'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Hadimin Gwamnan Nasarawa

'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Hadimin Gwamnan Nasarawa

  • 'Yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari har cikin birnin Lafia, babban birnin jihar Nasarawa, inda su ka tafka ta'asa
  • Tsagerun sun yi harbi kan mai uwa da wabi kafin daga bisani su nufi wajen wanda su ka zo daukewa
  • 'Yan bindigan sun yi awon gaba da daya daga cikin hadiman gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, a yayin harin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Nasarawa - Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace hadimin gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule.

'Yan bindigan sun sace Dr. Muhammed Egye Osolafia, wanda aka fi sani da Deedat, wanda yake shi ne mataimaki na musamman kan harkokin jin kai ga Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa.

'Yan bindiga sun sace hadimin gwamnan Nasarawa
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule Hoto: Abdullahi A. Sule Mandate
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa an sace Dr. Muhammad Egye Osolafia ne daga gidansa da ke garin Lafia, babban birnin jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan

Abin fashewa ya tarwatse a masana'antar sojojin Najeriya, an rasa rayuka

'Yan bindiga sun sace hadimin Gwamna Sule

Rahotanni sun nuna cewa an yi garkuwa da shi ne bayan ya iso gidansa da ke unguwar Tudun Amba a daren ranar Asabar.

Maharan sun iso yankin suna harbe-harbe a iska, kafin su nufi inda hadimin gwamnan yake.

Abokin aikinsa, Mista Peter Ahemba, wanda shi ne mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin jama’a, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Mista Peter Ahemba, wanda ya bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki kuma abin takaici, ya ce ya samu labarin sacewar ne daga wani abokin aikinsu.

Sace Osolafia ta faru ne kimanin watanni biyu bayan an yi garkuwa da Yusuf Musa, babban sakatare a ma’aikatar yaɗa labarai da al’adu, daga gidansa da ke Ungwan Nungu, a cikin birnin Lafia.

Me 'yan sanda su ka ce kan lamarin?

Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa, SP Ramhan Nansel, game da lamarin ba a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Ana batun sulhu, dakarun sojoji sun dakile harin 'yan bindiga a Katsina

Legit Hausa ta kira layin wayarsa amma bai dauka ba.

'Yan bindiga sun yi garkuwa da hadimin gwamnan Nasarawa
Shugaban 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

Karanta wasu karin labaran kan 'yan bindiga

Sojoji sun dakile harin 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro sun yi artabu da 'yan bindiga bayan sun kai wani hari a jihar Katsina.

'Yan bindigan dai sun kai harin ne a wasu kauyuka biyu na karamar hukumar Kusada da sassafe.

Dakarun sojojin tare da hadin gwiwar 'yan sanda da jami'am rundunar C-Watch sun yi nasarar dakile harin da 'yan bindigan su kai bayan an yi musayar wuta mai tsanani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng