Rai Bakon Duniya: An Yi Rashin Babban Malamin Musulunci a Adamawa

Rai Bakon Duniya: An Yi Rashin Babban Malamin Musulunci a Adamawa

  • Majiyoyi sun tabbatar da rasuwar wani malamin addinin Musulunci a Adamawa, Sheikh Modibbo Dahiru Aliyu Ganye
  • Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana bakin cikinsa kan rasuwar a cikin wata sanarwa, inda ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin
  • Pantami ya yi addu’ar neman rahamar Allah ga Sheikh Ganye, yana yi masa fatan shiga Aljanna tare da sauran malamai da iyaye

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Yola, Adamawa - Majiyoyinmu sun tabbatar da mana da rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Adamawa.

An tabbatar da cewa marigayi Sheikh Modibbo Dahiru Aliyu Ganye ya rasu a ranar Talata da ta wuce 16 ga watan Satumbar 2025 a garin Ganye.

Pantami ya jajanta da malamin Musuluci ya rasu
Sheikh Isa Ali Pantami da Malam Modibbo Dahiru Ganye. Hoto: Prof. Isa Ali Pantami.
Source: Youtube

Pantami ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin

Sheikh Isa Ali Pantami ya yi jimamin rasuwar margayin a yau Asabar 20 ga watan Satumbar 2025 a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Masarautar Kano ta yi babban rashi, Sarkin Gabas ya rasu bayan hatsarin mota

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesa Pantami ya nuna kaduwarsa bisa rashin da aka yi inda ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin.

Malamin ya kuma yi masa addu'a ta musamman da fatan samun rahama ga marigayin da sauran wadanda suka riga mu gidan gaskiya.

A cikin rubutun, Farfesa Pantami ya ce:

"Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Raaji'un!.
"Muna mika ta'aziyyar rasuwar daya daga cikin iyayenmu, Shaykh Modibbo Dahiru Aliyu Ganye.
"Muna rokon Allah ya yafe masa kura-kurensa, ya sanya Aljannah ce makomarsa tare da sauran iyayenmu da malamanmu da zuriyarmu."

Yadda aka gudanar da sallar jana'izar marigayin

Daya daga cikin hadiman shugaban karamar hukumar Ganye, Farouq Mohammed Ganye ya ce tuni aka binne marigayin bisa tsarin Musulunci.

An tabbatar da cewa an yi sallar marigayin a ranar Alhamis 18 ga watan Satumbar 2025 da misalin karfe 10 na safe a garin Ganye da ke jihar Adamawa.

Isa Tafida ya wallafa a Facebook cewa an yi addu’o’i ga marigayin yayin da manyan malamai, dattawa da sauran al’umma suka halarta.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Malamin da ya fi 'tsufa' yana wa'azi ya bar duniya yana shekaru 95

Ya ce mutane da dama sun yi jimamin mutuwar marigayin duba da gudunmawar da ya ba addini kafin barinsa duniya.

Abin da mutane ke fada game da marigayin

Daga bisani, Tafida ya yada hotunan daruruwan al'umma da suka halarci jana'izar marigayin cikin alhini da fatan rahama ga mamacin.

Mutane da dama sun yi alhinin mutuwar marigayin inda suka yi masa fatan samun rahama a gobe kiyama duba da hidima ga addini da ya yi.

Malamin Musulunci a Kano ya kwanta dama

A baya, kun ji cewa jihar Kano ta yi rashin malamin Musulunci, Sheikh Manzo Arzai, a ranar Lahadi 31 ga Agusta, 2025 da ta gabata.

Imam Muhammad Nur Muhammad Arzai ya sanar da lokacin jana’izar, inda ya ce mutane da dama sun samu halartar jana'izar marigayin da aka yi a Kano.

An gudanar da jana’izar a Zawiyar Sheikh Manzo Arzai da ke Unguwar Arzai a Kano, inda aka yi addu’ar Allah ya gafarta masa ya kuma saka masa da gidan aljanna.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.