An Yi Rashi: Bayan Rasuwar Tsohon Sufeta Janar na Yan Sanda, an Sanya Ranar Jana'izarsa
- Rundunar ‘yan sanda ta fitar da cikakken jadawalin jana’izar tsohon sufeta janar na hukumar, Solomon Arase
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa Arase ya rasu ne a ranar 31 ga Agustan shekarar 2025 yana da shekara 69 a duniya
- Jana’izar za ta fara a Abuja ranar 24 ga Satumba da taron tunawa, sannan ta ci gaba da addu’o’i da tafiya Benin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Bayan sanar da rasuwar tsohon sufeta janar na yan sanda, Rundunar a Najeriya ta sanar da jadawalin jana’izarsa.
Marigayi Solomon Ehigiator Arase ya rasu ne a ranar 31 ga Agustan shekarar 2025 yana da shekara 69 a duniya.

Source: Twitter
Za a birne tsohon sufetan yan sanda
Hakan na cikin wata sanarwa da rundunar yan sanda ta tabbatar a shafinta na Facebook a jiya Alhamis 18 ga watan Satumbar 2025.

Kara karanta wannan
Jiragen yakin sojin saman Najeriya sun jefa bama bamai a Borno, an kashe ƴan ta'adda
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar ta ce ta shirya karrama Arase ne saboda gudunmawar da ya ba al'umma yayin da yake aiki wanda ba za a taba mantawa da hakan ba.
Majiyoyinmu sun ce an yabawa tsohon sufeta janar na 18 daga cikin ‘yan sauran, saboda jagoranci, aikin alheri da kuma jajircewa wajen gyaran tsarin aikin ‘yan sanda.

Source: Twitter
Jadawalin birne marigayi Solomon Arase
A cewar sanarwar CSP Benjamin Hundeyin, za a fara bikin a Abuja ranar 24 ga Satumba da taron tunawa a cibiyar ‘yan sanda ta Jabi.
Za a ci gaba da addu’ar a ranar 26 ga Satumba a 'Holy Trinity Catholic Church', Maitama, sannan a koma gidansa a Abuja, kafin a kai Benin.
A Sabongida-Ora, za a gudanar da tafiyar kyandir ranar 29 ga Satumba, ranar 2 ga Oktoba kuma za a yi zaman ban kwana a kotu.
Haka nan, za a yi waƙar bauta a 'St. Paul’s Catholic Church', sannan a gudanar da addu'a ta musamman na iyali kafin jana’izar babba.
Za a yi babban jana’iza ranar 3 ga Oktoba a 'St. Paul’s Catholic Church', sannan a birne shi a gidansa na Benin City.
Sauran shirye-shiryen jana'izar Arase
Bayan haka za a yi liyafar taro a wurin taro na Victor Uwaifo, sannan ranar 5 ga Oktoba kuma za a rufe da addu’ar godiya.
Solomon Arase, mai lambar yabo ta CFR da digirin PhD a fannin shari’a, ya zama IGP a Afrilu 2015, ya yi ritaya a Yuni 2016.
Ya rasu a asibitin Cedarcrest, Abuja, bayan gajeriyar rashin lafiya da ya yi fama da ita, inda ya bar babban tarihi a Najeriya.
An samu bayanai kan rasuwar Solomon Arase
Kun ji cewa kwamishinan hukumar da'ar ma'aikata ta Najeriya kuma tsohon dan Majalisa ya yi bayani kan rasuwar tsohon sufetan yan sanda, Dr. Solomon Arase.
A yan kwanakin nan dai an fara yada jita-jitar cewa Arase ya mutu ne sakamakon gubar da ya ci a abinci.
Jita-jitar ta kuma jero sunayen wasu manyan mutane da ake zargin su suka hada baki wajen ganin bayan tsohon shugaban yan sandan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
