Mutane 2 Sun Kamu da Cutar Ebola a Birnin Tarayya Abuja? NCDC Ta Yi Karin Haske
- Hukumar NCDC ta tabbatar da ba a samu cutar Ebola ko Marburg a jikin mutane biyu da ake zargin sun kamu da cututtukan ba a Abuja
- Dr Jide Idris, shugaban NCDC ya ce yanzu haka an yi wa mutanen gwaje-gwaje kan zazzabin Lassa don gano abin da ke damunsu
- NCDC ta gargadi jihohi da su ƙarfafa sa ido, su shirya cibiyoyin killace mutane yayin da aka sake samun bullar Ebola a wasu kasashe
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar NCDC ta tabbatar da cewa mutane biyu da aka yi wa gwaji kan zargin sun kamu da Ebola ko Marburg a Abuja, ba su kamu da cutar ba.
Hukumar ta fitar da sanarwar a ranar Juma’a, inda ta ce an gudanar da gwaje-gwaje na farko kan mutanen, kuma sakamakon bai nuna Ebola ba.

Source: Twitter
Shugaban NCDC, Dr Jide Idris, ya ce an fara gwajin wasu cututtuka masu haɗari kamar zazzabin Lassa da kuma zazzabin Dengue, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alamomi da yadda ake daukar Ebola
Hukumar ta ce matakin ya zama wajibi saboda mutane sun shiga firgici sakamakon rade-radin da ke yawo game da rahotannin bullar cututtukan a Abuja.
Ebola cuta ce mai tsanani wacce take haddasa zubar jini a jiki, kuma kashi 25 zuwa 90 cikin 100 na wadanda suka kamu da ita na mutuwa.
Mutane na ɗaukar cutar ne ta hulɗa da jinin dabbobin da suka kamu ko kuma ta ruwan jikin mutane masu cutar, inji rahoton WHO.
An ce mutanen da suka kamu da cutar kan fara nuna alamomi kamar zazzabi mai zafi, ciwon tsoka, ciwon kai, da rauni, kafin ta rikide zuwa matsanancinya.
Idan ba a gano ta tare da yin maganinta da wuri ba, tana iya jefa mutum cikin tsananin rashin lafiya da zubar da jini, har ma ta kai ga kisa cikin karamin lokaci.

Kara karanta wannan
Hatsarin Jirgi ya rutsa da mutanen da suka gudo daga harin yan bindiga, an rasa rayuka
Yadda aka samu jita-jitar bullar Ebola a Abuja
Dr Jide Idris, ya ce:
"Hukumar NCDC na son sanar da mutane cewa mutane biyu da aka yi wa gwaje-gwaje saboda sun nuna alamomin Ebola da Marburg, a Abuja, ba sa dauke da wadannan cututtuka.
"Yanzu haka dai muna yi masu gwaje gwaje kan wasu cututtukan da ke da irin wannan alama kamar zazzabin Lassa da kuma zazzabin Dengue."
An rahoto cewa, wani mutumi ne da ya iso kasar daga Kigali, ya kai kansa wani asibitin Abuja, lokacin da ya ji zazzabi mai zafi ya rufe shi.
"Matakin da ya dauka na kai kansa abinci, da kuma kokarin da ma'aikatan jinya da sauran malaman asibiti suka yi, ya taimaka an dauki matakin gaggawa tare da ganin ba a samu barkewar cutar ba, da ace yana dauke da ita.
"Wannan abin a yaba ne, lallai, kowane dan Najeriya na da hakkin gabatar da kansa domin ayi masa gwaje-gwaje da zarar ya kamu da rashin lafiya bayan dawowa daga kasar waje."

Kara karanta wannan
Filato: Bincike ya bankado yadda aka hallaka mutum kusan 12,000 a 'yan shekarun nan
- Dr Jide Idris.

Source: Getty Images
Shirye-shiryen NCDC kan cututtuka
Hukumar NCDC ta ce ta riga ta ɗauki matakan kariya bayan samun barkewar cututtuka a wasu ƙasashe.
Wannan ya haɗa da tsaurara bincike a filayen jirgin sama, tabbatar da cewa an tanadi komai a asibitocin da ake killace marasa lafiya, da kuma rarraba kayan kariya.
An shawarci jihohi da su ƙarfafa sa ido kan cututtuka, su shirya cibiyoyin killace marasa lafiya, sannan likitoci, su kasance cikin shiri a kowane lokaci.
Hakanan, an bukaci jama’a su kula da tsafta, su guji hulɗa da dabbobi masu haɗari, su kuma hanzarta zuwa asibiti idan sun kamu da rashin lafiya da ba a saba gani ba.
Ebola ta kashe mutane 15 a Congo
A wani labarin, mun ruwaito cewa, akalla mutane 15 suka mutu yayin da aka samu barkewar sabuwar kwayar cutar Ebola a Jamhuriyyar Congo.
An rahoto cewa mutane 28 ne ake zargin suna dauke da cutar a lardin Kasai, inda aka gano wata kwayar Ebola da ake kira da Zairense.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun farmaki bayin Allah suna ibada, an rasa rayukan mutane 22 a Nijar
Hukumar lafiya ta duniya ta ce yanzu haka tana aiki cikin gaggawa domin dakile yaduwar cutar tare bayyana matakan da ta fara dauka a Congo.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
