Sabuwar Cuta Mai Cin Naman Jiki Ta Bulla a Adamawa, Gwamnati Ta Fara Bincike
- Akalla mutane 67 sun kamu da cuta mai cin naman jiki a Adamawa, inda mutane bakwai suka mutu, aka yiwa takwas tiyata
- Ana zargin cutar Buruli Ulcer ce, wacce kwayar Mycobacterium ulcerans ke haifarwa, amma masana ba su tabbatar ba tukuna
- Hukumar lafiya ta yi kira ga jama’a da su daina danganta cutar da sihiri, tare da neman magani domin kauce wa mace-mace
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin tarayya ta fara bincike a dakin gwaje-gwaje domin gano musabbabin barkewar wata sabuwar cuta da ke cin naman mutum a Adamawa.
An ruwaito cewa, cutar, wadda ta bulla a garin Malabu, da ke karamar hukumar Fufore, ta kashe akalla mutane bakwai zuwa yanzu.

Source: Twitter
Cuta mai cin naman mutum ta bulla a Adamawa
Dr Adesigbin Olufemi, mukaddashin kwamishinan shirye-shiryen kula da cututtuka irin su tarin fuka, Buruli Ulcer da kuturta, ya bayyana hakan a hira da NAN a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce daga ranar 10 ga Satumba, an tabbatar da cutar a jikin mutane 67, inda aka yi wa takwas daga cikinsu tiyata a Asibitin Koyarwa na Modibbo Adama, da ke Yola.
Rahotanni sun nuna cutar kan fara da kuraje masu ruwa, daga bisani ta fashe ta fara cin naman jiki, wani lokaci har ta lalata ƙashi.
Dr. Olufemi ya bayyana cewa har yanzu ba a tabbatar da musabbabin cutar ba, amma ana zargin Buruli Ulcer ce, wacce cutar Mycobacterium ulcerans ke haifarwa.
Ya ce wannan kwayar cuta na rayuwa ne a wuraren da ruwa ke taruwa, da kogunan da ba sa gudana, kuma har yanzu ba a gano yadda ake yada cutar ba.
Adamawa ta kai dauki, REDAID ta tallafa
Mukaddasshin ya yaba da yadda gwamnatin Adamawa, tarayya, kungiyoyin tallafi tare da kungiyar REDAID suka kai dauki wurin tun 14 ga Satumba, inji Daily Trust.
Ya ce marasa lafiya da cutar ba ta tsananta a jikinsu ba na karbar magani a ƙananan asibitoci, yayin da ake yi wa wadanda suka tsananta tiyata a manyan asibitoci.
Ya jaddada cewa wayar da kan jama’a na da muhimmanci, domin wasu mazauna yankin sun alakanta cutar da sihiri, abin da ya jinkirta neman magani da wuri.

Source: Original
Bukatar tsaftar ruwa da hanyoyin kiwon lafiya
Dr. Olufemi ya bayyana cewa Malabu gari ne mai nisa, da ke da tazarar awa biyu daga Yola, kuma rashin hanyoyi ya jinkirta isar da agaji cikin gaggawa.
Ya ce tsaro na dogon lokaci kan kiwon lafiya ya shafi tsaftar ruwa da muhalli, domin jama’a za su rage zuwa koguna idan akwai rijiyoyin burtsatse da kuma na famfo.
Hukumar lafiya ta ƙasa ta tabbatar da cewa gwamnati tare da abokan hulɗa suna nan kan bakansu na kula da marasa lafiya da kuma hana yaduwar cutar.
'Babu Ebola a Abuja' - NCDC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar NCDC ta ce ba a samu cutar Ebola ko Marburg a jikin mutane biyu da ake zargin sun kamu da su ba a Abuja.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Bam ya tarwatse da yara 'yan firamare suna wasa cikin aji a Benue
Dr Jide Idris, shugaban NCDC ya ce yanzu haka an yi wa mutanen gwaje-gwaje kan zazzabin Lassa don gano abin da ke damunsu.
NCDC ta gargadi jihohi da su ƙarfafa sa ido, su shirya cibiyoyin killace mutane yayin da aka sake samun bullar Ebola a wasu kasashe.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

