Ta Ki Yin Shiru, Ta Sake Bankado Wani Laifin Akpabio

  • Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta koma majalisar dattawa bayan dakatarwar watanni shida, tare da rakiyar magoya bayanta
  • A lokacin rakiyar, ’yan sanda sun harba barkonon tsohuwa don tarwatsa magoya bayanta, yayin da suke kiran Akpabio ya yi murabus
  • ’Yar majalisar ta bayyana cewa Sanata Godswill Akpabio ya dauke ta tamkar baiwa ko ’yar aiki, abin da ta kira mulkin kama-karya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta koma majalisar tarayya biyo bayan bude ofishinta a ranar Talata, bayan watanni shida da dakatar da ita.

Legit Hausa ta rahoto cewa 'yar majalisar dattawan ta isa ginin majalisar bisa rakiyar daruruwan masoyanta a safiyar Talata.

Sanata Natasha ta shiga ofishinta da ke cikin majalisar tarayya bayan watanni shida.
Sanata Natasha Akpoti tana gaisawa da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio. Hoto: @NATASHA4SEN_SRM
Source: Twitter

Natasha ta tariyo rayuwarta bayan dakatarwa

Yayin da ta shiga ofishinta, ta samu wuri ta zauna, Sanata Natasha ta zanta da manema labarai, ciki har da jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Sanata Natasha ta isa Majalisar Dattawa tare da dandazon magoya baya, an tarwatsa su

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar, ta rahoto cewa 'yar majalisar da ke wakiltar mazabar Kogi ta Tsakiya, ta sake yin sabon zargi kan shugaban majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio.

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi zargin cewa Godswill Akpabio ya mayar da ita tamkar 'yar aikin gidansa a cikin majalisar.

'Yar majalisar ta ce:

"Daga dakatar da ni da aka yi ba bisa ka'ida ba, mun tsallake tarnakin masu rufe mana hanyoyi, mun tsallake sharrin matar nan 'yar Facebook, lallai, mai rabon gani badi sai ya gani.
"Ina mika godiya ga Ubangiji, da daukacin al'ummar Kogi ta Tsakiya da ma Najeriya baki daya, musamman mijina. Ina rokon Ubangiji ya sa duk mazaje su rika goyon bayan matansu kamar yadda mijina yake mun."

Natasha ta sake caccakar Sanata Akpabio

'Yar majalisar dattawan, ta ce ta dauki duk abin da ya faru a matsayin kaddara, kuma hakan ya kara mata karfin gwiwar fadin gaskiya komai dacinta.

Kara karanta wannan

Rigima za ta kare: Majalisar dattawa ta bude ofishin Natasha bayan wata 6

"Sanata Akpabio sanata ne kamar ni, shi ba gwamnan wannan masarautar ba ne, amma a haka ya rika mu'amalantata kamar wata baiwa, ko 'yar aikinsa a majalisar nan.
"Abin takaici ne a ce a irin wannan lokaci, bayan shekaru masu yawa da samun 'yanci, a ce muna da shugabannin majalisar tarayya da ke mulkin kama karya, lallai abin takaici ne."

- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

'Yar majalisar ta ce duk da an dakatar da ita ba bisa ka'ida ba, amma ta ji dadi cewa babu ranar da ta zo ta wuce ba tare da ta gudanar da ayyuka ga mazabatarta ta Kogi ta Tsakiya ba.

Sanata Natasha ta zargi Akpabio da daukarta tamkar 'yar aiki ko baiwarsa a majalisar dattawa.
Sanata Natasha Akpoti, 'yar majalisar dattawa da ke wakiltar mazabar Kogi ta Tsakiya. Hoto: Natasha Akpoti-Uduaghan
Source: Facebook

Masoyan Natasha sun shaki barkonon tsohuwa

BBC Pidgin ta rahoto cewa 'yan sanda sun harba barkonon tsohuwa kan magoya bayan Sanata Natasha, lokacin da suka yi mata rakiya zuwa ginin majalisar tarayya.

An ce 'yan sandan sun hana magoya bayan 'yar majalisar shiga ginin, lamarin da ya tilasta su amfani da barkokon tsohuwa don tarwatsa dandazon matasan.

Ko a lokacin, magoya bayan 'yar majalisar, sun rika yin kira ga Sanata Godswill Akpabio ya yi murabus daga mukaminsa, saboda zarge-zargen cin zarafi da ake yi masa.

Kara karanta wannan

Majalisar tarayyar Najeriya ta dage ranar dawo wa da makonni 2

Kalli bidiyon tattaunawar da AIT ya wallafa a X.

An bude ofishin Natasha a majalisa

Tun da fari, mun ruwaito cewa, an bude ofishin Sanata Natasha Akpoti mai wakiltar Kogi ta Tsakiya bayan watanni shida yana kulle a majalisar tarayya.

Matakin ya biyo bayan karewar wa’adin dakatar da Natasha da aka yi saboda zargin saba ka’idojin majalisa bayan wata takaddama da Godswill Akpabio.

Majalisar dai ba ta fitar da wata sanarwa ba kan matsayin sanatar, kuma ana jiran ganin yadda za a yi lokacin da majalisar za ta sake zama a watan Oktoba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com