Shugaba Tinubu Ya Ziyarci Iyalan Buhari a Kaduna, An Ji Abin da Ya Fadawa Aisha
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci iyalan marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a gidansu da ke cikin Kaduna
- Tinubu ya tabbatar wa Aisha Buhari da sauran iyalan marigayin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da dabbaka ayyukan da ya bari
- Shugaban ya kai wannan ziyara ne yayin da ya je Kaduna domin halartar daura auren dan tsohon gwamnan Zamfara, Sanata Abdul'aziz Yari
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyarar ta'aziyya gidan Marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ke jihar Kaduna.
Mai girma Tinubu ya je gidan Buhari ne yayin da ya ziyarci Kaduna domin halartar daurin auren dan tsohon gwamnan Zamfara kuma Sanata mai ci, Abdul'aziz Yari.

Source: Twitter
Mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin kafafen sada zumuntar zamani, Dada Olusegun ne ya tabbatar da hakan a bidiyon da ya wallafa a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan baku manta ba, Muhammadu Buhari ya rasu ne a wani asibiti a birnin Landan na kasar Birtaniya ranar Lahadi, 13 ga watan Yuli, 2025.
Shugaba Tinubu ya shirya wa Buhari jana'izar girmamawa a Daura kuma da kansa ya tashi daga Abuja ya halarci wurin suturar marigayi abokinsa na siyasa.
Tinubu ya ziyarci iyalan Buhari a Kaduna
A yau Juma'a, 19 ga watan Satumba, 2025, Tinubu ya kai ziyara Kaduna domin halartar bikin dan Sanata Abdul'aziz Yari, Nasirudeen da amaryarsa, Safiyya Idris.
Bayan daura auren, Tinubu ya wuce zuwa gidan Buhari na nan Kaduna, inda ya kara yi wa Aisha Buhari ta'aziyya tare da tabbatar mata cewa gwamnatinsa na tare da su
Da yake jawabi a gidan Buhari, Shugaba Tinubu ya ce marigayin ya rasu amma ya bar masu halaye na kirki da za su ci gaba da koyi da su.
Abin da Tinubu ya fada a gidan Buhari
"(Buhari) ya rasu ya bar mu amma ya bar mana gadon da za mu dauka, ya bar mana gadon kyakkyawan fata, sadaukarwa kishin kasa da gaskiya."
"Ina tabbatar miki (Aisha Buhari) da sauran iyalansa cewa za mu dabbaka ayyukan da jagoranmu ya bar mana kuma za mu tabbatar cewa sun dore."
- In ji Shugaba Tinubu.

Source: Twitter
Shugaba Tinubu ya hadu dan marigayin, Yusuf Buhari, da Hajiya Aisha Buhari a wannan ziyara da ya kai masu a Kaduna yau Juma'a.
Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda na cikin manyan jiga-jigan da suka shiga tawagar Shugaba Tinubu da ta ziyarci gidan Marigayi Muhammadu Buhari.
Bola Tinubu ya kara tunawa da Marigayi Buhari
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta manta da magabacinsa, Marigayi Muhammadu Buhari ba.
Tinubu ya bayyana haka ne bayan karbar bakuncin wasu manyan jiga-jigan 'yan Najeriya karkashin jagorancin Gwamna Dikko Umaru Radda a fadarsa da ke Abuja.
Shugaban kasar ya kara da cewa za su mika komai ga Ubangiji wanda ya halicci kowa kuma su rungumi hukuncinsa bayan rasuwar Buhari tare da yi masa addu'ar samun gidan aljanna.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

