'Yan Bindiga Sun Bi Dare, Sun Bude Wuta a Gidan Babban Malami a Jihar Nasarawa
- 'Yan bindiga sun bude wuta yayin da suka kai hari gidan malamin addini a garin Agyaragu a karamar hukumar Obi ta jihar Nasarawa
- 'Yan ta'addan sun yi awon gaba da matar faston, Patience Nasamu da bakuwa, sun bar jariri dan watanni uku a tsakar gida
- Fasto Nasamu ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce lokacin da 'yan bindigar suka whiga gidan, yana coci wurin yiwa wani addu'ar neman lafiya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Nasarawa - Wasu ’yan bindiga sun sace Matar Fasto Samuel Nasamu na Cocin Word of God Church da ke Agyaragu a ƙaramar hukumar Obi, Jihar Nasarawa.
Rahotanni sun nuna cewa matar babban malamin addinin mai suna, Misis Patience Nasamu ta shiga hannun yan bindiga ne lokacin da suka farmaki gidan da take zaune.

Source: Original
Rahoton Leadership ya nuna cewa bayan matar malamin, maharan sun kuma hada da wata dalibarsa da ta kai ziyara gidan, sun yi awon gaba da su zuwa cikin jeji.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai ’yan bindigar sun bar jaririn faston mai watanni uku da haihuwa a gidan, abin da ya jefa garin gaba ɗaya cikin firgici.
Yan bindiga sun bude wuta a gidan malami
Shaidu sun ce maharan sun dira gidan faston ne da misalin ƙarfe 8:15 na dare, ranar Lahadi, inda suka tilasta wa matar ta buɗe musu ƙofa bayan sun yi ta harbe-harbe a sama.
Fasto Nasamu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, ya bayyana cewa 'yan bindigar sun yi ƙoƙarin karya tagogi da ƙofofin gidan da guduma, amma ba su iya shigowa ba saboda ƙarfin kariya.
Ya ce lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan kammala ibadar cocin, lokacin da ya fita ya yi wa wani mamba mai rashin lafiya addu’a.

Kara karanta wannan
Ana sulhu da 'yan ta'adda a Katsina, 'yan bindiga sun sace hakimi da wasu mata 2 a Filato
Yadda aka sace matar fasto da bakuwarsa
“Ina cikin addu’a ga daya daga cikin dalibai na masu zuwa coci wanda ke fama da rashin lafiya sai matata ta kira ni.
"Abin da kawai na ji daga gare ta shi ne addu’a, ko bayyana abin da ke faruwa ba ta iya ba. Da na iso gida, sai na tarar an sace ita da baƙuwar da ta zo garemu, an bar jaririnmu a nan,” in ji shi.

Source: Getty Images
Faston ya ƙara da cewa jami’an rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa sun ziyarci wurin domin tantance lamarin da kuma daukar matakin da ya dace.
Duk da haka, malamin ya ce har yanzu masu garkuwar ba su tuntubi iyalansa domin neman kuɗin fansa ba, in ji rahoton PM News.
'Yan bindiga sun sace dan siyasa a Kaduna
A wani labarin, kun ji cewa wasu miyagun 'yan bindiga sun farmaki kauyuka biyu a kananan hukumomin Kudan da Makarfi da ke cikin jihar Kaduna.
Yayin wadannan hare-hare da aka kai kusan lokci guda, maharan sun sace mutum uku ciki har da wani sanannen dan siyasa a yankin.
Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun afka wa mutane da dare, ba tare da tsammani ba, inda suka bude wuta a iska don tsorata jama'a.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

