An Saki Sunayen Sababbin Sarakuna 20 da Mai Martaba Sarki Ya Nada a Lokaci Guda
- Ooni na Ile-Ife, Oba Ogunwusi, ya nada sababbin sarakuna 20 a jihar Osun, ya jaddada cewa an yi nadin ne domin kara hidima ga jama’a
- Daga cikin wadanda aka nada akwai Obajio na Moore, Olu na Erinle da Olu na Ifeparapo, Adetoro na Awoyaya da Olu na Abeji
- An bukaci sababbin sarakunan da su yi mulki da hikima da tawali’u, su kuma raya al’adu da ci gaban tattalin arzikin al’ummominsu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Osun - Babban Ooni na Ile-Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, ya nada sababbin sarakuna 20 a fadar Oodua dake Ile-Ife, Jihar Osun, a ranar Asabar.
Daraktan yada labarai na fadar Oodua, Otunba Moses Olafare, ne ya fitar da sanarwar nadin sarakunan, da kuma sunayen wadanda aka nada.

Source: Twitter
Sarkin Yarbawa ya nada sarakuna 20
Jaridar Leadership t rahoto jerin sababbin sarakunan da aka nada sun hada da Oba Adegoke Owojori, Obajio na Moore; Oba Olatunde Owole Erinle, Olu na Erinle; da Oba Kehinde Adeyinka Adetoro na Awoyaya.
Sauran sun hada da Oba Adegbaju Azeez, Olu na Ifeparapo; Oba Adedunni Gbadegesin, Olu na Onida; Oba Gbade Agboola, Olu na Irewole; da Oba Adebamiji Adeniyi Habedeen, Olu na Onimon.
An kuma nada Oba Abdul Wasiu Hassan, Olu na Alaseyori; Oba (Dr.) Gbadegesin Elubode, Olu na Obagibile; Oba Oladipo Olayinka Fasesin, Olu na Famia; da Oba Akinola John Adebayo Fadoyin, Olu na Kajola Obalara.
Haka zalika, akwai sauran sarakunan da aka nada kamar Oba Akeem Ogungbade, Olu na Elefon-Obagibile Olofin; Oba Awojobi Lateef Olawale, Loja na Oke-Owena; Oba Mayowa Awosope, Olu na Ayedire; da Oba Fatai Abass Adeyini, Olu na Aye-Arode.
Sauran sun hada da Oba Bolanle Azeez Odebola, Olu na Asarogun; Oba Olufemi Olajide Omidirepo, Olu-Oke na Oke-Ora Iranje; Oba Gbenga Adewole Ogunleye, Olu na Abeji; Oba Adegoke Olafare Arilewola, Olu na Idu Ladare; da Oba Afeez Iyiola Akinyele, Olu na Erinje.
Kiran sarki ga sababbin sarakuna
A jawabinsa, Ooni Adeyeye Ogunwusi ya jaddada cewa sarauta ba alamar jin dadin kai ba ce, illa alhakin hidima ga jama’a.
Ya bukace su kasance jagorori na zaman lafiya, su raya hadin kai tsakanin al'umma, tare da samar da ci gaba a yankunansu, inji rahoton PM News.
Shima Lowa Adimula na Ile-Ife, Oba Adeyeye Adekola Adesiyan, ya gargadi sababbin sarakunan da su yi mulki da hikima da tawali’u.

Source: Twitter
An yi wa sarakuna nasiha kan mulki
Oba Adeyeye Adekola ya shaidawa sababbin sarakunan cewa an yi masu wannan nadin domin hidimtawa al'umma ba wai don takarar mulki ba.
A nasa bangaren, Obalufe na Ile-Ife, Oba Idowu Olaniyi Adediwura, ya bukaci sababbin sarakunan da su ci gaba da kasancewa masu biyayya ga asali masarautar Ile-Ife.
Oba Idowu Olaniyi Adediwura ya fadawa sarakunan bukatar da ke da akwai ta bayar da gudummawa ga ci gaban al’adu da tattalin arzikin al’ummominsu.
'Ba a Najeriya kadai ake wahala ba' - Ooni
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi ya yi kira ga 'yan Najeriya da su kara ba gwamnati lokaci kan halin da ake ciki.
Babban basaraken Yarbawan ya bayyana matsalar tsadar rayuwa da yunwar da ake fama da su a Najeriya a matsayin wani lamari da ya shafi duniya baki daya.
Bisa haka Basaraken ya bukaci ƴan Najeriya su bai wa gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ƙarin lokaci domin gyara matsalar hauhawar farashi.
Asali: Legit.ng


