NNPCL Ya Samu Ribar Naira Tiriliyan 1, amma Bai Tura ko Sisi a Asusun Tarayya ba
- Kamfanin NNPCL ya samu ₦1.06trn daga ribar PSC tsakanin Janairu zuwa Agusta, amma bai tura ko sisi ga asusun tarayya ba
- Duk da raba kaso zuwa kuɗin gudanarwa da binciken mai, NNPCL bai biya kudin rabo na ₦2.17trn na 2025 ga asusun FAAC ba tukuna
- Rahoton FAAC na Agusta 2025 ya nuna cewa ribar da NNPCL ya samu a cikin watanni takwas ba ta kai hasashen ₦1.57trn ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kamfanin NNPCL ya samu ribar Naira tiriliyan 1.06 daga sayar da fetur a yarjejeniyar PSC tsakanin Janairu zuwa Agusta 2025, a cewar sabon rahoton kwamitin asusun FAAC.
Sai dai, duk da wannan riba mai yawa, rahoton ya nuna cewa kamfanin bai tura ko sisi zuwa asusun tarayya ba a cikin watanni takwas na samun kudin.

Kara karanta wannan
Abin kunya: An kama masu karkatar da kudin tallafin 'taki' da ake rabawa talakawa a Katsina

Source: Twitter
Me ake nufi da ribar mai a yarjejeniyar PSC?
Wannan ya saba da tsammanin cewa kamfanin zai tura wa asusun FAAC akalla Naira tiriliyan 2.16 a matsayin kudin rabo a lokacin, inji rahoton The Cable.
PSC wata yarjejeniya ce tsakanin NNPCL, gwamnatin Najeriya, da kamfanonin mai, wacce take fayyace yadda za a raba albarkatun da aka hako.
A karkashin wannan tsarin, “ribar mai” na nufin abin da ya rage bayan cire kudaden gudanarwa da aikin hakar mai, sannan a raba shi tsakanin gwamnati da sauran bangarori.
Kididdigar ribar NNPCL a 2025
Rahoton FAAC na Agusta 2025 ya nuna cewa ribar da NNPCL ya samu ta gaza cimma hasashen ₦1.57trn.
A Janairu kamfanin ya samu ribar ₦105.91bn, a Fabrairu ya samu ribar ₦127.66bn, yayin da a Maris ya samu ribar ₦204.96bn.
A Afrilu ya samu ri ar ₦121.93bn, a Mayu ya samu ₦129.39bn, sannan Yuni ya fadi zuwa ₦22.77bn.

Kara karanta wannan
Rashin wuta: Bayan bayin Allah sun fara mutuwa, gwamnati ta kai sola asibitin Kano
Amma a watan Yulim ribar NNPCL ta tashi zuwa ₦84.48bn, sai kuma a Agusta da ya samu ribar da ta fi kowane lokaci yawa, da ₦263.12bn.
Rarraba kudaden NNPCL a 2025
Rahoton ya bayyana cewa NNPCL ya raba kudaden da ya samu zuwa manyan fannoni uku: kuɗin gudanarwa na kamfanin (30%), kuɗin binciken mai (30%), da kaso na asusun tarayya (40%).
Wannan ya haifar da rabon ₦318.05bn a matsayin kuɗin gudanarwa, ₦318.05bn ga bincike, da ₦424.07bn ga asusun tarayya.
Duk da haka, babu komai a layin da ya kamata ya nuna kudin da NNPCL ya tura wa asusun FAAC na tsawon wannan lokaci.

Source: Getty Images
NNPCL: Martanin cibiyar Agora Policy
A wani rubutu da cibiyar Agora Policy ta wallafa a shafinta na X, ta ce duk da wadannan kudaden, NNPCL ya cika 15% ne kawai na burin kudaden shiga da aka tsara ga tarayya, yayin da ya bayar da 67% na rabon tarayya daga ribar mai.
“NNPC bai biya ko sisi na kudin rabo ga FAAC a shekarar 2025 ba, wanda ya kamata a kalla ya kai ₦2.17trn a cikin watanni takwas,” inji cibiyar.

Kara karanta wannan
Shugaban kasa, gwamnoni da kananan hukumomi sun raba Naira tiriliyan 2.2 a wata 1
Cibiyar ta kara da cewa wannan kudin rabon shi ne ya maye gurbin kuɗaɗen shiga daga EO, wanda a baya shi ne mafi girman tushen kuɗi daga fannin mai.
FAAC ya raba N2.22trn a Agusta
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kwamitin FAAC ya raba Naira tiriliyan 2.225 ga gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi a watan Agusta 2025.
Wannan shi ne mafi girma da aka taɓa rabawa a tarihi, kuma karo na biyu a jere da FAAC ta raba kudin da suka haura wa Naira tiriliyan 2 a wata guda.
Jimillar kuɗin shiga da aka samu gaba ɗaya ya kai N3.635trn, amma an kashe N124.839bn wajen tara kuɗin, sannan an ware N1.285trn na tallafi, da ajiyar gwamnati.
Asali: Legit.ng