Zuwan Tinubu Ya Yi Amfani, An Kaddamar da Ayyukan da Za Su Taimaki Musulmi a Sultan Bello
- An gina sabon wurin alwala mai cin mutane 300 da bandaki 50 na zamani a masallacin Sultan Bello da ke Kaduna
- Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tknubu ya kaddamar da wadannan ayyuka na zamani wanda kamfanin Tantita ya yi a masallacin
- Tinubu ya yaba da wannan aiki a lokacin da ya halarci daura auren dan tsohon gwamnan Zamfara, Sanata Abdul'aziz Yari
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu ya kaddamar da sababbin ayyuka na zamani a masallaci mai dumbin tarihi watau Sultan Bello da ke Kaduna.
Kamfanin tsaro na Tantita Security Services Nigeria Limited (TSSNL) ne ya dauki nauyi kuma ya samar da sababbin kayayyakin da za su taimaki musulmai a Sultan Bello.

Source: Twitter
Wane ayyuka Tinubu ya kaddamar a Sultan Bello?
Leadership ta ce ayyukan da Tinubu ya kaddamar sun haɗa da wurin alwala na zamani, bandaki 50 da ke da sashen manyan mutane (VIP), da kuma tankin ruwa na sama mai ɗaukar lita 300,000.
Wannan ayyuka dai za su taimaka wa masu ibada da masallaci da ma mutanen da ke rayuwa a Unguwar Sarki a Kaduna.
Tinubu, wanda ya kai ziyara Kaduna domin halartar ɗaurin auren ɗan tsohon gwamnan Zamfara, Sanata Abdul’Aziz Yari, ya yaba da wadannan ayyuka da kamfanin ya yi.
Ya bayyana su a matsayin shaida ta haɗin kai da kuma kokarin da kamfanoni ke yi wajen taimaka wa al’umma a sassa daban-daban na Najeriya.
Yadda masallacin ke fama da matsala a baya
Kafin wannan gagarumin aiki, masallacin na dogaro da ƙaramin wurin alwala wanda ya yi wa masu ibada kadan, musamman a lokutan sallar Juma’a.
Sabon wurin alwala na yanzu na daukar mutum 300 lokaci guda, yayin da tankin ruwan zai iya samar da ruwa ga masallacin da ma al’ummar unguwar.
Injiniyan da ya jagoranci aikin, Abba Mubashir, ya bayyana cewa an gina wurin alwalar da bandaki bisa ƙa’ida kuma an yi mai inganci.
“Tun daga tushe har zuwa kammalawa, komai an yi mai kwari. Wurin alwala ya wadatu, sannan tankin lita 300,000 zai samar da ruwa ga masallacin da al’umma,” in ji shi.

Source: Twitter
An bayyana yadda aka gina sabon wurin alwalan
Babban Ladan na Masallacin Sultan Bello, Malam Abdurrahman Abdulhamid, ya yi godiya ga kamfanin bisa farfaɗo da aikin da aka bari.
“Alhamdulillah, wannan aiki asali Jack Rich ne ya fara shi, amma aka bar shi sama da shekaru uku zuwa huɗu. Yanzu kamfanin Tantita ya shiga ya karasa.
"Yanzu mutum 300 na iya yin alwala lokaci guda, akwai bandaki 50 ciki har da VIP, sannan tankin ruwan lita 300,000 zai ba masallaci da al’umma ruwa,” in ji shi.
Ya yi addu’a Allah ya saka wa Tantita da alheri, tare da kira ga kamfanin da ya ci gaba da irin waɗannan ayyukan da suka shafi ci gaban al’umma.
Bola Tinubu ya ziyarci iyalan Buhari
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci iyalan marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a Kaduna.
Da yake jawabi a gidan Buhari, Shugaba Tinubu ya ce marigayin ya rasu amma ya bar masu halaye na kirki da za su ci gaba da koyi da su.
Shugaba Tinubu ya hadu dan marigayin, Yusuf Buhari, da Hajiya Aisha Buhari a wannan ziyara da ya kai masu a Kaduna ranar Juma'a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


