Sowore Ya Rubuta Zungureriyar Takarda ga Amurka kan Zargin Wike da Tara Kadarorin Haram

Sowore Ya Rubuta Zungureriyar Takarda ga Amurka kan Zargin Wike da Tara Kadarorin Haram

  • Mai rajin kare hakkin dan adam, Omoyele Sowore ya shigar da ƙorafi a gaban Babban Lauyan jihar Florida a kan Nyesom Wike
  • Sowore, wanda ya shigar da ƙorafin ta hannun lauyansa yana neman a kwace kadarorin da Nyesom Wike ya saya a ɓoye
  • Omoyele Sowore ya zargi Wike da sayen gidaje uku a Winter Springs, Florida da darajarsa ya kai $6m da kuɗin 'haram'

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam kuma mawallafin Sahara Reporters, Omoyele Sowore, ya rubuta ƙorafi ga Babban Lauyan jihar Florida, James Uthmeier.

A cikin zungureriyar takardar, Sowore ya nemi a kwace kadarorin da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya mallaka a ƙasar Amurka da kuɗin kasa.

Kara karanta wannan

2027: Gangar siyasa ta fara kaɗawa, Sanata ya ƙaddamar da kungiyar zaɓen Tinubu

Sowore ya mai karar Wike ga gwamnatin Florida
Hoton Ministan Abuja, Nyesom Wike Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Source: Facebook

Ƙorafin wanda lauya Deji Adeyanju ya sanya hannu a kai ranar 22 ga Satumba, 2025, kuma ya wallafa a shafinsa na Facebook ya roki gwamnatin Florida ta duba batun.

Sowore ya kai ƙarar Wike Florida

A cikin ƙorafin, Ministan Abuja, Wike da matarsa, Mai shari’a Eberechi Suzzette Nyesom-Wike na Kotun Daukaka Kara, sun mallaki gidaje uku masu tsada a Winter Springs, Florida.

Sowore ya ce jimillar kuɗin gidajen ya zarce $6m, kuma an sayi dukkanin su ne da kuɗi kai tsaye sannan aka mika kadarorin ga ƴaƴan Wike – Jordan, Joaquin da Jazmyne.

Sowore ga zargi Wike da sayen kadarorin haram a Florida
Hoton mai fafutukar kare hakkin dan adam, Omoyele Sowore Hoto: Omoyele Sowore
Source: Twitter

Bisa ƙorafin, an yi cinikin gidajen tsakanin 2021 zuwa 2023 ta wani tsari na 'quit claim deeds' kuma hakan ya kewaye tsarin biyan kudi banki.

Hanyar da aka bi wajen mallakar gidajen da biyan kudi, a cewar lauyoyin Sowore ya saba ka’ida tare da nuna alamar safarar kuɗin haram.

Kara karanta wannan

Ministan Abuja ya kawo cikas a PDP, ya dauko batun tsaida Jonathan takara a 2027

Zargin Sowore a kan Wike

Ƙorafin ya kuma ce Wike bai bayyana wadannan kadarori na ƙasashen waje ga Hukumar Ɗa'ar Ma’aikata (CCB) ba, abin da dokar Najeriya ta tilasta.

Haka kuma ya nuna cewa albashinsa a matsayin ma’aikacin gwamnati tun 1999 ba zai iya sayi kadarori masu nauyin da ya mallaka ba.

Lauyan Sowore, Adeyanju ya ambaci dokokin Florida da na Tarayyar Amurka da suka shafi halatta kuɗin haram da kwace kadarori.

Ya kuma ambaci shirin Ma’aikatar Shari’a ta Amurka na Kleptocracy Asset Recovery Initiative wanda ke bibiyar kadarorin jami’an gwamnati masu cin hanci daga ƙasashen waje. A gefe guda, Sowore ya ce abin da Wike ya yi a Florida na ɗaya daga cikin al’adar rashawa da ya saba a Najeriya.

Ya ce ana zargin Wike da mallakar filaye masu darajar biliyoyin Dala a Abuja ta hannun kamfanoni na bogi da kuma danginsa. Sowore ya bukaci Babban Lauyan Florida ya binciki asalinsu kuɗin da aka yi amfani da su wajen sayen gidajen.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Sowore ya tattaro lauyoyi, zai yi shari'a da DSS, Facebook da X a kotu

Ya kuma fara shirin kwace su, ya gurfanar da wadanda abin ya shafa gaban kotu tare da sanya takunkumi da haramta wa Wike shiga Amurka.

Wike ya tsallake rijiya da baya

A wani labarin, kun ji tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya sake waiwayar abubuwan da suka wakana a zaben gwamna na 2019 da suka jawo rudani.

Wike, wanda yanzu Ministan Abuja ne, ya bayyana cewa da gumu ya yi gumu, wani babban jami'in soja ya bayar da umarni da a harbe shi bayan siyasa ta ɗauki zafi.

Ya ce a lokacin da yake gwamna, rikicin siyasa da tsamin zabe ya kai ga wani Janar din soja ya yi watsi da umarninsa sannan ya ce a bude masa wuta nan take.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng