Rashin Wuta: Bayan Bayin Allah Sun Fara Mutuwa, Gwamnati ta Kai Sola Asibitin Kano

Rashin Wuta: Bayan Bayin Allah Sun Fara Mutuwa, Gwamnati ta Kai Sola Asibitin Kano

  • Gwamnatin tarayya ta kaddamar da aikin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a asibitin koyar wa na AKTH
  • An fara aikin ne bayan hukumar asibitin ta roƙi kamfanin rarraba hasken wuta na KEDCO ya dawo da wutar da ya yanke
  • Aikin da aka ƙaddamar a harabar AKTH da ke Kano zai laƙume Naira biliyan 12 a wani yunkuri na kare rayukan jama'a

A'isha Ahmd edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnatin tarayya ta kaddamar da aikin samar da wutar lantarki ta hasken rana a asibitin AKTH.

Ta ɗauki matakin ne kwanaki biyu kacal bayan rikicin wutar lantarki tsakanin asibitin da kamfanin rarraba wuta na KEDCO da asibitin.

Gwamnatin Tinubu ta ce za ta wadata manyan asibitoci da wuta
H-D: Hon. Bichi yana jawabi, dan majalisa da kayan fara aikin sola a AKTH Hoto: Hon Abubakar Kabiru Abubakar Bichi
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa Hon. Abubakar Bichi, wanda ya jagoranci kaddamarwar, ya bayyana cewa an ware sama da N12bn don yin aikin.

Kara karanta wannan

Filato: Bincike ya bankado yadda aka hallaka mutum kusan 12,000 a 'yan shekarun nan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta ƙaddamar da aikin sola a AKTH

'Dan majalisar ya bayyana cewa gwamnati ta yanke shawarar yin aikin domin raba asibitin da dogaro da wutar lantarki ta gwamnati gaba ɗaya.

Hon. Bichi, wanda shi ne ya jagoranci kawo aikin, ya ce wannan shiri wani ɓangare ne na manufar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ya ce manufar shirin a ƙarƙashin 'Renewed hope agenda' shi ne a samar da hasken wuta mai amfani da rana ga manyan jami’o’i da asibitocin koyarwa.

Bichi ya yi godiya ga Shugaba Tinubu bisa amincewa da tallafa wa aikin, yana mai cewa hakan na nuna jajircewar gwamnati wajen inganta harkokin kiwon lafiya.

'Dan majalisar ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ware sama da Naira biliyan 300 a cikin kasafin kuɗin 2025 domin ci gaba da aiwatar da wannan shiri.

Shirin gwamnati kan wutar lantarki

Hon. Abubakar Bichi, ya ce ana sa ran dukkanin manyan makarantu da asibitocin koyarwa za su samiy wuta mai hasken rana mai ɗorewa.

Kara karanta wannan

Dangote ya ce ana neman ya saka tallafin man fetur na Naira tiriliyan 1.5 a Najeriya

A nasa jawabin, Ministan Kimiyya, Fasaha da Ƙirƙira, Uche Nnaji, ya ce aikin na AKTH shi ne matakin farko na tabbatar da manufar gwamnati a kan hasken wutar lantarki.

A bangarensa, darakta-janar na Hukumar Samar da Makamashi ta Ƙasa (ECN), Dakta Mustapha Abdullahi, ya tabbatar da cewa za a kammala aikin kafin ƙarshen Disamba.

Gwamnatin tarayya ta kai aikin sola AKTH
Hoton Dan Majalisa, Hon Bichi da sauran jama'a a yayin kaddamar da aikin sola Hoto: Hon Abubakar Kabiru Abubakar Bichi
Source: Facebook

Ya ce hukumar ta himmatu wajen samar da wutar da ba ta da lahani ga muhalli, kuma mai araha a dukkanin cibiyoyin ilimi da asibitocin koyarwa.

Shugaban asibitin AKTH, Farfesa Abdulrahman Sheshe, ya bayyana farin cikinsa kan wannan ci gaba.

Ya ce asibitin na kashe sama da Naira miliyan 150 a wata kan kudin wuta da kuma Naira miliyan 30 wajen sayen dizal. Shugaba ne asibitin ya ce sabuwar hanyar samar da wutar hasken rana za ta rage wa asibitin nauyin kuɗin da ake kashe wa da akalla 30%.

Asibitin AKTH ya roki kamfanin KEDCO

A baya, mun ruwaito cewa AKTH ya yi kira ga kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano (KEDCO) da ya dawo da wutar lantarkin da ya katse domin ceton rayuka.

Kara karanta wannan

ICPC: Kotu ta jika wa gwamnatin Kano aiki kan tsarin tallafin karatu

Shugabar sashen hulɗa da jama’a na asibitin, Hauwa Inuwa Dutse, ta ce katsewar wutar na kawo cikas ga marasa lafiya musamman masu dogaro da iskar numfashi.

Asibitin ya bayyana cewa kodayake yana sane da bashin da ake binsa na wutar lantarki, bai kamata hakan ya zama hujjar barin marasa lafiya cikin haɗari ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng