Mutane Sun Fara Shan Romo da Aka Rabawa Talakawa Sama da Naira Biliyan 300 a Najeriya
- Gwamnatin Najeriya ta bayyana aniyarta na ci gaba da tallafawa marasa galihu a kowace shekara domin rage masu radadi
- Ministan Harkokin Kudi, Wale Edun ya ce zuwa yanzu an rabawa talakawa sama da Naira biliyan 300 a fadin Najeriya
- A alkaluman da ma'aikatar kudi ta fitar, ta ce 'yan Arewa sun fi amfana da shirin tallafin N25,000 fiye da yan Kudu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa zuwa yanzu ta rabawa mutane tallafin Naira biliyan 330 a karkashin shirin tallafawa marasa karfi.
Ministan Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Wale Edun, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja yau Laraba.

Source: Twitter
The Nation ta ce a taron, Edun ya ce an kirkiro shirin.ne domin rage wa talakawa da marasa galihu raɗaɗin matakan tattalin arzikin da aka aiwatar.
Yadda aka rabawa mutane N330bn a jihohi
A cewarsa, kowane mai cin gajiyar wannan shiri zai samu tallafin N25,000 sau uku, jimulla N75,000 domin rage radadin matsin tattalin arziki.
“Manufarmu ita ce mutane miliyan 15 su amfana, kowane mutum daya ya karɓi ₦25,000 sau uku. Zuwa yanzu, mutane miliyan 8.11 (kashi 54 cikin 100) sun samu rabon farko.
"Sai kuma wasu mutane miliyan 2.75 sun karɓi rabo na biyu, yayin da mutum miliyan 2.43 suka kammala karɓar matakai uku gaba ɗaya,” in ji shi.
Gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da shirin
Ministan ya tabbatar da cewa daga yanzu za a saka shirin a cikin kasafin kuɗin shekara-shekara na ƙasa domin tabbatar da dorewarsa.
Ya kuma bayyana cewa ba za a raba kuɗin a hannu kai tsaye ba, sai dai a tura su zuwa asusun mutane masu cin gajiyar shirin ta hanyar BVN da NIN.
Mista Edun ya jaddada cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da tallafin na isa ga wadanda aka yi dominsu, in ji rahoton The Cable.
Yan Arewa sun fi amfana da tallafin N25,000
A bayanan da ma’aikatar Kudi ta Najeriya ta fitar kan rabon wannan tallafi ta nuna cewa, Arewa ta samu kashi 72% na jimillar kuɗaɗen da aka raba yayin da Kudu ta samu kashi 28%.
Dangane da jinsi kuwa, ma'aikatar ta bayyana cewa mata sun kai kashi 69% na masu amfana yayin sa maza kuma ba su wuce kashi 31%.
Game da shekarun wadanda suka samu tallafin, 8% suna ƙasa da shekaru 20, 30% tsakanin shekaru 21–35, 22% tsakanin shekaru 36–50, 36% tsakanin shekaru 51–65, da kuma 4% da suka haura shekaru 65.
Za a taimakawa matasa 100,000 a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin horar da matasa 100,000 ayyuka tare da ba su takardar shaidar kwarewa.
Bayan horo da takardar shaidar aiki, za a hada kwararrun da aka horas da su da ayyuka kai tsaye ta hanyar amfani da wata sabuwar manhaja ta yanar gizo.
Gwamnatin ta tabbatar da cewa za a baiwa matasa, mata da masu bukata ta musamman damar shiga, domin karfafa damammakin aikin yi a cikin kasa.
Asali: Legit.ng


