Rashin Imani: Wata Mata Ta Sa Cokali a Wuta, Ta Cusa a Al'aurar Kanwar Mijinta
- Yan sanda sun kama matar aure, Zuwaira Hassan bisa zargin cusa karfe mai zafi a al'aurar kanwar mijinta a jihar Bauchi
- Rahoto ya nuna cewa matar ta aikata wannan danyen aiki ne saboda ta na zargin cewa kanwar mijin, yar shekara 10 a duniya, mayya ce
- Kwamishinan yan sandan Bauchi ya sha alwashin gudanar da bincike mai zurfi domin tabbatar da an yiwa yarinyar da aka zalunta adalci
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi - ‘Yan Sandan Jihar Bauchi sun kama matar aure, Zuwaira Hassan da ke zaune a Magama-Gumau a karamar hukumar Toro, bisa zargin kona al'aurar kanwar mijinta.
Ana zargin matar ta yi amfani da wani cokalin karfe da ya dauki zafi bayan ta sanya shi a wuta, ta kona wasu sassan al'aurar yarinyar 'yar shekara 10 a duniya.

Kara karanta wannan
An yi rashi: Bayan rasuwar tsohon sufeta janar na yan sanda, an sanya ranar jana'izarsa

Source: Original
Yadda matar aure ta zalunci kanwar mijinta
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar yan sandan Bauchi, CSP Mohammed Ahmed Wakil, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, cewar rahoton Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
“A ranar 11 ga Satumba, 2025 da misalin ƙarfe 12:30 na dare, wani Yahuza Usman, ya kai rahoton abin da ya faru a ofishin ‘yan sanda na Toro.
"Ya shaida wa yan aanda cewa matar dan uwansa, Zuwaira Hassan ta yi amfani da cokalin karfe da aka sa a wuta ya dau zafi, ta cusawa yar uwarsa mai shekara 10 a al'aura.'
'Yan sanda sun garzaya wajen da abin ya faru, suka dauki yarinyar zuwa asibitin gwamnati na Toro domin samun kulawar gaggawa, sannan suka cafke wadda ake zargi.
Matar ta fadi dalilin yi wa yarinyar haka
Kakakin 'yan sandan ya kara da cewa yayin bincike, Zuwaira ta amsa laifinta da cewa tun farko yarinyar ta sa aka canza wa 'yayanta dakin kwana, suka koma kwanciya wuri daya.
"Zuwaira ta ce bayan canza dakin, ‘ya’yanta biyu sun fada mata cewa suna ta yin mafarkai marasa daɗi game da yarinyar.
"Hakan ya sa ta kai yarinyar wajen wata mai maganin gargajiya, Fatima Abdullahi, wadda ta ce yarinyar mayya ce, ta kuma ba ta magungunan gargajiya na kariya daga mayu."
"Daga baya, Zuwaira ta saka cokalin ƙarfe cikin wuta, ta umurci ‘ya’yanta Umar Ibrahim da Abubakar Ibrahim su daure hannuwa da ƙafafun yarinyar, sannan ta tura mata cokalin mai zafi a al’aura bisa umarnin wannan mai magani."
- CSP Mohammed Ahmed Wakil.

Source: Twitter
Wane mataki yan sanda suka dauka?
Ahmed Wakil ya ce yan sanda sun yi nasarar kama wannan mai magani tare da matar da ake zargi, yanzu haka ana ci gaba da bincike kan lamarin, in ji Daily Post.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya ba da umarnin a mika lamarin sashen binciken manyan laifuffuka (SCID) domin gudanar da bincike mai zurfi, tare da tabbatar da cewa an yi wa yarinyar adalci.
Magidanci ya kai karar saurayin diyarsa a Kaduna
A wani labarin, kun ji cewa wani magidanci ya kai karar saurayin diyarsa gaban kotu a jihar Kaduna bisa zarginsa da satar kudin gadon matarsa da ta mutu.
Mutumin mai suna Joseph, ya shaidawa alkali cewa saurayin ya kwashe kudaden da suka kai Naira miliyan 13 da aka biya a matsayin fanshon mamaciyar.
Diyar magidancin ta ce saurayinta ya dauki katin ATM ɗinta ba tare da ta sani ba, sannan ya cire kudin daga asusun bankinta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

