Shugaba Tinubu Zai Hadu da Jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso, An Samu Bayani
- Shugaba Bola Tinubu, Atiku Abubakar da Rabiu Musa Kwankwaso za su hadu a bikin nadin sabon Sarkin Ibadan, jihar Oyo
- An shirya bikin nadin Oba Rasidi Ladoja a matsayin Olubadan na 44 ranar Juma'a, 26 ga watan Satumba, 2025 a birnin Ibadan
- Kwamitin shirya bikin nadin ya tabbatar da cewa manyan jiga-jigan da aka gayyata sun amsa cewa za su halarci taron
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ibadan, jihar Oyo - Shirye-shiryen nada sabon Sarkin Ibadan watau Olubadan na Ibadanland, Oba Rasidi Ladoja ya yi nisa jihar Oyo.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da jagoran NNPP na kasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso na cikin manyan jiga-jigan da ake sa ran za su halarci bikin nadin basaraken.

Source: Facebook
The Nation ta ruwaito cewa jagoran adawar Najeriya kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar na cikin wadanda ake sa ran za su halarci taron.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Tinubu zai hadu jiga-jigai a Ibadan
Tinubu da Ladoja sun yi aiki tare a Majalisar Dattawa a lokacin da aka rushe Jamhuriya ta Uku.
Bayan haka kuma, a lokacin da Tinubu ke wa’adi na biyu a matsayin Gwamnan Legas, Ladoja na rike da mulki a matsayin Gwamnan Jihar Oyo.
Za a nada Ladoja a matsayin Olubadan na 44 na Ibadanland a ranar Juma’a mai zuwa, 26 ga watan Satumba, 2025 a dakin taron Mapo Hall da ke Ibadan.
A baya-bayan nan, Oba Ladoja ya bayyana cewa Shugaba Tinubu da sauran manyan baƙi sun tabbatar masa da cewa za su halarci bikin nadinsa.
Kwamitin nadin Olubadan sun fara gayyata
Bugu da Kari, Shugaban Kwamitin Shirya Bikin Nadin Olubadan na 44, Cif Bayo Oyero, ya tabbatar da cewa Shugaba Tinubu da sauran manyan baƙi za su halarta.
Ya fadi haka ne yayin da yake magana da ’yan jarida a taron manema labarai da aka gudanar a fadar Olubadan da ke Oke-Aremo, Ibadan,
Cif Oyero ya bayyana nadin da za a yiwa Ladoja a matsayin wanda zai shiga tarihi, yana mai cewa nadin ba kawai biki ba ne, zai kara tabbatar da tasirin masarautar Ibadanland.

Source: Facebook
Shugaban kwamitin ya ce:
“Hawan Oba Ladoja karagar sarauta tafiya ce da aka fara shekaru da dama da suka gabata, hanya ce da aka bi bisa tsari tare da hikimar.”
Ya jaddada cewa kasancewar Ladoja tsohon Sanata, Gwamna, kuma yanzu sarki, zai taimaka wajen kusantar da harkokin mulki ga jama'a.
MURIC ta nemi a dage nadin Olubadan
A wani labarin, kun ji cewa Kungiyar Kare Hakkokin Musulmi ta Kasa (MURIC) ta yi kira da a dage bikin miƙa sandar sarauta ga sabon Sarkin Ibadan da aka shirya a ranar Juma'a.
Gwamnatin Oyo da masarautar Ibadan sun shirya gudanar da bikin ne a ranar 26 ga watan Satumbaar 2025 da muke ciki bayan mutuwar marigayi tsohon Sarki.
Sai dai kungiyar MURIC ta yi Allah wadai da sanya ranar Juma'a wanda ya yi daidai da lokacin da Musulmai ke gudanar ibada da addu'o'insu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

