Jiragen Yakin Sojin Saman Najeriya Sun Jefa Bama Bamai a Borno, An Kashe Ƴan Ta'adda
- Rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF) ta ce ta kai wani sabon hari ta sama a Borno, inda ta hallaka 'yan ta'adda da dama
- An kai harin ne a ranar Laraba, 17 ga Satumba, 2025, a yankin Bula Madibale da ke Gezuwa, bayan samun bayanan sirri
- Wannan harin ya biyo bayan wani hari da aka kai Bula Madibale a ranar 15 ga Satumba, inda aka kashe fiye da 'yan ta'adda 20
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - Dakaratun Operation HADIN KAI (AC OPHK), na rundunar sojin saman Najeriya (NAF), sun ƙara tsananta hare-haren sama a Arewa maso Gabas.
Wadannan tsauraran farmaki da sojojin saman ke kai wa sun yi sanadin hallaka da dama daga cikin ‘yan ta’adda tare da rusa gine-ginen su a jihar Borno.

Source: Twitter
Mai sharhi kan lamuran tsaro a Arewa maso Gabas da kuma yankin Tafkin Chadi, Zagola Makama ne ya rahoto hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gano sansanin 'yan ta'adda a Borno
Majiyar ta ce daraktan hulɗa da jama’a na NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya yi bayani kan harin baya bayan nan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 18 ga Satumba, 2025.
A cewar sanarwar, sojoji sun kai hari da misalin ƙarfe 10:50 na safiyar ranar Laraba, 17 ga Satumba 2025, bayan samun bayanan sirri kan motsin ‘yan ta’adda a Bula Madibale cikin yankin Gezuwa.
Binciken farko kafin kai harin, ya gano kusan ‘yan ta’adda 45 suna taruwa a wurin, wasu na shigowa a kan babura, wasu kuma a kan kekunan daga wurare dabam-dabam.
An hallaka 'yan ta'adda da dama
An kuma gano tutoci biyu na ‘yan ta’adda suna kadawa a wurin, abin da ya tabbatar da cewa wurin sansani ne, kuma matattarar 'yan ta'addan.
Bisa ga wannan sahihin bayani, jiragen yajin AC OPHK sun kaddamar da harin sama, inda aka hallaka ‘yan ta’adda da dama, aka rusa gine-ginensu da sauran muhimman kayayyakinsu.
Ehimen Ejodame ya jaddada cewa wannan farmaki na nuna ƙudirin sojojin na hana ‘yan ta’adda sake haɗuwa, ƙarfafa kai, ko kuma kai hare-hare kan al’umma.

Source: Original
Harin sojoji ya hallaka 'yan bindiga 20
Harin na baya-bayan nan na zuwa ne kwana biyu bayan wani irinsa da dakarun sojojin saman suka kai a yankin Bula Madibale na dajin Sambisa.
Majiyar tsaro ta bayyana cewa an kai harin ne a ranar 15 ga Satumba, 2025, inda aka samu nasarar hallaka fiye da ‘yan ta’adda 20 tare da rusa sansaninsu.
Bayanan sirri daga bangaren Watchkeepers ne suka taimaka wajen kai farmakin, da misalin ƙarfe 2:25 na rana.
Rundunar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da kai hare-hare kan 'yan ta'adda har sai an dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Arewa maso Gabas.
Sojojin sama sun kashe 'yan Boko Haram
A wani labarin, mun ruwaito cewa, sojojin saman Najeriya sun yi ruwan bama bamai kan 'yan ta'addan Boko Haram masu tayar da kayar baya a Borno.
Rundunar sojojin ta bayyana cewa jiragen yakinta sun kai hare-hare a maboyar 'yan ta'addan da ke cikin dajin Sambisa, bayan samun sahihan bayanai.
Farmakin da sojojin suka kai, ya sanya an kashe mayaka da kwamandojin kungiyar ta'addancin wadda ta yi kaurin suna wajen kai hare-hare.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


