An Fara Kokarin Taba Mutuncin Shehu Danfodiyo a Najeriya, Babban Malami Ya Yi Magana
- Sheikh Isa Talata Mafara ya bukaci a tashi a kare jihadin Shehu Usmanu Danfodio daga wasu gurbatattun mutane masu neman jirkita tarihi
- Malamin ya ce dole zuriyar Danfodiyo da sauran al'ummar musulmi su kare tarihin jihadin da Shehun ya yi don yada musulunci
- Talata Mafara ya yi wannan magana ne a wurin taron da zuriyar Marigayi Sheikh Ibrahim Maituta suka shirya a jihar Sakkwato
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto - Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Isa Talatan Mafara, ya yi kira ga zuriyar Shehu Usmanu Danfodiyo da abokan tafiyarsa da su kare mutunci da gadon da kakanninsu suka bari.
Ya yi wannan kira ne yayin taron farko na zuriyar Sheikh Ibrahim Maituta, ɗaya daga cikin kwanandojin Shehu kuma mai ɗauke tutar Danfodiyo a lokacin jihadin Sakkwato.

Source: Facebook
Sheikh Isa Talata Mafara ya soki abin da ya kira yunƙurin wasu mutane na ɓata tarihi ta hanyar bayyana Jihadin Sakkwato a matsayin kabilanci, in ji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malami ya bukaci a kare jihadin Danfodiyo
Da yake tsokaci kan karairayi da kagen da ake jinginawa jihadin Danfodiyo, Sheikh Isa ya ce:
"Dole mu tashi mu yaki wadannan kagaggun labarai, wadannan mutanen kirki sun ba da gudummuwa fiye da misali wajen yada addinin musulunci a Najeriya da Afirka.
"Sun tafi sun bar mana gado wanda ya shafi ilimi, tsoron Allah da kuma taimakon mutane."
Ya jaddada muhimmancin zumunci a tsakanin dangi da yan uwa, tare da ƙarfafa su da su ci gaba da riƙe dabi’un haɗin kai, neman ilimi da tallafawa juna.
An yabi daya daga cikin makusantan Danfodiyo
A nasa jawabin, Dr. Aminu Musa Yabo ya bayyana Sheikh Maituta a matsayin Sa'i na farko, wanda ke da alhakin tarawa da raba zakka, kuma mai kula da baitul-mali a lokacin Shehu Usmanu Danfodiyo.
Dr. Aminu Yabo ya ƙara bayyana cewa Maituta, wanda ya kasance babban malami, ya auri Khadija, ’yar Shehu Danfodiyo, inda suka haifi ’ya’ya takwas.
Daga cikin zuriyarsa akwai tsohon Mataimakin Gwamnan Sakkwato, Manir Daniya; Sa’in Kilgori na yanzu kuma babban mai ba da shawara a masarautar Sarkin Musulmi, Dr. Muhammadu Jabbi Kilgori; da tsohon Shugaban Kwastam, Alhaji Garba Muhammad Kilgori.
Waziri na Sakkwato, wanda ya wakilci Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya yaba wa gidauniyar Maituta bisa shirya taron.
Gwamnan Sakkwato ya yi nasiha
Haka nan, Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu, wanda Shugaban Ma’aikatansa, Alhaji Aminu Dikko ya wakilta, ya ƙarfafa zuriyar da su yi koyi da sadaukarwar Sheikh Maituta wajen neman ilimi da hidima ga al’umma.
“Mutanen wancan lokacin sun daraja ilimi kuma ba su yarda da zaman banza ba. Ina kira gare ku da ku riƙi neman ilimi, ku kama sana'o'i masu kyau kuma ku taimaki al'ummarku."

Source: Twitter
Sultan ya ja hankalin shugabannin Arewa
A wani rahoton, kun ji cewa mai alfarma Sarkin Musulmi ya nuna damuwa kan matsalar almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta a Arewacin Najeriya.
Sultan Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bayyana cewa wadannan matsaloli biyu ya kamata shugabannin Arewa su sa a gaba su magance su.

Kara karanta wannan
NAHCON ta nuna damuwa, Sheikh Pakistan ya hango matsalar da za a iya samu a Hajjin 2026
Sarkin Musulmi ya nuna cewa akwai miliyoyin irin waɗannan yara da suke yawo a garuruwa, birane da ƙauyuka a faɗin yankin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

