Bayan Rasuwarta, Shugaba Tinubu Ya Tuna ’Ya’yan Marigayiya, Ya ba Su Aiki a Abuja
- Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin bai wa ’ya’yan marigayiya tsohuwar shugabar ma'aikata a Abuja aiki
- Tinubu ya dauki wannan matakin ne domin tallafawa rayuwar iyalan marigayiyar, Grace Adayilo da ta rasu a Abuja
- Minista Nyesom Wike ya bayyana Adayilo a matsayin mai gaskiya, jajirtacciya, mai tawali’u da biyayya ga aikinta
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana kokarin Bola Tinubu bayan rasuwar tsohuwar shugabar ma'aikata a Abuja.
Wike ya ce Bola Tinubu ya bayar da umarnin daukar ’ya’yan marigayiya Grace Adayilo aiki nan take a birnin tarayya Abuja.

Source: Facebook
Sanarwar ta fito ne daga cocin 'National Christian Centre' yayin jana’izar Adayilo, wacce ta rasu a ranar 1 ga Satumba, 2025, cewar rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaushe marigayiya Grace ta rasu?
Marigayiyar kafin rasuwarta, ita ce mace kuma 'yar asalin babban birnin tarayya da Shugaba Bola Tinubu ya nada shugabar ma'aikatan hukumar FCTA.
Wata majiya daga hukumar raya babban birnin tarayya (FCTA), ta ce Grace Adayilo ta rasu ne a safiyar Litinin, 1 ga Satumba, 2025.
A ranar Alhamis din makon jiya ne aka yi wa Grace Adayilo ganin karshe, lokacin da ta wakilci Nyesom Wike a wani taron 'yan G7.
Taimakon da Tinubu ya yi wa iyalan marigayiyar
Wike ya ce matakin ya zama dole domin tallafawa iyalanta bayan rasuwarta a matsayin mai kula da su, tare da yabawa marigayiyar.
Ya ce:
"Dukkanmu mun sani wata rana za mu mutu, wannan tabbas babu kwana-kwana amma wasu daga cikin mutuwa da ake yi idan suka faru, dole za a ji zafi sosai."
Wike ya ce mutuwarta ta fi ciwo saboda ba ta nuna wata alama ba; an gan ta a aiki yau, gobe kuma labarin mutuwa ya iso.

Source: Facebook
Wike ya fadi gudunmawar marigayiyar a Abuja
Wike ya bayyana yadda ya fara haduwa da ita bayan nadin babban sakatare, matsayin da Tinubu ya kirkiro domin inganta harkokin aikin gwamnati.
"Na ce ina son mutum wanda ya ke da jajircewa da mutunta aiki, mutum mai kan-kan da kai da kuma wanda zai yi biyayyar aiki.
"Shugaban kasa ya umarce ni da na ba 'ya'yan marigayiyar guda hudu aiki nan take saboda Tinubu ya fahimci cewa a yanzu babu mai rike iyalinta."
- Nyesom Wike
Ya kara cewa Adayilo ba ta yi wasa da albashi ko hakkokin ma’aikata ba, tana kammala ayyuka cikin gaggawa, kuma uwa nagari ce ga kowa.
Ministan ya kuma bayyana cewa Adayilo tana da kwarewa a siyasa da iya hada kan jama’arta fiye da yadda aka sani.
Tinubu ya kaddamar da aiki a masallaci
Mun ba ku labarin cewa yayin ziyara a jihar Kaduna, Bola Tinubu ya kaddamar da wasu ayyuka a masallacin Sultan Bello da ke jihar Kaduna.
An gina sabon wurin alwala mai cin mutane 300 da bandaki 50 na zamani a babban masallacin da ke jihar.
Tinubu ya kaddamar da wadannan ayyuka na zamani wanda kamfanin Tantita ya yi a masallacin inda ya yaba da wannan aiki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

