Jagoran 'Yan Bindiga Ya Fara Cika Alkawari kan Yarjejeniyar Sulhu a Katsina
- Yarjejeniyar sulhun da aka cimmawa a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina ta fara aiki
- Jagoran 'yan bindiga, Isiya Akwashi Garwa, ya mutunta batun sulhu ta hanyar sako mutanen da ya yi garkuwa da su
- Mazauna yankin sun nuna farin cikinsu kan wannan ci gaban, inda su ka bukaci ya yi wa sauran miyagu magana su daina kai hare-hare
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Jagoran 'yan bindiga, Isiya Akwashi Garwa, ya sako mutane 28 da ake zargin ya sace a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina.
Jagoran 'yan bindigan ya sako mutanen ne ba tare da an biya kuɗin fansa ba, sakamakon yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimmawa a yankin.

Source: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
'Ku kashe 30, fiye da haka su taso': Tantirin dan bindiga ya yi gargadi ana tsaka da sulhu
Isiya ya sako mutanen da ya sace
Jagoran 'yan bindigan da yaransa sun mika mutanen da aka sace din ga jami’an karamar hukumar Faskar a ranar Laraba, 17 ga watan Satumban 2025.
Rahotanni sun nuna cewa mafi yawan mutanen da aka saki mazauna kauyukan Mairuwa, Kanon-haki da Yar Dabaru ne.
Hukumomin yankin sun tabbatar da cewa sakin mutanen ya samo asali ne daga wani shirin sulhu da aka kaddamar domin dawo da zaman lafiya da rage hare-haren tashin hankali.
Shugabannin al’umma a Faskari sun bayyana lamarin a matsayin alamar ci gaba mai kyau tare da kira ga ɓangarorin biyu da su ci gaba da bin tsarin zaman lafiya.
Haka kuma sun bukaci jagoran ‘yan bindigan da ya tilasta wa sauran tsagerun da ke kai hare-hare a yankin su daina.
Gwamnati ta tabbatar da lamarin
Wani jami’in karamar hukumar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da sako mutanen.
"An saki mutanen da rana ba tare da an biya ko kwabo ba. Shugaban ‘yan bindigan ya cika alkawarin da ya ɗauka a karkashin tattaunawar zaman lafiya.”
- Wani jami'in gwamnati
A gefe guda kuma, mazauna yankin sun bayyana farin ciki da dawowar waɗanda aka sace lafiya, inda wasu ke kira da a samar da karin tabbacin tsaro domin dorewar yarjejeniyar zaman lafiyan.

Source: Twitter
Wani mazaunin Faskari, Hayatu Usman ya shaidawa Legit Hausa cewa suna fatan sulhun ya dore.
"Abin da ya yi abin a yaba ne. Muna fatan wannan sulhun ya dore domin an yi a baya amma ba a cimma nasara ba."
"A kullum addu'ar mu ita ce Allah ya kawo mana karshen wannan masifar."
- Hayatu Usman
Karanta wasu labaran kan 'yan bindiga
- Karfin hali: 'Yan bindiga sun gabatar da manyan bukatu 3 kan sulhu a Katsina
- 'Dabarar da aka yi Katsina ta kawo karshen 'yan bindiga da kashi 70,' Gwamnati
- Sulhu: 'Dan bindiga, Ado Aliero ya nemi afuwar mutanen da aka kashe wa 'yan uwa
'Yan bindiga sun farmaki motar NSCDC

Kara karanta wannan
Katsina: Bayan Kachallah Isiya, tantirin ɗan bindiga ya cika alkawari domin mutunta sulhu
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga su yi wa jami'an hukumar tsaro ta NSCDC kwanton bauna a jihar Katsina.
Wani jami'in hukumar ya rasa ransa har lahira yayin da wasu jami'ai hudu su ka jikkata a harin da 'yan bindigan su ka kai musu a kan hanyar 'Yan Tumaki-Danmusa.
Jami'an na hukumar NSCDC sun fito daga wani aiki ne lokacin da'yan bindigan suka yi musu kwanton bauna.
Asali: Legit.ng
