'Yan Fashi da Makami Sun Kutsa Banki, Sun Wawure Makudan Kudin Jama'a
- Rahotanni na nuni da cewa 'yan fashi da makami sun kai hari bankin Polaris na reshen Awka da ke jihar Anambra
- An ruwaito cewa ‘yan fashin sun kutsa dakin ajiya tare da sace wasu kudi da ba a bayyana adadinsu ba
- Jami’an ‘yan sanda da hukumomin bankin sun fara bincike domin gano yadda lamarin ya faru da kamo barayin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Anambra – An kai mummunan hari a bankin Polaris da ke unguwar Amenyi, cikin birnin Awka na jihar Anambra, wanda ya jawo tashin hankali ga ma’aikata da kwastomomi.
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan fashin sun kutsa cikin bankin da dare, inda suka karya dakin ajiyar kudi tare da wawure wasu makudan kudi da ba a bayyana adadinsu ba.

Source: Original
Legit ta tattaro bayanai kan harin da aka kai bankin ne a cikin wani sako da Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X.
Lamarin ya jefa ma’aikatan bankin da al’ummar da ke amfani da shi cikin damuwa, yayin da hukumomin tsaro da bankin suka fara bincike domin gano yadda aka gudanar da fashin.
Yadda aka gano an kai hari a banki
Shugabar reshen bankin, Okpara Ugoo Chiaka da ke zaune a titin Nnosike Akabugo ce ta gano lamarin da safe lokacin da ta iso wajen aiki.
Rahotanni sun nuna cewa da misalin karfe 7:30 na safe ta isa wajen ta tarar an karya kofa da ofisoshi ciki har da babban dakin ajiyar kudi.
Bayan shiga cikin bankin, ta lura cewa an riga an yi barna a wuraren gudanar da ayyuka, sannan an lalata abubuwa da dama kafin a wawure kudin.
Wannan ya sa bankin ya sanar da hukumomin tsaro cikin gaggawa domin fara kokarin cafke mutanen da suka kai harin.

Source: Getty Images
Halin da ake ciki a bankin bayan hari
Wata majiya daga cikin ma’aikatan ya bayyana cewa kwastomomi sun shiga cikin rudani bayan jin labarin fashin.
Duk da haka, an tabbatar musu cewa bankin na daukar matakai domin tabbatar da tsaro da kuma cigaba da aiki cikin yanayi na kwanciyar hankali.
Hukumomi sun fara binciken fashin bankin
Bankin ya bayyana cewa an riga an sanar da rundunar ‘yan sanda game da lamarin, inda jami’an tsaro suka fara gudanar da bincike domin gano wadanda ke da hannu.
An kuma ce bankin ya kaddamar da bincike domin tantance irin rashin tsaro da ya ba wa barayin damar kai hari.
An tabbatar cewa jami’an tsaro za su yi amfani da dukkan hanyoyin bincike domin gano wadanda suka aikata fashin.
Sojoji sun kama kayan 'yan ta'adda
A wani rahoton, kun ji cewa dakarun rundunar sojojin Najeriya sun kama wasu motoci dauke da kayan da ake zargi na 'yan ta'adda ne a Yobe.
Rahotanni sun bayyana cewa an kama motoci tirela biyu da wasu kananan motoci kirar Sharon cike da kayayyaki.
Bayanin da sojojin suka fitar ya nuna cewa an kama masu tuka motocin da mataimakansu domin gudanar da cikakken bincike.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


