Kwana Ya Kare: Malamin da Ya Fi 'Tsufa' Yana Wa'azi Ya Bar Duniya Yana Shekaru 95
- Al’ummar Kirista a Jihar Benue sun shiga jimami bayan rasuwar tsohon fasto mafi tsufa, Simon Agu Mashika
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa marigayin da ya fi kowa shekaru a Fastoci ya mutu yana da shekara 95 bayan fama da jinya
- Marigayin, wanda aka haifa 1930, ya sadaukar da fiye da shekaru 70 cikin hidimar bishara, yana yin wa’azi cikin sauki da imani mai karfi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Makurdi, Benue - Al’ummar Kirista a Jihar Benue sun shiga makoki bayan rasuwar fitaccen malamin addini da ya sadaukar da rayuwarsa.
Rahotannin sun tabbatar da mutuwar Fasto Simon Agu Mashika, wanda aka dauka a matsayin tsohon fasto mafi tsufa.

Source: Facebook
Babban Fasto ya mutu a jihar Benue
Hakan na cikin wata sanarwa da daya daga cikin 'ya'yansa, Sunday Imoh ya tabbatar a shafin Facebook a yau Alhamis 18 ga watan Satumbar 2025.

Kara karanta wannan
Filato: Bincike ya bankado yadda aka hallaka mutum kusan 12,000 a 'yan shekarun nan
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Imoh ya ce marigayin mai shekaru 95 shi ne babban yayan mahaifiyarsa wacce take da shekaru 77 a duniya.
Matashin ya ce ana tsammanin marigayin Faston ya fi kowa dadewa yana wa'azi har zuwa yau da Ubangiji ya karbi rayuwarsa.
Ya ce:
"Duk da muna godewa Allah saboda kyakkyawar rayuwa mai tsawo, cike da kauna, kulawa da daraja ta Pa Mashika.
"Za mu dade muna kewar abin da Baba ya yi, Baba wataƙila shi ne tsohon malamin wa’azi mafi tsufa har zuwa yau."

Source: Original
Takaitaccen tarihin Fasto Mashika da gudunmawarsa
Majoyoyi sun tabbatar da cewa marigayin ya rasu cikin salama a barcinsa yana da shekara 95 a duniya.
An haifi Mashika a shekarar 1930, inda ya sadaukar da fiye da shekaru 70 yana hidimar bishara cikin sauki da tsantsar bangaskiya.
Ko da a tsufarsa, ya kasance mai shiga ayyukan coci, yana tuka kansa a mota zuwa hidima kuma yana karanta Littafi Mai Tsarki ba tare da gilashi ba.
Har zuwa rasuwarsa, Mashika yana kasancewa akai-akai a shirye-shiryen 'Remnant Christian Network' a Makurdi, yana yi wa’azi da addu’o’i.
Wani Fasto Arome Osayi, wanda kan gayyace shi kan dandalin wa’azi, ya bayyana shi a matsayin wakili kuma mai nemawa al'umma mafita.
Mutane da dama sun yaba da rawar da ya taka wajen karfafa bangaskiya a Benue tare da renon matasa da dama cikin aikin bishara.
Fasto Mashika ya bar iyalinsa, ‘ya’yansa da kuma masoyansa da dama, ana sa ran iyalansa za su sanar da shirye-shiryen jana’iza a kwanaki masu zuwa.
Babban Fasto ya bar duniya
Kun ji cewa al'ummar Kiristoci a Najeriya sun yi rashi da mutuwar fitaccen malamin coci a jihar Enugu da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.
Babban Fasto na Nsukka, Rabaran Francis Okobo, ya rasu yana da shekara 89 a asibitin 'Niger Foundation, Enugu' da ke jihar.
An haifi Okobo ranar 4 ga Nuwambar shekarar 1936 yayin da aka nada shi limami a 1966, kuma ya zama babban Fasto na Nsukka a 1990.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
