Tashin Hankali: An Harbe Wani Jagoran Jam'iyyar APC har Lahira a gaban Iyalinsa
- An kashe Hon. Ejeh Udeh, babban jigon jam’iyyar APC a jihar Benue, bayan wasu ‘yan bindiga sun bude masa wuta a gidansa
- Ganau sun bayyana yadda harin ya faru a gaban iyalinsa, inda matarsa da ‘ya’yansa suka shaida kisan da ya firgitar da 'yan garin
- Kisan jigon na APC ya jefa mutane cikin firgici, yayin da jama’a ke kira ga gwamnati ta gaggauta kamo wadanda suka yi kisan
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Benue - Wani mummunan al’amari ya auku a safiyar Litinin a garin Otukpo na jihar Benue, inda wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka halaka Hon. Ejeh Udeh, wani fitaccen jigon jam’iyyar APC.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan sun iso gidan marigayin da ke unguwar Ugboju da tsakar dare, kuma suka nemi wuri suka boye, suna jiran dawowarsa.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kashe ƴan sandan Najeriya 5, sun yi awon gaba da bindigoginsu a Kogi

Source: Facebook
'Yan bindiga sun kashe jigon APC
An ce, 'yan bindigar sun ga lokacin da Hon. Ejeh Udeh ya iso gidan, suka kyale shi har ya shiga ciki, sannan suka bi bayansa, inji rahoton Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Maharan, sun bude wa jigon jam'iyyar ta APC wuta a tsakiyar gidansa, a kan idon matarsa da ‘ya’yansa, lamarin ya jefa su a mummunan tashin hankali da bugun zuciya.
Makwabta sun ce sun ji karar harbe-harbe a daren, lamarin da ya tayar musu da hankula, amma ba a iya kai masa dauki ba har sai da maharan suka tafi.
An ce bayan tafiyar maharan ne, mutane suka isa gidan, inda aka tarar da Hon. Ejeh Udeh kwance cikin jini, kafin daga bisani a tabbatar da mutuwarsa.
Kisan jigon APC ya girgiza mutane
Bayan tabbatar da mutuwarsa, an ce an garzaya da gawarsa asibitin gwamnati na Otukpo inda aka adana ta a dakin ajiye gawa.
Mazauna gari da dama sun bayyana bakin cikinsu, inda suka yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro da su tabbatar da an gano wadanda suka aikata ta’asar.
Rahotanni sun nuna cewa marigayin ya kasance mutum mai karfin gwiwa wajen hada kan al’umma da kuma tallafa wa jam’iyyar APC a yankin.

Source: Original
Ana jiran martanin APC kan kisan jigonta
A halin yanzu, rundunar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro ba su fitar da wata sanarwa ba kan lamarin.
Sai dai akwai kiraye-kirayen gaggawa daga ‘yan siyasa da al’ummar Otukpo da su hanzarta bincike domin kawo adalci ga iyalan mamacin.
Kisan Hon. Udeh ya sake jefa jihar Benue cikin firgici, domin a 'yan kwanakin nan an samu hare-hare, garkuwa da mutane da tashin hankula a wasu sassan jihar.
Yanzu haka, magoya bayan jam’iyyar APC da sauran jama’a na jiran yadda gwamnati za ta dauki mataki, yayin da ake sa ran manyan jiga-jigan jam’iyyar za su fitar da sanarwa.
'Yan bindiga sun kashe kusa a APC
A wani labarin makamancin wannan, mun rahoto cewa, 'yan bindiga sun kashe jigon APC, Akaabo Johnson da wasu mutum uku a jihar Benue.
An kashe Mista Akaabo Johnson ne a harin da 'yan bindigar suka kai garuruwan Mbalom da Mbasombo a karamar hukumar Gwer ta Gabas
Shugaban karamar hukumar Gwer ta Gabas, Timothy Adi ya yi tir da wannan harin, yana mai cewa wannan ne hari na biyu cikin makwanni biyu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

