Mutanen da Ake Hasashen Za Su Maye Gurbin Mahmood Yakubu a Shugabancin INEC

Mutanen da Ake Hasashen Za Su Maye Gurbin Mahmood Yakubu a Shugabancin INEC

FCT, Abuja - Wa'adin Farfesa Mahmood Yakubu a matsayin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ya kusa karewa.

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Farfesa Mahmood Yakubu zai kammala wa'adinsa a shugabancin hukumar INEC a watan gobe.

Mutanen da za a iya nadawa shugabancin INEC
Hoton Farfesa Lai Olurode, Sam Olumekun da Kenneth Ukeagu Hoto: Demola Adefajo, INEC Nigeria, Emmanuel C. Nwachukwu
Source: Facebook

Mahmood Yakubu ya kafa tarihi a INEC

Jaridar Daily Trust ta yi duba kan mutanen da za su iya maye gurbin Farfesa Mahmood Yakubu daga shugabancin INEC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An nada Farfesa Mahmood Yakubu a shugabancin hukumar INEC a shekarar 2015.

Tsohon shugaban kasa, marigayi Muhammadu Buhari ya sake nada shi kan mukamin a shekarar 2020, kamar yadda wata sanarwa a shafin statehouse.gov.ng ta tabbatar.

Hakan ya sanya ya zama shugaban hukumar INEC wanda ya fi dadewa kan kujerar a tarihin Najeriya.

Yayin da wa'adinsa ke shirin karewa, tambayar wanda zai gaje shi tana kara ɗaukar hankalin ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

INEC: Yakubu ya fadi dalilin ajiye aiki, Tinubu ya shirya nada magajinsa makon nan

Mutanen da ake hasashen za su shugabanci INEC

Ga jerin mutanen da ake hasashen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai iya nadawa a shugabancin hukumar INEC.

Mutum biyu daga cikinsu sun fito ne daga yankin Kudu maso Yamma.

1. Abdullahi Mohammed Liman

An haifi mai shari’a Abdullahi Mohammed Liman a ranar 11 ga watan Fabrairu, 1959, kuma ya zama lauya a shekarar 1984.

Abdullahi Mohammed Liman dan asalin jihar Nasarawa ne, da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya.

Ya fara aikin lauya a Nasarawa kafin daga bisani ya koma Abuja, daga nan aka naɗa shi a matsayin alkalin kotu yana da shekara 42 a ranar 27 ga Yuli, 2000.

Mai shari’a Abdullahi Mohammed Liman ya sha shiga cikin shari’o’i masu ce-ce-ku-ce.

Daga cikinsu akwai hukuncinsa na dakatar da maido da Sanusi Lamido Sanusi a matsayin Sarkin Kano na ɗan lokaci, da kuma umarninsa na dakatar da yunkurin cafke tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje.

Kara karanta wannan

Abin da Tinubu ya fada da Shugaban INEC ya ajiye aiki, ya ba shi kyautar sallama

2. Bashiru Olamilekan

A farkon shekarar nan, an yada jita-jitar cewa an naɗa Farfesa Bashiru Olamilekan domin ya maye gurbin Farfesa Mahmood Yakubu, amma daga bisani aka gano ba gaskiya ba ne.

Ana ɗaukar shi a matsayin ɗaya daga cikin mutanen da za a iya nadawa a shugabancin hukumar.

3. Sam Olumekun

Sam Olumekun wanda ya fito daga jihar Ondo, kwamishina ne a hukumar INEC kuma yana jagorantar kwamitin wayar da kan masu kada kuri’a.

Ya taɓa rike muhimman mukamai da dama a cikin gwamnati da kuma hukumar zabe.

Ana hasashen Sam Olumekun ya zama shugaban hukumar INEC
Hoton kwamishina a hukumar INEC, Sam Olumekun Hoto: @inecnigeria
Source: Twitter

Hakazalika ya taba zama babban sakatare a fadar gwamnatin jihar Ondo kafin ya koma aiki a hukumar INEC.

Sam Olumekun ya yi aiki a matsayin kwamishinan zabe na jiha a Edo daga 2014 zuwa 2017, sannan daga baya a jihar Legas daga 2017 har zuwa karshen wa’adinsa a 2020.

4. Lai Olurode

An haifi Farfesa Lai Olurode a ranar 2 ga Nuwamba, 1952 a garin Iwo, jihar Osun.

Kara karanta wannan

Farfesa Mahmood Yakubu ya sauka daga mukamin shugaban INEC

Ya kammala karatun digirinsa na farko a fannin Sociology a jami’ar Legas (UNILAG) a shekarar 1979 da sakamako mai daraja ta farko.

Lai Okurode ya sake yin digirinsa na biyu a fannin ilmin halayyar 'Dan Adam a jami'ar UNILAG. Daga baya ya yi digirin digirgir a jami’ar Sussex, Birtaniya, a 1984.

Ya kuma yi karatun lauya a jami’ar UNILAG inda ya samu LL.B a shekarar 1990, sannan ya zama cikakken lauya a 1991.

An naɗa shi a matsayin kwamishinan INEC a ranar 30 ga Yuni, 2010, inda ya kula da jihohin Oyo, Ogun da Ekiti.

5. Kenneth Ukeagu

Kenneth Ukeagu tsohon darakta ne a hukumar zabe ta INEC.

Masanin ilmin halayyar 'Dan Adam ne kuma dan asalin jihar Abia. Ya shafe fiye da shekaru 30 yana aiki a hukumar INEC.

Jaridar Tribune ta ce tsohon shugaban kasa, marigayi Muhammadu Buhari ya naɗa shi a matsayin kwamishina a hukumar INEC.

6. Joash Amupitan

Farfesa Joash Amupitan ya fito ne daga Aiyetoro-Gbede a Karamar Hukumar Ijumu ta Jihar Kogi, wacce ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya.

Kara karanta wannan

Sanata Barau ya tabo batun tazarcen Tinubu, ya hango abin da mutanen Kano za su yi a 2027

An haife shi a watan Afrilu, 1967 a garin Aiyetoro-Gbede da ke jihar Kogi, inda yanzu yake da shekara 58.

Ya zama babban lauya a Najeriya wato SAN a watan Agustan shekarar 2014.

7. May Agbamuche-Mbu

An haifi Agbamuche-Mbu a Kano amma asalinta 'yar asalin jihar Delta ce da ke yankin Kudu maso Kudu na Najeriya.

Ta zama kwamishiniyar kasa a hukumar INEC a shekarar 2016.

Kafin ta shiga INEC, Agbamuche-Mbu ta kasance babbar lauya kuma abokiyar kafa kamfanin Norfolk, wani sanannen ofishin lauya da ke Legas.

Galadima ya yi gargadi kan nada shugaban INEC

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban kusa a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi gargadi mai zafi kan nada sabon shugaban hukumar INEC.

Buba Galadima ya ja kunnen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wajen nada wani alkalin kotun daukaka kara a shugabancin INEC.

Jigon na NNPP ya yi gargadin cewa na da alkalin ka iya haifar da yakin basasa a kasar nan, idan ba a yi taka tsan-tsan ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng