'Yan Bindiga Sun Kutsa cikin Gida, Sun Sace Malamin Addini kuma Ma'aikacin Asibiti
- Yan bindiga sun kutsa har cikin gida, sun yi awon gaba da wani fasto da ke aiki a asibitin FMC na gwamnatin tarayya a jihar Ondo
- Kungiyar AMLSN ta yi Allah wadai da lamarin, tare da kira ga gwamnatin Ondo da hukumomin tsaro su gaggauta ceto wanda aka sace
- Rundunar yan sanda ta tura jami'anta zuwa cikin daji domin ceto wanda aka sace Fasto Ayodeji Akesinro cikin koshin lafiya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ondo - Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace Fasto Ayodeji Akesinro, wanda ma’aikaci ne a cibiyar lafiya ta tarayya (FMC) da ke Owo, Jihar Ondo.
Rahotanni sun nuna cewa an yi garkuwa da malamin addinin kirista ne daga gidansa da ke Upenme a karamar hukumar Owo da misalin ƙarfe 7:00 na yammacin Alhamis.

Source: Original
Kungiyar ma'aikatan dakin gwaje-gwajen lafiya ta Najeirya (AMLSN), reshen Jihar Ondo, ta tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda Leadership ta kawo.
An bukaci dakarun tsaro su ceto Fasto
A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, MLS Akinlolu Ayodeji, tare da sakatarenta, MLS Adeola-Oyekan Joshua, suka fitar, AMLSN ta ce wannan lamarin abin takaici ne ƙwarai.
“Muna yaba wa ƙoƙarin gwamnatin Jihar Ondo a baya, musamman wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar a irin waɗannan lokuta.
"Saboda haka, muna kira ga gwamnatin ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamna Lucky Aiyedatiwa, ta tashi tsaye domin ganin cewa an saki abokin aikinmu ba tare da wani sharadi ba,” in ji sanarwar.
Kungiyar AMLSN ta aika sako ga jami'an tsaro
Kungiyar ta kuma shawarci mambobinta da jama’a su kwantar da hankulansu, yayin da ta yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta ɗaukar mataki domin ceto Fasto Akesinro.
Haka nan kuma AMLSN ta bukaci jami'an tsaro su kamo duk mai hannu a lamarin tare da gurfanar da su a gaban shari’a domin su girbi abin da suka shuka, rahoton Tribune.

Source: Facebook
Wane mataki yan sanda suka dauka?
Kwamishinan ’yan sanda na jihar Ondo, CP Adebowale Lawal, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa jami’an tsaro sun shiga dazuka suna aikin bincike domin ceto wanda aka sace.
Ya tabbatar da cewa ’yan sanda tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro za su tabbatar da cewa an kubutar da Fasto Akesinro cikin koshin lafiya.
“Mutanenmu sun shiga daji tare da sauran jami’an tsaro domin ceto wanda aka sace. Ina tabbatar muku cewa ba za mu huta ba wajen ganin an tabbatar da tsaron jama’ar jihar Ondo,” in ji CP Lawal.
'Yan sanda sun kashe masu garkuwa a Kebbi
A wani labarin, kun ji cewa dakarun 'yan sanda sun yi nasarar murkushe wasu yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a jihar Kebbi.
Jami'an 'yan sandan sun kashe masu garkuwa da mutanen ne a karamar hukumar Shanga da safiyar ranar Lahadi bayan gwabza fada tsakaninsu.
Rundunar yan sanda ta gode wa mazauna yankin saboda yadda suke gaggauta ba da bayanan sirri, yana mai jaddada cewa irin wannan haɗin kai shi ne ginshikin hana aikata laifuffuka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

