NECO: Kwankwaso Ya Yabi Aikin Abba bayan Daliban Kano Sun Doke na Sauran Jihohi

NECO: Kwankwaso Ya Yabi Aikin Abba bayan Daliban Kano Sun Doke na Sauran Jihohi

  • Daliban Kano sun faranta wa tsohon gwamnan jihar kuma tsohon dan takarar Shugaban Kasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso
  • Tsohon gwamnan ya bayyana cewa nasarar daliban ta nuna yadda gwamnatin Kano ta yi abin da ya dace a cikin shekaru biyu
  • Kwankwaso ya bayyana cewa ba haka kawai daliban su ka samu nasarar ba, musamman idan aka kwatanta da gwamnatin baya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon Gwamnan Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya jinjinawa daliban jihar a kan kwazon da su ka nuna a jarrabawar NECO.

Kwankwaso ya bayyana gamsuwarsa da sakamakon da daliban Kano su ka samu bayan NECO ta saki sakamakon SSCE na shekarar 2025 a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Babu karbo bashi: Uba Sani ya ce gwamnatinsa za ta yi ruwan ayyukan raya Kaduna

Kwankwaso ya jinjina wa daliban Kano
Hoton Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da Abba Kabiru Yusuf Hoto: @KwankwasoRM
Source: Twitter

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis, Sanata Kwankwaso ya ce wannan ba nasara ce kawai ga daliban kawai ba, har ma da jihar Kano baki daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NECO: Kwankwaso ya yabi daliban Kano

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana hazakar da daliban Kano su ka nuna a matsayin abin alfahari da ke nuna kokarin gwamnati a fannin ilimi.

Ya bayyana cewa:

"Ina so na taya daliban Kano murna da su ka zama kan gaba wajen samun sakamako mafi kyau a jarrabawar kammala sakandare ta NECO a tsakanin takwarorinsu."

Tsohon gwamnan ya ce ba haka kawai daliban su ka samu wannan gagarumar nasara ba, illa sakamakon tsayawa tsayin daka da Gwamnatin Kano ke yi wajen farfado da harkar ilimi a jihar.

Kwankwaso ya yabi Abba Gida Gida

Kwankwaso ya ce daliban Kano sun samu canji daga matsayi da su ke kai a lokacin da aka rike sakamakon jarrabawarsu saboda rashin biyan kudin jarrabawa.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara na shirin komawa mulki, dandazon mutane sun mamaye gidan gwamnati

Ya ce a yanzu, sun koma matakin jagora a kasar nan saboda yadda gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta bai wa ilimi fifiko a yadda ta ke tafiyar da gwamnati.

Kwankwaso ya jinjinawa gwamnatin Kano
Hoton tsohon Gwamnan Kano Rabi'u Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Kwankwaso ya ce:

"Dole ne a yaba wa gwamnatin Kano, a karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf na farfado da ilimi."

Tsohon Sanatan ya bayyana cewa wannan ci gaba wata alama ce ta amfanin da ke cikin bai wa bangaren ilimi muhimmancin da ya dace.

"Wannan alama ce karara da ke nuna cewa ci gaba da zuba hannun jari da bangaren ilimi da gwamnatin Kano ta yi a cikin shekaru 2."

Ya kuma bukaci Gwamnatin Jihar Kano da sauran masu ruwa da tsaki su ci gaba da tabbatar da wannan nasara da kuma ƙara ƙaimi wajen inganta tsarin ilimi.

Kwankwaso ya jaddada cewa ingantaccen ilimi shi ne garkuwar al’umma, kuma ci gaban kowace jiha zai dogara ne da irin ilimin da matasanta ke samu.

Abba ya yi murnar nasarar daliban Kano

A baya, mun ruwaito cewa Kano ta samu babban nasara a jarrabawar kammala makarantar sakandare (NECO) ta shekarar 2025, inda ta kasance kan gaba a wadanda su ka ci jarrabawar.

Kara karanta wannan

Filato: Bincike ya bankado yadda aka hallaka mutum kusan 12,000 a 'yan shekarun nan

Rahoton da hukumar NECO ta fitar ya nuna cewa daga cikin dalibai 1,358,339 da suka zauna jarrabawar, fiye da 818,000 sun samu aƙalla darussa biyar ciki har da Lissafi da Turanci.

Kano ta fi kowacce jiha fice da dalibai 68,159 da suka ci darussa biyar da suka haɗa da waɗannan muhimman darussa, Lagos ta zo ta biyu da dalibai 67,007 yayin da Oyo ta biyo baya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng