Wata 2 Kacal da Shiga Ofis, Yar Sarki kuma Mataimakiyar Shugaban Karamar Hukuma Ta Rasu

Wata 2 Kacal da Shiga Ofis, Yar Sarki kuma Mataimakiyar Shugaban Karamar Hukuma Ta Rasu

  • Mataimakiyar Shugaban Karamar Hukumar Badagry ta Yamma a jihar Legas, Princess Oluremi Ajose, ta rasu watanni biyu da kama aiki
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa ta rasu a ranar Asabar, abin da ya girgiza al’ummar yankin da ke Badagry.
  • Marigayiyar diyar Sarkin Apa Egun-Awori, Oba Oyekan Possi Ajose ce, lamarin da ya kara zurfafa jimami a gidan sarauta da al’umma

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Badagry, Lagos - Mataimakiyar Shugaban Karamar Hukumar Badagry ta Yamma a jihar Legas ta riga mu gidan gaskiya.

An tabbatar da cewa marigayiyar, Princess Oluremi Nutayi Ajose, ta rasu watanni biyu bayan ta hau kujerar mulki.

Mataimakiyar shugaban karamar hukuma ta rasu a Lagos
Marigayiya Oluremi Ajose da Gwamna Babajide Sanwo-Olu. Hoto: Hon. Ajose Peter Kumayon.
Source: Facebook

An yi rashin yar siyasa a Lagos

Shugaban karamar hukumar Olorunda, Hon. Ajose Peter Kumayon shi ya tabbatar da haka a yau Lahadi a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Rai bakon duniya: An yi rashin babban malamin Musulunci a Adamawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ajose ya yi jimamin mutuwar marigayiyar inda ya ce tabbas sun yi babban rashi mata jajirtacciya inda ya yi mata addu'a.

Ya ce:

"Cikin alhini da bakin ciki, ni, Hon. Ajose Peter Kumayon, Shugaban Karamar Hukumar Olorunda, na karɓi labarin mutuwar ƙanwarmu , Princess Oluremi Nutayan Ajose.
"Marigayiyar kafin rasuwarta, ita ce mataimakiyar Shugaban Karamar Hukumar Badagry ta Yamma a Lagos.
"Princess Oluremi ƙwararriya ce kuma baiwar Allah, shugaba ce mai tausayawa, tawali’u, da jajircewa wajen bunƙasa ci gaban ƙananan al’ummomi."

Daga bisani, Hon. Ajose ya bayyana gudunmawar da ta bayar da kuma yi mata addu'ar samun rahama a gobe kiyama.

Ya kara da cewa:

"Sadaukarwarta da zuciya kmai yau da take da shi sun taɓa rayuka da dama a Badagry da wajenta wurin ingata rayuwarsu."
A madadin Gwamnati da mutanen Olorunda, ina mika ta’aziyyata ga iyalinta, hukumomi a Badagry ta Yamma, da dukan dangin Ajose.
"Allah ya ba mu juriyar ɗaukar wannan rashi marar gushewa, kuma Allah ya jikan rayuwarta cikin tausayawa da cikakken salama."

Kara karanta wannan

Bayan rasuwarta, shugaba Tinubu ya tuna 'ya'yan marigayiya, ya ba su aiki a Abuja

An yi rashin mataimakiyar shugaban karamar hukuma a Lagos
Taswirar jihar Lagos da ke Kudu maso Yamma a Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Yaushe marigayiyar ta shiga ofis?

Rahotanni daga garin Badagry sun tabbatar da cewa marigayiyar ta rasu ranar Asabar 20 ga watan Satumbar 2025, abin da ya girgiza yan siyasa da al’ummomin yankin.

Ajose, wadda aka rantsar ranar 27 ga Yuli 2025 tare da shugaban karamar hukuma, Hon. Rauf Ibrahim Kayode Yemaren, sun kama rantsuwa bayan nadin Gwaman Babajide Sanwo-Olu.

Iyalan sun tabbatar da rasuwarta, inda suka bayyana cewa an kai gawarta dakin ajiye gawa domin ci gaba da shirye-shiryen jana’iza.

Princess Ajose ita ce diya ga Mai Martaba Oba Oyekan Possi Ajose, Alapan Apa Egun-Awori, abin da ya kara ta da jimami a masarautar yankin.

Kansila ta rasu mako 2 da shiga ofis

A baya, mun ba ku labarin cewa zababbar kansila ta Ibeju-Lekki, Oluwakemi Rufai, ta rasu kasa da makonni biyu da rantsar da ita.

Shugabannin karamar hukuma da APC sun bayyana rasuwar a matsayin babban rashi, yayin da aka yabawa da jarumtarta.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya isa jihar Kaduna domin halartar daura auren 'dan tsohon gwamna

Wasu 'yan Najeriya sun nuna alhini kan rasuwar kansilar yayin da wasu suka nuna damuwa kan rashinta da ta rasu a ranar 13 ga watan Agustan 2025.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.