Zargin N3bn: Alkali Ya Fusata, an Shekara 10 ana Shari'ar Tsohon Gwamna da EFCC

Zargin N3bn: Alkali Ya Fusata, an Shekara 10 ana Shari'ar Tsohon Gwamna da EFCC

  • Mai Shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya bayyana takaici a kan shari'ar tsohon gwamna, Gabriel Suswam da EFCC
  • Mai Shari'ar ya ce ko menene ya faru, bai dace a shafe shekaru 10 ana jan kafa a shari'ar da EFCC ta shigar kan tsohon gwamnan Binuwai ba
  • A zaman kotu da aka yi ranar Litinin, lauyoyin Suswam sun bukaci kotu ta daga shari'ar saboda wasu dalilai, lamarin da ya fusata alkali

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja –Mai Shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya nuna takaici kan yadda shari’ar zargin almundahanar tsohon gwamna ta ki ci ta ki cinyewa.

Hukumar EFCC na shari'a da tsohon gwamnan Binuwai, Gabriel Suswam a kan zargin almundahanar Naira biliyan 3.1, kuma an shafe shekaru 10 ana abu daya.

Kara karanta wannan

Atiku ko Tinubu: Kawunan magoya bayan Buhari na CPC ya rabu a kan zaben 2027

Alkali ya fusata a kan shari'ar Gabriel Susawam
Hoton tambarin EFCC da tsohon Gwamna Gabriel Suswam Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Source: Facebook

Premium Times ta wallafa cewa wannan ya biyo bayan neman karin lokaci na makonni uku da lauyoyin da ke kare Suswam suka nema,.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kara dage shari'ar tsohon gwamna

Daily Post ta ruwaito cewa lauyoyin Suswam sun kara neman lokaci inda suka bayyana cewa daya daga cikin su, Chinelo Ogbozor, na kwance a asibiti saboda rashin lafiya.

Lauyoyin sun shaida wa kotu cewa:

“Ana ta wannan shari’a na da shekaru 10 yanzu. Ko menene ya faru, shari’a bai kamata ta dauki irin wannan lokaci ba."

A cewar Hukumar EFCC, an shirya zaman kotun na ranar Litinin domin ba wa lauyoyin Suswam damar su fara kare shi, amma hakan ya gagara sakamakon bukatar dage shari’ar.

Kotu: Tsohon gwamnan ya ki kare kansa

EFCC ta fara shigar da kara a kan Gabriel Suswam da tsohon kwamishinansa na kudi, Omadachi Okolobia, tun a Nuwamba 2015.

Hukumar ta zarge su da karkatar da kudin da suka fito daga sayar da hannun jari na jihar Binuwai, ta kamfanin Benue Investment and Property Company Limited.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida zai rage bashin Ganduje, za a biya karin N5bn ga 'yan fansho a Kano

Bayan shari’a ta cigaba da tafiya shekaru da dama, masu kare Suswam suka ki fara ba da shaidarsu, inda suka nemi kotu ta wanke su.

A cewar lauyoyin, EFCC ba ta gabatar da hujjoji masu karfi da zai sa a ci gaba da shari'a da wanda su ke kare wa daga zarge-zargen.

EFCC ta shafe shekaru 10 tana shari'a da Suswam
Hoton Shugaban EFCC, Olukoyode, da tambarin hukumar Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Source: Facebook

Amma a ranar 23 ga Yuli 2025, Mai Shari’a Lifu ya yi watsi da wannan bukata, ya ce akwai dalilai masu karfi da aka gano a kansu, ya kuma umarce su da su fara kare kansu.

A zaman na Litinin, Joseph Daudu (SAN), lauyan Suswam, ya ce suna da korafi a kotun daukaka kara, kuma ya nemi a dakatar da shari’ar har sai wancan kotun ta yanke hukunci.

Sai dai lauyan EFCC, Oluwaleke Atolagbe, ya ce babu bukatar jiran kotun daukaka kara tunda babu hukuncin da ke tilasta hakan.

Yanzu haka dai an dage cigaban shari’ar zuwa 10 ga Oktoba, 2025, don masu kare kansu su fara gabatar da shaidunsu.

EFCC ta cigaba da shari'a da tsohon Minista

A baya, mun ruwaito cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC) ta sake gurfanar da tsohon Ministan Wuta da Karafa, Dr. Olu Agunloye, a gaban babbar kotun tarayya.

Kara karanta wannan

Mambilla: EFCC ta maida tsohon minista gaban kotu kan zargin almundahanar $6bn

Hukumar EFCC ta mayar da shi gaban kotun da ke Apo, Abuja, bisa zargin aikata laifuffuka bakwai da suka hada da cin hanci da bijirewa umarnin shugaban kasa.

Bayan an gurfanar da shi a gaban Mai Shari’a Jude Onwuegbuzie Agunloye ya musanta dukkanin wani laifi da ake zarginsa da aikatawa, tare da cewa bita-da-kulli ake masa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng