Zaman Sulhu: Sheikh Gumi Ya Gargadi Jami'an Tsaro kan 'Yan Ta'adda
- Fitaccen Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana gamsuwa da yadda mazauna Katsina ke sulhu da 'yan ta'adda
- Ya bayyana haka ne bayan an samu labarin cewa an sake zama da wasu shugabannin 'yan ta'adda da mazauna karamar Sabuwa a Katsina
- Sheikh Gumi ya nemi gwamnati ta bi tsarin sulhu irin na Neja Delta wajen koya wa tubabbun yan ta'addan muhimmancin zaman lafiya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Katsina – Shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi gargadi a kan kawo wa shirin zaman lafiya a Katsina barazana.
Sheikh Gumi, ya shahara wajen kiraye-kirayen sasanci da ’yan bindiga a matsayin hanya mafi dorewa don kawo karshen matsalar.

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya sake nanata wannan matsayi bayan zaman tattaunawa da aka gudanar a wasu yankuna na jihar a ’yan makonnin da suka wuce.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Ahmad Gumi ya yabi zaman sulhu
A ranar Asabar, 13 ga watan Satumba, wasu fitattun shugabannin ’yan bindiga da hukumomi ke nema ruwa a jallo sun bayyana a tattaunawar zaman lafiya a Matazu da Faskari.
Sheikh Gumi ya ce irin wannan matakin da aka dauka a Karamar Hukumar Sabuwa yana da matukar muhimmanci wajen dorewar zaman lafiya.
Ya bukaci jami’an tsaro da shugabannin gargajiya su guji duk wani abu da zai rusa wannan sabuwar fahimta a tsakanin 'yan ta'adda da jama'a.
Malamin ya bukaci gwamnati da ta yi amfani da tsarin sake janyo hankalin masu dauke da makami kamar yadda aka yi da tsofaffin ’yan awaren Neja Delta.

Source: Facebook
Ya ce:
“Alhamdulillah. Mun samu labarin cewa a yau, Karamar Hukumar Sabuwa ta kulla zaman sulhu da ’yan bindiga da ke cikin dazuka don tabbatar da zaman lafiya a dukkannin yankin."
Addu'ar Gumi kan sulhun 'yan ta'adda
Sheikh Ahmad Gumi ya yi addu'a a kan masu kokarin rura wutar rikicin da tsakanin mazauna sassa daban-daban da 'yan ta'adda.
A cewarsa:
"Masu hura wutar Yaki, Allah Ya dakushe su. Kuma Jami'ai su guji bata wannan sulhu, har a koyar da su zaman lafiya, kamar yadda a ka yi wa yan bindigar Neja delta. Allah Ya kawo mana zaman lafiya. Amin."
Kalaman fitaccen malamin sun jawo cece-kuce a tsakanin masu bibiyar shafinsa, inda wasu ke ganin kamar yana goyon bayan abin da 'yan bindiga ke aikatawa.
Wasu kuma na ganin cewa gazawar gwamnati ce ta sanya jama'a su ka fara nemo mafita domin su samu saukin kashe su da ake yi ba dare ba rana.
Sheikh Gumi ya dura kan tsohon Gwamna
A wani labarin, kun ji cewa shahararren malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya yi zazzafan martani kan sauya shekar Nasir El-Fufa'i.
Sheikh Gumi ya bayyana cewa El-Rufa’i, wanda a baya ya yi rusau da zaluntar mutane yayin da yake kan mulki, yanzu ya koma kuka da sukar gwamnati da saboda ya rasa madafun iko.
Sheikh Gumi ya ce halin da El-Rufa’i ya shiga yanzu ya kamata ya zama wa’azi ga sauran shugabanni, musamman wadanda ke kan karagar mulki suna abin da su ka ga dama.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


