Manyan 'Yan Siyasa 4 da Za Su Koma Bakin Aiki bayan Janye Dokar Ta Baci a Rivers
- Shugaba Bola Tinubu ya sanar da dawowar gwamnatin Siminalayi Fubara bayan karewar watanni shida na dokar ta-baci a Rivers
- Janye dokar ta bacin na nufin, Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu da wasu shugabannin siyasa za su koma bakin aiki
- Tinubu ya yi kira ga shugabanni su guje wa rikici, ya ce dimokuraɗiyya za ta yi nasara ne kawai cikin zaman lafiya da haɗin kai
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Bayan tsawon watanni shida, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da ƙarewar dokar ta-baci da ya sanya a jihar Rivers.
Shugaban kasar na Najeriya ya bayyana cewa, gwamnatin Siminalayi Fubara ce yanzu za ta ci gaba da tafiyar da al’ammuran Rivers.

Source: Facebook
Tinubu ya janye dokar ta baci a Rivers
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba, 17 ga Satumba, Shugaba Tinubu ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Ina mai farin cikin sanar da ku cewa dokar ta-baci a jihar Rivers za ta zo ƙarshe daga ƙarfe 12 na daren yau (Laraba).
Sanarwar, ta tabbatar da cewa manyan ‘yan siyasa da aka dakatar a lokacin dokar ta-bacin za su koma kujerunsu.
Shugabannin siyasa 4 da za su koma aiki
Legit Hausa ta zakulo manyan shugabannin siyasar Rivers da za su koma kan kujerunsu bayan sanarwar Tinubu, su ne:
1. Gwamna Siminalayi Fubara
Gwamna Siminalayi Fubara, zai koma kan kujerarsa bayan dakatar da shi da Tinubu ya yi na tsawon watanni shida.
Tinubu ya ce rikicin da ya shiga tsakanin gwamnan da majalisar dokokin jihar ya durƙusar da harkokin mulki, wanda ya sa aka dauki mataki na ayyana dokar, amma yanzu, bayan karewar wa'adinta, Fubara zai koma ofis.
2. Mataimakiyar gwamna, Ngozi Odu
Ita ma mataimakiyar gwamnan jihar Rivers, Ngozi Nma Odu za ta koma kujerarta ta ci gaba da mulki, kamar Fubara.

Kara karanta wannan
Atiku ya yi nazari, ya gano abin da yake tunanin ya hana kawar da 'yan bindiga a Najeriya
Shugaban ƙasa ya bayyana cewa dawo da jagorancin gwamnati zai dawo da kwanciyar hankali da daidaito a jihar Rivers.
3. Kakakin majalisar jiha, Amaewhule
Martins Amaewhule, kakakin majalisar dokokin jihar, na cikin manyan shugabannin siyasa hudu da za su koma kan kujerarsu.
Tinubu ya ce yana fatan kakakin majalisar zai zama ginshiƙi wajen daidaita dangantaka tsakanin bangaren zartarwa da majalisar jihar.
4. Mambobin majalisar dokokin Rivers
Dukkanin mambobin majalisar dokokin jihar Rivers da aka dakatar a lokacin dokar ta-baci za su koma bakin aiki.
Shugaba Tinubu ya tunatar da su muhimmancin yin haɗin kai da gwamnati domin samar da zaman lafiya da ci gaban jihar.

Source: Twitter
Tinubu ya yi gargadi da jan kunne
Shugaban ƙasa ya yi amfani da wannan dama wajen tunatar da shugabannin siyasa a fadin ƙasa cewa:
“Za mu iya kawo al’ummarmu ribar dimokuraɗiyya ne kawai idan muna cikin yanayin zaman lafiya, bin tsari a gudanar da kyakkyawan mulki.”
Ya kuma kira gwamnoni da majalisun dokoki a faɗin ƙasar da su koyi darasi daga rikicin Rivers tare da guje wa rikicin da zai rushe gwamnatinsu.
Rivers: Dalilin kawo karshen dokar ta-baci
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya sanar da kawo ƙarshen dokar ta-baci da ya ayyana a jihar Rivers a watan Maris din 2025.
Tinubu ya ce ya janye dokar ne yanzu saboda ya samu kwarin gwiwa daga sababbin al’amura da suka nuna alamar sulhu da shirin shugabannin jihar Rivers na komawa tafiyar da mulki ta hanyar dimokuraɗiyya.
A sanarwar da ya fitar a ranar Laraba, shugaban kasar ya ce babu dalilin ci gaba da dokar ta-baci a jihar bayan tsawon watanni shida da na ayyana ta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

