Safarar Ƙwaya: Yadda Ƴan Najeriya 3 Suka Tsira daga Hukuncin Kisa a Saudiyya
- Mahajjatan Najeriya uku sun samu ‘yanci daga Saudiyya bayan makonni huɗu a tsare bayan da aka zarge su da safarar kwayoyi
- An gano cewa wata ƙungiyar masu safarar kwayoyi ce ta sanya kwayoyi a jakunkunan mahajjatan a filin jirgin saman Kano
- Bayan samun rahoton, Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin a tattauna da hukumomin Saudiyya, lamarin da ya kai ga an sako su
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Wasu mahajjatan Najeriya uku, sun tsira daga hukuncin kisa, bayan da aka tsare su makonni hudu a Saudiyya, bisa zargin safarar kwayoyi.
Mutanen sun samu 'yanci biyo bayan tattaunawa tsakanin hukumar NDLEA da hukumar yaki da sha da fataucin kwayoyi ta Saudiyya (GDNC).

Source: Getty Images
Sunayen 'yan Najeriya da Saudiyya ta saki
Rahoton BBC Hausa ya nuna cewa, alhazan Najeriya ukun da aka saki bayan makonni huɗu a tsare sune:

Kara karanta wannan
Ribas: Peter Obi ya zargi gwamnatin Najeriya da yi wa dimokuradiyya kisan mummuke
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
- Hajiya Maryam Hussain Abdullahi daga jihar Jigawa
- Hajiya Abdullahi Bahijja daga jihar Kano
- Malam Abdulhamid Saddieq daga jihar Jigawa
Hukumar NDLEA ce ta tabbatar da sakin mahajjatan a taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Laraba, 17 ga Satumba, 2025.
Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi, ya bayyana cewa wata kungiyar masu safarar miyagun kwayoyi a filin jirgin saman Kano ce ta sanya kwayoyi a jakunkunan mahajjatan ba tare da saninsu ba.
Ya ce an sanya kwayoyi a kayan mutanen ne lokacin da za su je yin Umrah ta jirgin Ethiopian Airlines ET940 daga Kano zuwa Jiddih a ranar 6 ga Agusta, inda aka kama su bayan saukarsu.
Bincike ya fallasa masu safarar kwaya
Shugaban NDLEA, Janar Mohamed Buba Marwa (ritaya), ya umarci gudanar da cikakken bincike bayan iyalan mahajjatan sun kai koke game da kama 'yan uwansu.
Wannan bincike ya kai ga cafke shugaban ƙungiyar masu safarar kwayoyin, Mohammed Ali Abubakar wanda aka fi sani da Bello Karama, tare da wasu abokan harkallarsa uku ciki har da ma’aikatan jirgi.

Kara karanta wannan
NAHCON ta nuna damuwa, Sheikh Pakistan ya hango matsalar da za a iya samu a Hajjin 2026
Wadanda aka kama tare da Bello Karama akwai Celestina Emmanuel Yayock, Abdulbasit Adamu Sagagi, da Jazuli Kabir, kuma an riga an gurfanar da su gaban kotu, inji rahoton Punch.
Tinubu ya taimaka aka sako mahajjatan 3
Bayan samun shaidu da ke tabbatar da cewa mahajjatan Najeriyar ba su da laifi, Buba Marwa ya shiga tattaunawa kai tsaye da hukumomin Saudiyya, musamman hukumar GDNC.
Wannan mataki ya samu cikakkan goyon baya daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ya ce ba za a bar wani ɗan Najeriya ya sha wahala a ƙasar waje saboda abin da bai aikata ba.
An rahoto cewa, Saudiyya ta sako daya daga cikin mahajjatan a ranar Lahadi, yayin da aka sako sauran biyun a ranar Litinin.

Source: Facebook
Hukuncin sha da safarar kwayoyi a Saudiyya
Dokar Saudiyya kan yaki da miyagun kwayoyi, wadda aka kafa bisa umarnin sarki mai lamba 4/B/966, ta raba hukunci tsakanin masu safarar miyagun kwayoyi, masu fatauci, da masu amfani da su.
1. Masu fataucin miyagun kwayoyi
Hukunci mafi tsauri ga mutanen da ke da hannu wajen safarar miyagun kwayoyi da shigar da su cikin kasar Saudiyya shi ne kisa, cewar rahoton shafin gwamnatin Saudiyya.
Mutumin da ya shigo da miyagun kwayoyi daga waje ana daukarsa a matsayin "fataken miyagun kwayoyi," haka shi ma mutumin da ya karbi miyagun kwayoyi ya raba wa masu sayarwa.
2. Masu dillacin miyagun kwayoyi
Dokar miyagun kwayoyi ta bambanta tsakanin mutumin da ya fara dillacin miyagun kwayoyi a karon farko da kuma wanda aka riga aka hukunta a baya.
Ga wanda ya fara aikata laifin a karon farko, hukuncin dauri ne, ko bulala, ko tara, ko kuma dukkan su. Amma ga wanda ya maimaita laifin, ana kara masa hukunci kuma za a iya yanke masa hukuncin kisa.
3. Masu amfani da miyagun kwayoyi
Alkali na yanke ya masu tu'ammali da miyagun kwayoyi hukuncin daurin shekaru biyu kuma ana hukunta shi bisa shari'a.
Idan mai laifin ɗan ƙasar waje ne, ana korarsa shi daga kasar. Sannan mai tu'ammali da kwaya amma yana zuwa wajen likita don ya daina, ana kai shi asibitin da aka kebe don gyara tarbiyar masu shaye shaye.
Dokar Saudiyya, bisa ga shawarar Majalisar Dinkin Duniya, tana ɗaukar masu amfani da miyagun kwayoyi a matsayin majinyata da suke buƙatar kulawar likita.
Saudiyya ta cafke Maryam Hussaini
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Saudiyya ta cafke Maryam Hussaini Abdullahi, ‘yar Kano, bisa zarginta da mallakar wata jaka da aka samu tabar wiwi a ciki.
Abdullahi Baffa, mijin Maryam, ya zargi kamfanin jiragen Ethiopian Airlines da sauya jakunkuna, da ya jawo aka danganta sunan matarsa da jakar da ba tata ba.
Ya roƙi gwamnatin Najeriya ta taimaka wajen tabbatar da gaskiya, ciki har da buƙatar a duba bidiyon CCTV a filin jirgin Kano don wanke mai dakinsa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

