Yan Bindiga Sun Farmaki Malamin Addini, Sun Bindige Shi bayan Garkuwa da Wasu
- ‘Yan bindiga sun kuma kai wani farmaki a jihar Enugu da ke Kudancin Najeriya inda suka hallaka malamin addini
- Maharan sun kashe Fasto Mathew Eya na cocin Katolika St. Charles, Eha-Ndiagu a karamar hukumar Nsukka
- Wasu rahotanni sun nuna cewa ba garkuwa da shi aka nufi ba, an kai harin ne musamman don hallaka shi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Nsukka, Enugu - Wasu yan bindiga sun tare babbar hanya inda suka farmaki tawagar malamin addinin Kirista a jihar Enugu.
Maharan sun bindige Fasto Mathew Eya ba tare da bata lokaci ba bayan tare motar da ya ke a karamar hukumar Nsukka da ke jihar.

Source: Facebook
Rahoton The Guardian ya tabbatar da cewa an kashe marigayi Mathew Eya wanda shi ne limamin cocin St. Charles Katolika, Eha-Ndiagu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi rashin babban Fasto a Nsukka
Kisan wannan malami na zuwa kwanaki kadan bayan mutuwar wani dattijon malamin addini a garin Nsukka da ke jihar.
Al'ummar yankin sun kadu da aka sanar da rasuwar babban Faston wanda ya bar duniya yana da shekaru 89 a duniya.
Babban Fasto na Nsukka, Rabaran Francis Okobo, ya rasu bayan fama da jinya a asibitin 'Niger Foundation, Enugu' da ke jihar.
An haifi Okobo ranar 4 ga Nuwamba, 1936, an nada shi limami a 1966 yayin da kuma ya zama babban Fasto na Nsukka a 1990.
'Yan bindiga sun hallaka Fasto a Enugu
Kisan wannan Fasto da aka yi ya jefa shakku kan tsaron yankin musamman bayan hare-hare a kwanakin nan.
An ruwaito cewa yan bindiga sun kai hari kan Fasto Eya a hanyar Eha-Ndiagu, kuma ya mutu nan take, yayin da aka yi garkuwa da wasu fasinjoji.
Wasu majiyoyi suna zargin musamman aka kawo harin domin kashe shi ba wai nufin garkuwa da shi ba ne.

Kara karanta wannan
Kwana ya kare: Malamin da ya fi 'tsufa' yana wa'azi ya bar duniya yana shekaru 95

Source: Original
Abin da ake zargi game da kisan Faston
Sai dai wasu majiyoyi sun nuna cewa kisan na iya zama kisan kai ne kai tsaye ba garkuwa ba, shaidu sun ce an tare shi kusa da inda ake aikin gina asibiti.
"Sun lalata tayoyin motar wanda ya tilasta wa motar tsayawa don dole, nan take suka bindige Faston a wurin ba tare da bata lokaci ba."
- Wata majiya ta tabbatar
Marigayi ya fito daga Ugbaike a Enugu Ezike, karamar hukumar Igbo-Eze ta Arewa da ke jihar a Kudancin Najeriya, cewar rahoton Daily Post.
Rundunar ‘yan sanda da Katolikan Nsukka ba ta fitar da sanarwa ba tukuna, yayin da jama’a ke kira da a dauki matakin kawo karshen tashin hankali.
'Yan bindiga sun sace Fasto a Ondo
A baya, mun ba ku labarin cewa yan bindiga sun kutsa har cikin gida, sun yi awon gaba da wani Fasto da ke aiki a asibitin FMC na gwamnatin tarayya a jihar Ondo.
Kungiyar AMLSN ta yi Allah wadai da lamarin, tare da kira ga gwamnatin Ondo da hukumomin tsaro su gaggauta ceto wanda aka sace.
Rundunar yan sanda ta tura jami'anta zuwa cikin daji domin ceto wanda aka sace Fasto Ayodeji Akesinro cikin koshin lafiya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

