Sauki Ya Samu da Aka Hallaka Tantirin Dan Bindiga Yana cikin Shirya Kai Mummunan Hari

Sauki Ya Samu da Aka Hallaka Tantirin Dan Bindiga Yana cikin Shirya Kai Mummunan Hari

  • Hadin gwiwar jami’an tsaro sun ceto wani ma’aikacin gwamnati da aka sace tare da kashe wani fitaccen shugaban ‘yan ta’adda
  • Rahotanni sun nuna cewa dan bindigar da tawagarsa sun jagoranci kashe yan sa-kai, satar mata da kuma garkuwa da mutane
  • Rundunar ta kwato bindigogi, wayoyi, kudade da kayan tsafi daga maboyar ‘yan ta’addan, inda aka tabbatar da tsaurara sintiri a Abuja

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Hadin gwiwar jami’an tsaro da suka haɗa da 'Guards Brigade', Rundunar ‘Yan sanda, da DSS, sun yi wa yan ta'adda illa.

Yayin sinitirin da aka yi, jami'an sun ceto wani ma’aikacin gwamnati tare da kashe fitaccen jagoran ‘yan ta’adda, Abdullahi Umar, wanda aka fi sani da “Duna”.

Jami'an tsaro sun hallaka shedanin dan bindiga
Gundun yan bindiga da dakarun sojoji a fagen daga. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Twitter

An yi nasarar hallaka tantirin dan bindiga

Majiyoyi sun shaida wa Zagazola Makama cewa nasarar ta biyo bayan munanan hare-haren da tawagar suka yi, ciki har da kashe wani dan sa-kai.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: An kama tireloli 2, wasu motoci cike da kayan 'yan ta'adda

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar majiyoyin, a ranar 15 ga Satumba da misalin karfe 9:15 na dare, ‘yan ta’addan sun kai wa yan sa-kai hari a shingen Kpobi, inda mutum biyu suka jikkata.

Daya daga cikin yan sa-kai da ake kira Bako Pwaza, daga bisani ya rasu a Asibitin Abuja, bayan samun raunukan bindiga a farmakin.

A ranar 17 ga Satumba da misalin 10:32 na dare, wannan tawaga ta toshe hanyar Bristol Academy a Karu, inda suka sace Nafiu Idris, jami’in FCTA.

Wata majiya ta ce:

“Jami’an Anti-Kidnapping Unit suka hada kai da Guards Brigade, DSS, masu farauta da yan sa-kai, suka bi sahun maboyar ‘yan ta’addan.
“A ranar 18 ga Satumba da misalin 7:30 na safe, ‘yan ta’addan sun yi artabu da jami’an tsaro, uku sun mutu ciki har da ‘Duna’.”
Jami'an hadin guiwa sun kashe dan bindiga a Abuja
Rundunar yan sanda da dakarun sojoji a Najeriya. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Twitter

Nasarorin da jami'an tsaro suka samu

An bayyana cewa, an ceto Nafiu Idris da aka yi garkuwa da shi don a biya Naira miliyan 150, ba tare da wani lahani ba aka kubutar da shi.

Kara karanta wannan

Malami ya shiga rikici da gwamna, ana zarginsa da ingiza ta'addanci a jihar Kebbi

Jami’an tsaro sun kwato bindigogi biyu AK-49, mujallu biyu, harsasai, wayoyi, katunan ATM, kudade, kayan tsafi, da sauran kayayyaki daga sansanin ‘yan ta’addan.

Majiyoyin sun bayyana cewa “Duna” shi ne ya kitsa manyan hare-haren garkuwa da mutane a Karu, Guzape, Kpaduma, Kurudu da sassa na jihar Nasarawa.

An kuma gano cewa tawagar ta shirya wani sabon hari a ranar 18 ga Satumba da misalin 10:00 na dare a rukunin gidaje na gwamnatin tarayya da ke, Karu.

Sojoji sun kashe Kachallah Babangida a Kwara

A baya, kun ji cewa sojojin Najeriya karkashin Operation Accord III sun yi nasarar kashe mataimakin shugaban ‘yan ta’adda a jihar Kogi.

Dakarun sun yi arangama da miyagun ne a cikin daji bayan samun sahihin bayanan sirri kan wajen da suke haduwa.

Bayan nasarar, rundunar ta ce za ta ci gaba da sintiri da kai farmaki don kawar da barazanar ‘yan ta’adda a fadin jihar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.