Tinubu, 'Yan Siyasa, Malaman Izala da Darika Sun Cika Kaduna Auren Dan Sanata Yari
- An gudanar da auren ɗan Sanata Abdulaziz Yari, Nasirudeen, da amaryarsa Safiya Shehu Idris a Kaduna cikin taron manyan baki
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da gwamnoni da dama sun halarci bikin, tare da wasu 'ya siyasa da jagororin jam’iyyu
- Bayan bikin, Tinubu ya kai ziyara gidan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya gana da Aisha Buhari da iyalansa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - An gudanar da auren ɗan Sanata Abdulaziz Yari, Nasirudeen Abdulaziz Yari Abubakar da amaryarsa Safiya Shehu Idris a Masallacin Sultan Bello, Kaduna.
Auren ya tara manyan baki daga fadin Najeriya ciki har da shugaban kasa, gwamnoni, ministoci, ’yan majalisa da fitattun shugabannin addini.

Source: Facebook
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a X cewa sun ziyarci gidan marigayi Muhammdu Buhari bayan daura auren.

Kara karanta wannan
'Za mu dora daga inda ya tsaya,' Anji abin da Tinubu ya fadawa iyalan Buhari a Kaduna
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bikin daurin auren ya kasance wani babban dandali na haduwar ’yan siyasa daga jam’iyyu da larduna daban-daban.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya jagoranci tawagar gwamnati daga Abuja zuwa Kaduna domin halartar bikin tare da wasu manyan jami’an gwamnati da shugabanni.
Manyan Najeriya sun cika garin Kaduna
Shugaban matasan APC, Dayo Israel, ya wallafa sunayen wasu daga cikin mutanen da suka raka shugaban kasa daga Abuja zuwa Kaduna a shafinsa na X.
Ciki har da Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na Kwara, Umar Bago na Neja, da Gwamna Uba Sani na Kaduna.
Haka kuma, Sanatoci kamar Barau Jibrin, Sani Musa, da Opeyemi Bamidele sun halarci bikin tare da ministoci kamar Wale Edun da Atiku Bagudu.
Hakazalika, shugaban jam’iyyar APC na ƙasa da tsohon shugaban jam’iyyar duk sun samu halartar bikin.
Karin wasu manyan da suka je Kaduna
Bikin ya kuma jawo manyan ’yan siyasa daga jam’iyyun daban-daban ciki har da 'yan adawa da masu rike da madafun iko.
Tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya kasance cikin mahalarta, tare da Gwamna Dikko Radda na Katsina, Gwamna Mai Mala Buni na Yobe, da Gwamna Douye Diri na Bayelsa.
Douye Diri ya wallafa a X cewa taron ya nuna yadda za a iya haɗa kai duk da bambancin al’adu a Najeriya.

Source: Twitter
Malaman Izala da darika sun hallara
A fannin addini kuwa, manyan malamai daga kungiyar Izala da Darika da ma wadanda ba su kungiyar sun halarci bikin.
Sheikh Abdullahi Bala Lau, Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe, Sheikh Yusuf Sambo Rigacikun, Sheikh Nasiru Abdulmuhyi da Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi duk sun je.
Shafin Jibwis na Facebook ya wallafa cewa wasu daga cikin malamai sun jagoranci walimar aure kafin a daura shi.

Source: Facebook
Tinubu ya je gidan Buhari a Kaduna
Bayan kammala auren, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyara gidan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A gidan, shugaban kasar ya gana da Aisha Buhari da ’ya’yanta ciki har da Yusuf Buhari kuma manyan 'yan siyasa ne suka raka shi gidan.
An daura auren 'dan Kwankwaso
A wani rahoton, kun ji cewa yayin da aka hadu a Kaduna auren dan Abdulaziz Yari, an daura auren dan Kwankwaso a Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ne ya zama wakilin Mustapha Rabiu Kwankwaso.
Shugaban hukumar Hisba ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa na cikin malaman addini da suka halarci daurin auren.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

