Turken Wutar Lantarki Ya Lalace, Yankuna da Dama Sun Fada cikin Duhu a Kaduna

Turken Wutar Lantarki Ya Lalace, Yankuna da Dama Sun Fada cikin Duhu a Kaduna

  • Babban layin wutar lantarki na kamfanin TCN ya lalace a Kaduna, lamarin da ya jefa jama’a da kasuwanni cikin duhu a Rigasa
  • Ruwan sama da iska mai karfi aka ce suka haddasa lamarin, bayan barayin karafa sun sace wasu muhimman sassan layin wutar
  • TCN ta umarci KAEDCO ya haɗa tashar wutar Mogadishu da ta Abakwa domin rage radadi ga yankunan da abin ya shafa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Dubban gidaje da kasuwanni a Kaduna sun fada cikin duhu bayan rugujewar babban turken wutar lantarki na kamfanin wuta na Najeriya (TCN).

Mai magana da yawun TCN, Ndidi Mbah, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa turken wuta na bakwai na Kaduna, mai dauke da layin wuta na daya da na biyu ne ya lalace.

Kara karanta wannan

Trump ya ce an masa makarkashiya bayan ya samu matsaloli 3 a taron UN

An dauke wutar lantarki a wasu yankunan Kaduna bayan rushewar turken wuta.
Hoton turken wutar lantarki, da wani gari cikin dare amma da wutar lantarki. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

TCN: Wutar lantarki ta lalacewa a Kaduna

Kamfanin TCN ya wallafa sanarwar Ndidi Mbah a shafinsa na X, yana mai cewa lamarin ya shafi yankin Rigasa, karamar hukumar Igabi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta kara da cewa mamakon ruwan sama da iska mai karfi a ranar Alhamis, 18 ga Satumba, 2025, ne ya jawo lalacewar babban layin rarraba wutar.

TCN ta bayyana cewa iska mai karfi ta karya layin wutar, amma barayin karafa sun kara dagula matsalar ta hanyar sace muhimman sassan layin.

Ndidi Mbah ya ce injiniyoyin TCN sun gano cewa an lalata wasu kayayyakin layin wutar da da gangan, wanda ya sanya iskar ta iya lalata shi cikin sauki.

Bayanin TCN kan lalacewar wuta

Sanarwar TCN ta ce:

"Kamfanin wutar lantarki na Najeriya (TCN) na sanar da al'ummar jihar Kaduna cewa turken layin wutarmu na bakwai da ke daukar layin wuta na I da na II a Rigasa ya lalace.

Kara karanta wannan

Bincike: NSIB ta fadi abubuwa 2 da suka jawo hadarin jirgin kasar Kaduna zuwa Abuja

"Rushewar husumiyar ya jawo katsewar samar da wutar lantarki ga kamfanin rarraba wutar lantarkin Kaduna (KAEDCO), musamman a bangaren da ya shafi Kudancin Kaduna.
"A yayin da aka je ana binciken lamarin, TCN ta gano cewa wasu barayi sun sace wasu muhimman kayayyakin husumiyar, wanda ya jawo rushewarta cikin sauki."
Kamfanin TCN ya ce yana iya kokarinsa don gyara matsalar wutar lantarki da aka samu a Kaduna.
Taswirar Kaduna da ke a Arewa maso Yammacin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Matakan da TCN ya dauka a Kaduna

Don rage tasirin lalacewar wutar, TCN ya umarci kamfanin KAEDCO da ya hada tashar wutar lantarkin Mogadishu mai karfin 33kV da tashar wutar Abakwa mai karfin 33kV domin samar da wuta.

Wannan matakin zai ba wasu yankunan jihar damar samun wuta, musamman yankin Mogadishu, yayin da ake ci gaba da aikin gyara a inda wutar ta lalace.

Sanarwar ta ce tuni injiniyoyin TCN sun fara shirin sake gina sabon turken wutar cikin kankanin lokaci don dawo da wuta a yankin Rigasa.

Ndidi Mbah ya ce:

“Muna bada hakuri ga al’ummar da abin ya shafa bisa tankardar da aka samu, muna kuma godiya bisa juriya da fahimtarmu da ake yi.”

Amma ya ce katsewar wutar ba ta shafi yankuna kamar Kinkinau, Yan Tukwane, Kabala West, Unguwan Muazu, da Kaduna ta Arewa ba.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An yi kutse a shafin gwamnatin Najeriya, an wallafa wata takarda

Abin da 'yan Makarfi suka ce

A zantawar Legit Hausa da wasu 'yan layin Makarfi Road, Rigasa Kaduna, wadanda lamarin ya shafa, sun nuna cewa sun shiga damuwa saboda lalacewar wutar.

Hussaini Baban Nur ya ce:

"Tun shekaran jiya da aka yi wani ruwa mai karfi da iska, na ji a raina wuta za ta samu matsala. Washe gari kuwa muka ga ta lalace. Akwai gidajen da katangunsu suka rushe, bishiyoyi sun kakkarye. An yi iska mai karfi a ranar."

Amina Lawal ta ce:

"Ni ai har daren ya wuce ban runtsa ba, saboda wallahi iskar ta rika daga kwanon gidanmu, kamar za ta tafi da shi. Ruwan da aka yi kuwa, sai dai mai dauriya kawai, amma sai ka dauka ko dai ruwan hukunta mutane ne a kan laifuffukansu."

Wani mai sayar da kifi a nan Makarfi Road da ya nemi a sakaya sunansa ya ce:

"Kwana na biyu kenan babu wuta, kifi na ya fara saki, kankarar jikinsa ta fara narkewa, dama dai ba wutar kirki ake samu ba, to gashi kuma ta lalace."

Kara karanta wannan

'Dan majalisa Gabdi ya ce gwamnoni ne matsalar kasar nan, ya ba talakawa shawara

Ya ce yana fargabar kifinsa ya lalace kafin a gyara wutar, wacce ya ce babu wata alama ta za a gyara ta nan kusa.

Tushen wutar lantarki na kasa ya lalace

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tushen wutar lantarki na Najeriya ya sake lalacewa, lamarin da ya jawo daukewar wuta a fadin kasar.

Kamfanin rarraba wuta na Abuja (AEDC) ya fitar da sanarwa, da ta tabbatar da katsewar wuta a yankunan da yake kula da su a ranar 10 ga Satumba, 2025.

An rahoto cewa, karfin wutar lantarki ya ragu zuwa megawatt 50 kacal ga kamfanonin rarraba wutar lantarki na ƙasar, bayan matsalar da aka samu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com