Mambilla: EFCC Ta Maida Tsohon Minista gaban Kotu kan Zargin Almundahanar $6bn
- Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta sake gurfanar da tsohon Ministan Wuta, Olu Agunloye gaban kotu
- EFCC ta zarge shi da bijirewa umarnin Shugaban Kasa a 2003 da kuma bayar da kwangilar Mambilla ba tare da an ba shi izini ba
- Agunloye ya musanta laifuffuka bakwai da ake tuhumarsa da su, ya kuma fadi dalilin da a ganinsa, ya sa gwamnati ta maida shi saniyar ware
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC) ta kara gurfanar da tsohon Ministan Wuta da Karafa, Dr. Olu Agunloye, a gaban kotu.
EFCC ta mayar da shi gaban babbar kotun birnin tarayya da ke Apo, Abuja, bisa zargin aikata laifuffuka bakwai da suka shafi karɓar rashawa da bijire wa umarnin shugaban kasa.

Source: Facebook
Premium Times ta wallafa cewa an gurfanar da Agunloye ne a gaban Mai shari’a Jude Onwuegbuzie, inda ya karyata dukkan zarge-zargen da aka karanto masa a kotu.
EFCC ta sake mayar da tsohon Minista kotu
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Lauyan EFCC, M.K. Hussain, ya shaidawa kotu cewa hukumar ta sabunta tuhumar da take yi wa Agunloye.
Hukumar ta bakin lauyan, ta nemi a sake karanta masa zarge-zargen a yayin da lauyoyin wadanda ake kara, karkashin Adeola Adedipe (SAN), su ka ki amincewa da hakan.
A cewar EFCC, Agunloye ya sanya hannu a kan wata wasika da aka ce an tura wa kamfanin Sunrise Power and Transmission Ltd.
Ana zargin ya shaida wa kamfanin cewa gwamnatin Najeriya ta amince da gina tashar wutar lantarki ta Mambilla mai karfin megawatts 3,960.
Hukumar ta kara da cewa:
“Dr. Agunloye ya karya umarnin da shugaban kasa ya bayar a zaman majalisar zartarwa ta kasa a shekarar 2003, inda aka ki amince da bayar da kwangilar.”
Sauran zarge-zargen hukumar EFCC
EFCC ta kuma zargi Agunloye da hadin baki da wani Leno Adesanya wajen samar da takardar kwangilar aikin Mambillana jabu a karkashin wani tsari.
Har ila yau, an zargi Agunloye da karɓar sama da N5m daga kamfanin da kuma daga hannun Leno Adesanya a matsayin rashawa.
Sai dai Agunloye ya musanta dukkannin tuhumar da ake yi masa na samar da takardun bogi, rashawa da saba umarnin Shugaban Kasa,

Source: Twitter
Mai shari’a Onwuegbuzie ya dage cigaban shari’ar zuwa 9 ga Oktoba, 2025, domin ci gaba da sauraron shaidu.
A zaman kotun na baya, wani ma’aikacin banki, Adebayo Ilori, ya bayyana yadda wani ma’aikacin Sunrise, Jude Sotirin, ya aika wa Agunloye kudi N5m.
Tun farko, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya zargi Agunloye da bayar da kwangilar aikin Mambilla ba tare da izini ba a 2003.
Sai dai Agunloye ya ce ana kokarin mayar da shi saniyar ware kan matsalolin da suka biyo bayan gazawar gwamnati wajen cika sharuddan kwangilar.
Hukumar EFCC ta neman 'dan kasuwa
A baya, mun ruwaito cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta bayyana cewa tana neman wani attajirin dan kasuwa, Olasijibomi Suji Ogundele, ruwa a jallo.
A cewar sanarwar da EFCC ta fitar, ta ce ana neman Ogundele ne bisa zargin aikata laifuffuka da suka shafi karkatar da kudi da safarar kudin haram da sauran tuhume-tuhume.
Olasijibomi Ogundele, dan asalin karamar hukumar Ori-Ade a jihar Osun, shi ne shugaban kamfanin gine-gine na Sujimoto da ya shahara wajen gina gidaje masu tsada a Legas.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


