Hotunan Manya a Najeriya da Suka Halarci Bikin Karrama Rarara da Digirin Dakta
- An gudanar da bikin karrama mawaki Dauda Kahutu Rarara a Abuja, inda jami’ar European American ta ba shi lambar yabo
- Taron ya samu halartar manyan mutane ciki har da gwamnoni, ministoci da kuma amaryar Rarara, jarumar Kannywood Aisha Humairah
- Gwamna Dikko Radda, tsohon Sanata Sa’idu Alkali da NasIr Bala Ja’oji sun halarci taron don nuna goyon bayan mawakin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - A yau Asabar 20 ga watan Satumbar 2025 aka gudanar da bikin karrama mawaki Dauda Kahutu Rarara a Abuja.
Wata jami'a da aka ce sunanta European American University ce ta karama mawakin siyasan wanda yake kan ganiyarsa a yanzu.

Source: Facebook
An karrama Rarara da digirin girmamawa
Rahoton DCL Hausa ya tabbatar da haka inda ya wallafa hotunan taron da aka gudanar a yau Asabar a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron ya samu halartar manyan mutane daga Najeriya musamman masu mukamai a gwamnatin Bola Tinubu.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai amaryarsa da ya aura kwanakin baya kuma jaruma a Kannywood, Aisha Humairah.
Manyan Najeriya da suka halarci bikin a Abuja
Har ila yau, Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina da mawakin ya fito shi ma ya halarci bikin domin shaida karrama dan jihar.
Sauran sun hada tsohon Sanatan Gombe da Arewa kuma Ministan sufuri a Najeriya, Sanata Sa'idu Ahmed Alkali.
Sai kuma Nasir Bala Aminu Ja'oji daga jihar Kano wanda Bola Tinubu ya ba mukamin hadiminsa na musamman a kwanakin nan.

Source: Facebook
Abin da mutane ke cewa kan karrama Rarara
Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu game da wanna karramawa da aka yi wa mawaki Dauda Kahutu Rarara.
Wasu daga ciki sun yi masa fatan alheri yayin da mafi yawa ke yin shagube game da karramawar inda ake yi masa gorin karatun boko.
Sadeeq Dawud:
"Mutumin da bai je ko firamare da sakandare ba amma yanzu yana da digiri."
Haruna Kalos:
"Harkar ilimi ta lalace dai a wannan kasar ta mu, Allah ya ba mu mafita wai sai jahilai su za ku karrama."
Abubakar Sadiq:
"Bayan cin mutunci da jami'ar American University ta yi wa boko shi ko Dikko gani yake Rarara ne zai maida shi kujeran gwamna karo na biyu"
Abdulrashid S Pawa:
"Rarara mai 'capacity', digiri ruwan dare leka gidan kowa."
Sumayya Husain:
"Da Hausa kenan akayi jawabin ko."
Muhammed Surajo Ibrahim:
"Masha Allah, ubangiji ya sanya alheri."
Salisu Yunusa Tfoki:
"Gwara na Dauda a kan na su Kwankwaso da sauran wasu yan siyasar."
An soki Rarara bayan mutuwar Buhari
A baya, kun ji cewa mawaƙin siyasa, Dauda Abdullahi Kahutu Rarara ya fuskanci suka daga masoyan Muhammadu Buhari saboda rashin yin ta’aziyyar rasuwa.
Duk da Rarara ya saki bidiyo inda ya ce “Allah ya jiƙan maza”, amma bai kira sunan Buhari kai tsaye ba, abin da ya janyo cece-kuce.

Kara karanta wannan
An yi rashi: Bayan rasuwar tsohon sufeta janar na yan sanda, an sanya ranar jana'izarsa
Masu amfani da kafafen sada zumunta sun bayyana rashin jin daɗi, inda wasu ke kallon saƙon Rarara a matsayin rashin girmamawa ga Buhari.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

