Kakar Zawarawa Ta Yanke Saka, Uwargidan Gwamna Ta Fara Raba Masu Gidaje Kyauta
- Uwargidan gwamnan jihar Ebonyi, Uzoamaka Nwifuru ta fara rabawa zawarawa sababbin gidaje karkashin gidauniyar BERWO
- Gwamnatin Ebonyi karkashin jagorancin Gwamna Francis Nwifuru ce ta dauki nauyin gina gidajen da za a rabawa zawarawan
- Mata biyu da suka fara samun gida a karkashin wannan shiri, sun nuna farin ciki da godiya ga uwargidan gwamna da gwamnatin Ebonyi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ebonyi - Gwamnatin Jihar Ebonyi za ta raba sababbin gidaje na bulo masu ɗakunan kwana uku ga mata 26 da suka rasa mazajensu watau zawarawa.
Gwamnatin karkashin jagorancin Gwamna Francis Nwifuru za ta rabawa zawarawan gidaje ne a ƙarƙashin shirin 'Widow’s Housing Project'.

Source: Facebook
Vanguard ta ce shirin zai gudana ne ta hannun uwargidan gwamna, Uzoamaka Nwifuru, karkashin gidauniyarta mai suna Better Health for Rural Women, Children and Internally Displaced Persons (BERWO).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gina sababbin gidaje biyu a kowace ƙaramar hukuma daga cikin kananan hukumomi 13 na jihar Ebonyi, kuma za a bai wa zawarawa kyauta.
An fara rabawa zawarawa gidaje a Ebonyi
A wajen kaddamar da rabon gidajen a ranar Asabar, mata biyu daga cikin zawarawan da suka ci gajiyar shirin, sun nuna farin ciki bayan an mallaka masu gidajen.
Zawarawan da aka fara ba mabudan gidaje su ne, Misis Josephine Ekoyo daga kauyen Ndiegu Azu Echara a karamar hukumar Ikwo da Misis Cecilia Ogbuinya, yar kauyen Amagu Onicha a karamar hukumar Abakaliki.
Ekoyo, wacce aka mika mata mabudin sabon gida, ta ce tsawon shekaru tana rayuwa a cikin tsohon gidan da ya ruguje, wanda dangi da abokai suka riƙa gyara mata.
Yadda farin ciki ya lullube zawarawa 2
“A shekarun bayan gidan ya rufta, amma sai aka taimaka a gyara mini, ya kara ruftawa, an gyara, haka nake rayuwa har zuwa yau da na samu sabon gida,” in ji ta.
Ta gode wa Uwargidan gwamna da gwamnatin jihar Ebonyi bisa nuna soyayya da kulawa ake nuna wa ikomasu rauni a cikin al’umma.
Haka zalika, Ogbuinya, wacce ke rayuwa a cikin wani ƙaramin gida bayan ta rasa ‘ya’yanta shida, ta bayyana farin ciki tare da gode wa uwargidan gwamna.

Source: Facebook
Uwargidan gwamna ta gamsu da shirin
A jawabinta, uwargidan gwamnan Ebonyi, Uzoamaka Nwifuru ta bayyana shirin a matsayin “burii da ya zama gaskiya” da kuma cika manufar gidauniyarta.
Ta kuma bayyana gamsuwa da kammala aikin, tare da nanata alƙawarinta na dawo da fata da tsaro ga zawarawa da marayu, cewar rahoton Leadership.
“Wannan wani bangare ne na cika manufar gidauniyar BERWO wadda take da niyyar ɗaga rayuwar zawarawa a cikin al’umma. Ina farin cikin ganin an cimma burin,” in ji Uzoamaka Nwifuru.
Matashi ya yi tattaki saboda Gwamna Nwifuru
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Francis Nwifuru ya bai wa matashin da ya yi tattaki tun daga Legas zuwa Ebonyi kyautar Naira miliyan 10.
Matashin ya yi tafiyar kilomita 600 daga Ikorodu zuwa Abakaliki domin nuna godiya ga Gwamna Francis Nwifuru bisa samar da zaman lafiya a garinsu.

Kara karanta wannan
Abin kunya: An kama masu karkatar da kudin tallafin 'taki' da ake rabawa talakawa a Katsina
Kwamared Jeremiah Obaji ya samu kyaututtuka daga masoya, ciki har da mota, fili, kuɗi, da kuma tallafin Naira miliyan 10 daga Gwamna Nwifuru.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

