Shugaba Tinubu Ya Isa Jihar Kaduna domin Halartar Daura Auren 'Dan Tsohon Gwamna

Shugaba Tinubu Ya Isa Jihar Kaduna domin Halartar Daura Auren 'Dan Tsohon Gwamna

  • Manyan jiga-jigan gwamnatin tarayya, gwamnoni, sanatoci da 'yan Majalisar Tarayya sun taru a Kaduna domin halartar daurin auren
  • Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya dura Kaduna domin zuwa daura auren dan Sanata Abdul'aziz Yari mai suna Nasirudeen Yari
  • Gwamna Uba Sani, Babagana Zulum da wasu gwamnonin jihohi da Shugahannin Majalisar Tarayya sun tarbi Tinubu a filin jirgin sama

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya isa Kaduna a wata ziyara ta kwana daya da ya tsara kai wa jihar.

Rahoto ya nuna cewa jirgin shugaban kasar ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na kasa da kasa da ke garin Kaduna da misalin karfe 1:00 na rana yau Juma'a.

Shugaba Tinubu da Uba Sani.
Hoton Shugaba Bola Tinubu tare da Uba Sani bayan ya isa Kaduna Hoto: @SundayDare
Source: Twitter

Tashar Channels tv ta tattaro cewa Shugaba Tinubu ya samu tarba mai kyau daga gwamnoni da 'yan Majalisar Tarayya a lokacin da ya isa jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Majalisar Rivers ta ba Fubara umarnin gaggawa kan kasafin kudi da kwamishinoni

Yadda aka tarbi Shugaba Tinubu a Kaduna

Gwamnan Jihar Kaduna, Malama Uba Sani, tare da Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ministoci, sanatoci da sauran manyan jami’an gwamnati ne suka tarbi Tinubu a filin jirgi.

Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon Tajudeen Abbas da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio na cikin tawagar da ta tarbi Bola Tinubu.

Abubuwan da Tinubu zai yi a Kaduna

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya je Kaduna ne domin halartar bikin ɗaurin aure tsakanin Nasirudeen Abdul'aziz Yari da Safiyya Idris.

Nasirudeen ɗa ne ga tsohon gwamnan Zamfara kuma sanatan da ke wakiltar Zamfara ta Yamma a yanzu, Abdul’aziz Yari.

Ana kuma sa ran cewa yayin ziyarar, Shugaba Tinubu zai kai ziyara gidan tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari, a gidansa da ke Kaduna.

Idan ba ku manta ba, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya rasu a watan Yulin da ya gabata bayan fama da jinya a wani asibiti a birnin Landan.

Kara karanta wannan

Tinubu zai je gidan Buhari, manyan kasa za su dura Kaduna auren dan Sanata Yari

Shugaba Tinubu ya jagoranci tawagar gwamnatin Najeriya a wurin jana'izar girmamawa da aka shiryawa Buhari a Daura, jihar Katsina.

Ana ran Tinubu zai je gidam Buhari na Kaduna a wannan ziyara da ya kai yau Juma'a, domin sake yi wa Aisha Buhari, matar marigayin ta'aziyya.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Hoton mai girma shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @officialABAT
Source: Facebook

Bidiyon lokacin da Tinubu ya isa Kaduna

Imran Muhammad, wani sanannen mai amfani da kafafen sada zumunta ya wallafa bidiyon lokacin da Tinubu ya isa Kaduna a shafinsa na X.

Ya rubuta cewa:

"Shugaba Tinubu ya isa Kaduna domin halartar ɗaurin auren ɗan Sanata Abdul'aziz Yari.
"Ya samu tarba daga mai masaukin baki, Gwamna Uba Sani, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio; Mataimakinsa, Barau Jibrin, Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas; gwamnonin jihohi; sanatoci; ministoci; tsofaffin gwamnoni, da sauran manyan baki."

Tinubu ya ba Izala tallafin N10m

A wani labarin, kun ji cewa, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da tallafin miliyoyin kudi ga kungiyar JIBWIS wacce aka fi sani da Izala mai hedkwata a Jos.

Shugaba Tinubu ya yabawa kungiyar Izalah ta Jos bisa irin gudunmawar da ta ba shi a gwamnatinsa wanda ba zai taba mantawa da ita ba.

Kara karanta wannan

PDP ta fara rokon Fubara bayan APC ta yi masa tayin sauya sheka

Tinubu ya ba kungiyar reshen Gombe gudunmawar Naira miliyan 10 domin inganta ayyukansu duba da gudunmawar da suke ba shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262