Cutar Marburg: Abubuwa 4 da ya kamata ku sani sabuwar cuta mai kama da Ebola

Cutar Marburg: Abubuwa 4 da ya kamata ku sani sabuwar cuta mai kama da Ebola

Cutar Marburg ta samo asali ne daga biranen Marburg da Frankfurt da kuma Belgrade a kasar Yugoslavia a shekarar 1987.

A cewar WHO, cutar ta samo asali ne daga jemagu.

An fara gano cutar Marburg ne a 1967, inda mutane 31 sukayi rashin lafiya a Jamus da Yugoslavia inda aka gano cewa akwai cutar jikin birai a Uganda.

Legit tattaro muku abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da wannan cuta:

1. Tana iya bazuwa tsakanin mutum zuwa mutum

A cewar WHO, cutar ta samo asali ne daga cikin jemagu kuma tana iya bazuwa tsakanin mutum zuwa mutum ta zufar jiki ko idan yawun mutum ya fada kan abubuwa.

Idan mutum ya taba wani abu da kwayar cutar ta fada kai, mutum na iya kamuwa.

Kara karanta wannan

Dawowar Korona karo na 3: Gwamnatin tarayya ta yi magana kan sake kafa dokar kulle

2. Adadin mutane mafi yawa da suka mutu sakamakon cutar a shekara shine 227

A cewar Wikipedia, tun lokacin da cutar ta bulla a 1967, adadin mutanen da ta hallaka a shekara guda 227.

Mutum 227 sun mutu a shekarar 2004-2005 a Angola.

Bayan haka garin Durba da Watsa, a kasar Congo ta yi rashin mutum 128 tsakanin 1998-200.

Cutar Marburg: Abubuwa 4 da ya kamata ku sani sabuwar cuta mai kama da Ebola
Cutar Marburg: Abubuwa 4 da ya kamata ku sani sabuwar cuta mai kama da Ebola Hoto: cnn.com
Asali: UGC

3. Alamomin kamuwa da cutar

A cewar WHO, alamomin kamuwa da cutar sun hada da zazzabi, ciwon kai, gudawa, ciwon mara.

Wanda ya kamu da cutar cikin kwanaki bakwai, ana iya ganin jini cikin amansa da ba haya.

4. Babu maganin cutar

Kawo yanzu, babu rigakafin wannan cuta kuma babu maganinta, illa yan magunguna da ake baiwa masu fama da ita don rage radadi.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Wata sabuwar cuta 'Marbug' mai kama da Ebola ta bulla a kasar Guinea, kusa da Najeriya

'Marbug' mai kama da Ebola ta bulla a kasar Guinea, kusa da Najeriya

Wani mara lafiya ya kamu da wata cutar Marburg a kasar Guinea kuma ya mutu, a cewar jawabin da kungiyar lafiyar duniya ta saki ranar Litinin, 9 g Agusta, 2021.

CNN ta ruwaito cewa Wannan shine karo na farko da wata cuta mai kama da Ebola zata bulla a yankin yammacin Afrika.

An dauki samfurin Wannan cuta mai sanya mutum zazzabi daga jikin wani mara lafiya Gueckedou.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng