Filato: Bincike Ya Bankado Yadda aka Hallaka Mutum kusan 12,000 a 'Yan Shekarun nan

Filato: Bincike Ya Bankado Yadda aka Hallaka Mutum kusan 12,000 a 'Yan Shekarun nan

  • Kwamitin da gwamnatin Filato ta kafa domin binciken rikice-rikice a jihar da illolinsa ya kammala aikin da Gwamna Caleb Muftwang ya ba shi
  • Wani bangare na rahoton ya bayyana cewa fiye da mutane 11,749 ne suka rasa rayukansu a jihar daga 2001 zuwa 2025 saboda munanan hare-haren
  • Rahoton ya kuma gano cewa baya ga fadan kabilanci da addini ya dabaibaye jihar, akwai 'yan wasu jihohin da ke kai masu hari, sannan su tsere

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KanoJihar Filato ta sha fama da mummunan rikici iri-iri, daga ciki akwai rikicin manoma da makiyaya, da kuma rikicin addini da ƙabila na tsawon shekaru 24.

Kwamitin bincike da Gwamna Caleb Mutfwang ya kafa a watan Mayu 2025 ya fitar da rahoto a kan irin barnar da aka samu saboda wadannan rikice-rikice.

Kara karanta wannan

Rashin wuta: Bayan bayin Allah sun fara mutuwa, gwamnati ta kai sola asibitin Kano

An kai munanan hare-hare jihar Filato
Hoton Gwamnan Filato, Caleb Muftwang a cikin jimami Hoto: Plateau State Government
Source: Facebook

Premium Times ta wallafa cewa rahoton ya ce mutane 11,749 aka kashe, yayin da aka kai hari a ƙauyuka 420 tsakanin shekarar 2001 da Mayu 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kashe jama'a a Filato

Peoples Gazette ta wallafa cewa Shugaban kwamitin, Manjo Janar Nicholas Rogers mai ritaya, ya bayyana cewa an gudanar da bincike mai zurfi a kafin fitar da rahoton.

Ya ce an yi bincike a kan al’ummomin da lamarin ya shafa, jami’an tsaro, da kuma nazarin bayanan da su ka tattaro daga wadannan mutane.

Shugaban Kwamitin ya ce sun gano cewa rikicin ya shafi ƙananan hukumomi 13 a jihar yayin da aka salwantar da rayukan jama'a.

Rogers ya ce:

“Mun tabbatar da mummunan asarar rayuka da dukiyoyi. Mun gano 35% na dabbobi sun salwanta, 32.5% sun rasa matsugunnai, an lalata 16.8% na abinci, an kona 9.9% na gidaje sai kuma filaye 3.4% da aka kwace ba bisa ka’ida ba.”

Kara karanta wannan

Sulhu ya kankama, gwamna ya kawo shirin da za a tallafawa tubabbun 'yan bindiga

Ya ƙara da cewa, harin na da tasiri mara kyau ga lafiyar kwakwalwa, rayuwar jama'a da tattalin arziki.

Har ila yau, an gano cewa yawancin waɗanda ke kai harin na shigowa ne daga jihohin Taraba, Bauchi, Kaduna da Nasarawa, suna kai farmaki sannan su tsere.

Martanin Gwamnan Filato kan rahoton

Gwamna Caleb Mutfwang ya gode wa kwamitin bisa ƙwazon da suka nuna, tare da tabbatar da cewa zai tura rahoton zuwa gwamnatin tarayya domin aiwatarwa.

Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta riga ta fara ɗaukar matakai tun kafin kammala rahoton, ciki har da haya sababbin jami’ai fiye da 1,000 don shirin tsaron "Operation Rainbow".

An kashe mutane sama da 11,000 a Filato
Taswirar jihar Filato da ke fama da hare-hare Hoto: Legit.ng
Source: Original

Gwamnan ya ce:

“Mun fahimci cewa magance rikici ba wai kawai da bindiga ake yi ba, dole ne mu ɗauki matakan sulhu da ci gaban ɗan Adam. Mun kafa Hukumar Gina Zaman Lafiya domin shawo kan matsalolin tun daga tushe.”

Yan bindiga sun kai hari Filato

A baya, mun ruwaito cewa jama'a a jihar Filato sun shiga tashin hankali lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari a kauyuka har 10 a Doemak, dake karamar hukumar Qua’an-Pan.

Kara karanta wannan

An samu bayanai daga majiyar Aso Rock kan takarar Tinubu da Shettima a 2027

A wannan hari, miyagun mutanen sun kone gidaje sama da 30 kurmus, yayin da mutane fiye da 300 suka rasa matsugunni, lamarin da ya jefa jama'a a cikin mawuyacin hali.

Rahotanni sun nuna cewa harin ya zo ne yayin da manoma suke shirin girbin amfanin gona daga gonakinsu a jihar da ke fama da matsalolin tsaro daga na kabilanci zuwa na addini.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng