"Abin a Tausaya Mana ne," Manoma Suna Takaicin Karyewar Farashin Amfanin Gona a Najeriya
A lokacin da wasu daga cikin 'yan Najeriya ke farin ciki da faduwar farashin kayan abinci, manoma sun bayyana cewa wannan al'amari bai yi masu dadi ba.
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gamayyar kungiyoyin manoma na kasa reshen jihar Kano ta bayyana takaici a kan yadda gwamnatin tarayya ke taimaka wa wajen karya farashin abinci.
Shugaban gamayyar, Abdullahi Ali Mai Burodi ne ya bayyana takaicin manoman a tattauna wa da ya yi da Legit, a lokacin da ya ke amsa tambaya kan yadda su ke kallon umarnin Gwamnatin Tarayya.

Source: Getty Images
Channels TV ta ruwaito yadda Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin a karya farashin abinci domin sama wa jama'a saukin tsadar farashi da ake kuka a kai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manoma sun fadi illar karya farashin abinci
Shugaban AFAN reshen Kano, Ali Mai Burodi ya shaida cewa matakin karya farashin kayan abinci a Najeriya ba zai haifar wa manoma 'da mai ido ba.
Ya ce wannan mataki, zai shafi su kansu jama'ar kasa da ke farin ciki da raguwar farashin abinci, saboda manoma za su rage sha'awar noma.
A bayaninsa kan dalilin adawarsu da bada umarnin rage farashin abincin, Ali Mai Burodi ya ce:
"Amma dai abin da ya ke faru wa a yanzu, mu sayi taki har N70,000, yau a ce masara tana N20,000 da wani abu, waken suya N60,000 da wani abu, albasan ga ta nan ita ta fara zuwa."
"Albasa sai an cika maka buhu tsantsa, sannan a kara dora kusan wani rabin buhun a sama a dinke, a baka N8,000-N9,000. Ya Ilahi, ta ina mutum zai ji yana da sha'awar ci gaba da samar da abinci a nan gaba?"
"Wannan dalilin ya sa ko da wasu daga cikin 'yan uwanmu mano, suna cewa an karya masu gwiwa, to wannan kar ki dada kar ki rage, shi ke sa ba mu da tunanin ci gaba da samar da shi kansa abincin da yawa."
Kiran manoma ga gwamnatin Najeriya
Abdullahi Ali Mai Burodi ya bayyana cewa hanya daya da karya farashin abinci da zai yi wa kowa dadi a kasar nan shi ne gwamnati ta tabbata ta samar masu da kayayyakin noma.
Ya ce ta haka ne ko da an karya farashin, manoma ba za su yi asarar kudi mai yawa ba kamar yadda ake gani yana faru wa a halin yanzu.

Source: Facebook
A kalaman Shugaban AFAN:
"Nazari da mu ka yi a kan abin da ke faru wa a wannan shakarar na karyewar amfanin gona ta kowane bangare, karyewar kuma, ba karyewar da za a yi shiru ba ce, karyewa ce wacce ya kamata a fito ana kuka."
"Mu ba mu da haufi ko hilafa a kan mayukar idan gwamnati za ta shigo ta dawo da tallafi kamar yadda aka saba a baya a kan harkar noma. A taimaka wa manoma da kayayyaki, musamman irin su tantan da ake amfani da ita, irin wannan injin da ake yankan shinkafa da ita, wato 'combiner'"
"Duk irin wadannan abubuwan idan gwamnati za ta samar da su su wadata a hannun manoma, to mu ma ba za mu kashe kudi mai yawan da za mu damu idan amfanin gona ya karye ba."
Abdullahi Ali Mai Burodi ya bayyana cewa sukansu jama'ar gari da ke muryar karyewar farashin kayan abinci, su je su ci gaba.
Matsayar 'yan kasuwa kan karyewar farashin abinci
A yayin da ran manoma ya baci matuka, su 'yan kasuwa su ce abin da sauki, kamar yadda Kakakin kasuwar kayan abinci ta Singer a Kano, Bashir Madara ya shaida wa Legit.
Ya bayyana cewa dukkanin wani 'dan Najeriya da ke kishin talaka, kuma ya ga halin kunci da ake ciki na tsadar kaya zai yi marhabun da umarnin Shugaba Tinubu.
Bashir Madara ya ce amma wannan ba ya nufin 'yan kasuwa ba za su yi asara ba, duk da yana sa ran lamarin zai zo da sauki sosai.
A kalamansa:
"Shi dan kasuwa, a kowane lokaci da za a ce farashin kaya ya ragu, yana da wahala a ce ba a samu dan kasuwa da ya ke da kaya a kasa ba. Dole a samu asara daga hannun wasu 'yan kasuwa."

Kara karanta wannan
Kwana ya kare: Malamin da ya fi 'tsufa' yana wa'azi ya bar duniya yana shekaru 95
"Babu mamaki suna da mai tsohon farashi, ko wani abu makamancin haka. To amma abin da ya ke faru wa shi ne, mu kanmu 'yan kasuwa mun yi wayo kuma muna kallon yadda abubuwa su ke tafiya."
"Idan da mutum ya kan sayi kayan da su ka yi yawa, har ya ajiye ya ce a nan zai samu riba a nan gaba, to yanzu gaskiya abin da canza. Yanzu kusan kowa yana sayen kayan da zai iya sayar wa ne a cikin dan kankanin lokaci saboda yana sa ran kafin ya koma ya sayi wani ma, an kuma samu farashi ya ragu."
Bashir Madara ya shawarci gwamnati a kan ta rika duba 'yan kasuwa a duk lokacin da za ta sanar da irin wadannan mataki saboda kowa ya amfana yadda ake da bukata.
Tinubu ya bada umarnin karya farashin abinci
A baya, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin gaggawa ga Kwamitin Majalisar Zartarwa ta Kasa domin ɗaukar matakan rage farashin abinci a Najeriya.
Karamin Ministan Harkokin Noma, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, ya bayyana hakan bayan wani taro da aka gudanar a Birnin Tarayya, Abuja, inda ya ce sauki zai samu a kasa.
Shugaban ƙasa ya nuna damuwa sosai kan yadda tsaro da tsadar sufuri ke ƙara dagula matsalar kayan abinci, kuma ya ba da umarnin a dauki matakan magance matsalolin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



