Gwamnatin Sokoto Ta Bude Shafin Daukar Matasa 3,000 Aiki, Ana Bukatar Takardu 4
- Gwamnatin Sokoto ta sanar da bude shafin daukar matasa 3,000 masu kwalin NCE, HND da Digiri aiki a ma'aikatu daban daban
- Za a fara daukar ma’aikatan ne daga yau Litinin, 22 ga Satumba, 2025, kuma za a rufe shafin daukar aikin a ranar 6 ga Oktoba, 2025
- Kwamitin daukar ma'aikatan Sokoto, ya bayyana takardun da ake bukata don neman aikin da suka hada da takardar haihuwa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sokoto - Gwamnatin Sokoto ta sanar da cewa za ta fara daukar sababbin ma’aikata daga ranar Litinin, 22 ga Satumba, har zuwa 6 ga Oktoba, 2025.
Sakataren kwamitin daukar ma’aikata, Barista Gandi Muhammad, ya ce an kaddamar da shirin ne domin ba matasan jihar damar samun aiki a ma’aikatun gwamnati.

Source: Facebook
An bude shafin daukar aiki a Sokoto
Jaridar Punch ta rahoto Barista Gandi yana cewa wadanda suka cancanta za su iya karɓar fom kyauta daga ƙaramar hukumarsu, kafin daga bisani su cike fom ɗin a shafin yanar gizo: employment.sokotostate.gov.ng
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gandi Muhammad ya ce dole ne masu masu neman aikin su yi rajista da adireshin imel da lambar wayarsu na gaskiya, su kuma shigar da takardu masu inganci.
Takardun da ake bukata sun haɗa da shaidar kammala makaranta, takardar asalin ɗan ƙasa, takardar haihuwa, da lambar NIN. Za a kuma buƙaci ɗaukar hoton fasfo kai tsaye yayin cikewa.
Ya jaddada cewa cike fom da na yanar gizo kyauta ne gaba ɗaya, sannan duk wanda ya yi kuskuren cike fom din sau biyu zai iya rasa damar samun aikin.
Gwamnati ta ba matasan Sokoto shawara
Kwamitin ya bayyana cewa za a rika tura sakonni kai tsaye ta imel ko sakon kartakwana ga wadanda suka cancanta.
Ya bayyana cewa ta imel, ko shafin yanar gizo ne kawai wadanda suka cancanta za su ga sakon wucewa mataki na gaba, ko kiran tattaunawa.
Haka kuma, an gargadi jama’a da su guji biyan kowa wani kuɗi domin neman aikin, kwamitin yana mai cewa za a dauki ma'aikatan ne bisa cancanta.
“Muna kira ga matasa da su yi amfani da wannan dama domin samun aikin gwamnati cikin sauki, kuma bisa gaskiya da adalci."
- Barr. Gandi Muhammad.

Source: Original
Matasa 3,000 za a ba aiki a Sokoto
Mai magana da yawun gidan gwamnati, Mallam Abubakar Bawa, ya bayyana cewa Gwamna Ahmed Aliyu ya amince da daukar ma’aikata 3,000 daga ƙananan hukumomi 23 na jihar.
Gwamnan ya ce shirin zai rage zaman banza, ya kuma ƙarfafa ma’aikatun gwamnati da suka shafi lafiya, ilimi, da sauran fannoni na ci gaban jama’a, inji Premium Times.
Ya ce matasa masu NCE, HND ko digiri za su fi samun dama a shirin, domin gwamnati tana da niyyar mayar da hankali wajen ba su ayyukan da za su ciyar da jihar gaba.
Gwamna Fintiri zai dauki matasa aiki
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin jihar Adamawa za ta dauki matasa 12,000 aiki kafin Disambar 2025 domin yaki da rashin aikin yi.
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ne ya bayyana hakan a yayin ganawarsa da kungiyar kiristoci mata ta WOWICAN, a ziyarar da suka kai ofishinsa.
Gwamnan ya shaidawa kungiyar cewa gwamnatinsa ta daura damarar kafa tubalin ci gaba a ilimi, lafiya da sauransu ga kowane dan Adamawa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


